Podcasts by Category

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau

Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

569 - “Tabbas Muna Biyan Ma’aikatan Borno Albashin N7,000, Amma...”
0:00 / 0:00
1x
  • 569 - “Tabbas Muna Biyan Ma’aikatan Borno Albashin N7,000, Amma...”

    Shafukan sada zumunta na ta girgiza bayan da wani labari ya bayyana game da yanayin walwalar ma’aikata da albashinsu a jihar Borno.

    Ma’aikata da dama sun yi ta yada hoton albashinsu na N7,000; wasu N8,000 ko N13,000 ko N15,000 ga ma’aikatan lafiya.

    Shirin Najeriya a Yau ya gano gaskiyar abin da ya sa gwamnatin jihar Borno ke biyan irin wannan albashi da wasu suka ce bai taka kara ya karya ba.

    Thu, 02 May 2024
  • 568 - Yadda Wahalar Fetur Ke Jigata ’Yan Najeriya

    Karancin man fetur na neman tsayar da al'amura cak ga al'umma a wasu sassan Najeriya. Da dama sun ce lamarin ya shafe su kaitsaye kuma sakamakon haka suna dandana kudarsu.

    Shin yaushe wannan lamari zai zo karshe, musamman idan yi la’akari da cewa tun a  Kamafanin Mai Na Kasa (NNPC) ya ce ya maganace matsalar?

    A shirin Najeriya a Yau mun tattauna da wadanda abin ya shafa sannan mu ji ta bakin masu ruwa da tsaki kan yiwuwar samun mafita nan kusa.

    Tue, 30 Apr 2024
  • 567 - Abin Da Ya Sa Gwamnonin Arewa Suka Je Amurka Taron Tsaro

    Gwamnonin Arewacin Najeriya da ake fuskantar kalubalen tsaro na kokarin lalubo ko ta wace hanya a samu dabarar dakile matsalar.

    Tafiyar  gwamnoni 9 daga arewacin Najeriya zuwa Amurka a kwanan nan domin halartar taron tsaro ya nuna yadda suke kokarin daidaita lamarin har a matakin kasashen ketare.

    Saidai lamarin na zuwa ne a lokacin da wasu ke ganin an yi makamancinsa a Najeriya ba tare da halartar wani gwamna daga jihohin da suke fama da matsalar tsaron ba.

    Shirin Najeriya a Yau ya duba tasirin da taron zai yi wajen magance matsalar yankunan.

    Mon, 29 Apr 2024
  • 566 - Dalilin Da Fasfo Ya Zama Wajibi Ga Ɗanƙasa Ko Ba Don Tafiya Ba

    Shin ka taba tunanin damammakin da za ka iya rasawa saboda rashin mallakar fasfon dan kasa a Najeriya?

    Yawancin mutane basu maida hankali wajen mallakar fasfo domin a tunaninsu sai idan kana kokarin ketare kasa ya zama wajibi a gare ka, amma kuma akwai damammaki da za ka iya rasawa saboda rashin mallamar shi.

    To ku biyo mu cikin Shirin Najeriya a Yau domin jin irin amfanin da mallakar fasfo zai iya muku da kuma damarmakin da za ku iyya rasawa.

    Fri, 26 Apr 2024
  • 565 - Da Gaske Haƙa Rijiyoyin Burtsatse Na Haifar Da Matsala A Anguwanni?

    Ana cikin matsanancin karancin ruwa a yankuna daban-daban a Najeriya.

    Lamarin ya sa a 'yan shekarun mutane ke ta kokarin samar da rijiyoyin burtsatse wato 'Borehole' a turance. Sai dai a cewar masana yawanci yanzu rijiyyoyi na kafewa da kuma haifar da zaizayar kasa.

    Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda ko haƙa bohol-bohol zai iya haifar da matsala ga muhalli da kuma al'umma a anguwanni?



    Thu, 25 Apr 2024
Show More Episodes