Filtrer par genre

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau

Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

566 - Dalilin Da Fasfo Ya Zama Wajibi Ga Ɗanƙasa Ko Ba Don Tafiya Ba
0:00 / 0:00
1x
  • 566 - Dalilin Da Fasfo Ya Zama Wajibi Ga Ɗanƙasa Ko Ba Don Tafiya Ba

    Shin ka taba tunanin damammakin da za ka iya rasawa saboda rashin mallakar fasfon dan kasa a Najeriya?

    Yawancin mutane basu maida hankali wajen mallakar fasfo domin a tunaninsu sai idan kana kokarin ketare kasa ya zama wajibi a gare ka, amma kuma akwai damammaki da za ka iya rasawa saboda rashin mallamar shi.

    To ku biyo mu cikin Shirin Najeriya a Yau domin jin irin amfanin da mallakar fasfo zai iya muku da kuma damarmakin da za ku iyya rasawa.

    Fri, 26 Apr 2024
  • 565 - Da Gaske Haƙa Rijiyoyin Burtsatse Na Haifar Da Matsala A Anguwanni?

    Ana cikin matsanancin karancin ruwa a yankuna daban-daban a Najeriya.

    Lamarin ya sa a 'yan shekarun mutane ke ta kokarin samar da rijiyoyin burtsatse wato 'Borehole' a turance. Sai dai a cewar masana yawanci yanzu rijiyyoyi na kafewa da kuma haifar da zaizayar kasa.

    Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda ko haƙa bohol-bohol zai iya haifar da matsala ga muhalli da kuma al'umma a anguwanni?



    Thu, 25 Apr 2024
  • 564 - Me Ya Sa Ake Ƙin Faɗa Wa Mata Wasu Abubuwa Idan Za Su Yi Aure?

    Akwai abubuwan da ya kamata a rika bayyana wa mata idan za su yi aure amma kunya tana hanawa.

    Wasu sai sun je gidan aure suke tarar da abubuwan da ya kamata ace sun sani daga magabata, amma sai dai su tsinta a wajen kawayensu.

    Shirin Daga Laraba ya duba dalilan da ya sa ake kin bayyanawa mata wasu mahimman abubuwan da ya kamata su sani idan za su yi aure.

    Wed, 24 Apr 2024
  • 563 - Yadda Tsananin Zafi Zai Iya Cutar Da Dalibai A Makarantu

    Hukumomi sun bayyana jihohin da za a samu matsanancin zafi a Najeriya.

    Lamarin ya zo daidai lokacin da makarantu ke komawa hutu, inda ake fargabar yiwuwar yaduwar cututtuka a azuzuwa masu cunkuso.

    Shin ta wace hanya makarantu za su kauce wa yaduwar cututtuka masu alaka da matsanancin zafi? Shirin Najeriya a Yau na da karin bayani

    Tue, 23 Apr 2024
  • 562 - Rawar Da NNPP Ke Takawa A Dambarwar Dakatar Da Ganduje

    Dambarwa ta siyasa ci gaba da daukar hankali game da dakatar da shugaban jam’iyar APC na kasa

    Ana ta takaddama da zargin juna tsakanin jam’iyyun siyasa musamman na Kano da gwamnati mai ci a can.

    Toh amma wa ke wasa da hankalin wani ko rura wutar rikicin dakatar da Ganduje a jam’iyar APC, Shirin Najeriya a Yau na da karin bayani a kai.

    Mon, 22 Apr 2024
Afficher plus d'épisodes