Podcasts by Category
Wasanni

- 106 - An kammala gasar tseren Keke ta ƙasa karo na 6 a Jamhuriyyar Nijar
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan yadda aka gudanar da gasar tseren keke a jihar Maradi da ke Jamhuriyar Nijar. Wannan ne dai karo na 6 da ake gudanar da gasar da ta haɗa masu wannan wasa daga jihohi 8 na ƙasar, da nufin samun gwarazan shekara sannan kuma a zaɓa ƴan wasan da za su rinƙa wakiltar ƙasar a gasanni daban daban kama daga nahiyar Afirka dama matakin duniya idan dama ta samu.
Ku latsa alamar sauto don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh...............
Mon, 28 Sep 2026 - 105 - Duniyar Wasanni: Wace waina ake toyawa a gasar Frimiya Lig ta IngilaMon, 21 Sep 2026
- 104 - Ƙananan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a matakin Unguwanni sun fara cinikayyar ƴan wasa
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan yadda ake cinikayyar ƴan wasa a matakin ƙananan ƙungiyoyin Unguwanni. A yanzu dai ƙananan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da ke buga wasanni a matakin Unguwanni a jihar Kaduna, tuni suka rungumi tsarin cinikayyar ƴan wasa domin ƙarawa ƙungiyoyinsu ƙarfi.
Wasu daga cikin masu horas da irin waɗannan ƙungiyoyi sun ce wannan tsarin cinikayya ya taimaka wajen kawo ƙarshen rigingimu da a ke samu kan ƴan wasa, sannan kuma ana gudanar da ita ne kan kuɗin da suka fara daga naira dubu 30 zuwa sama.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh............
Mon, 07 Sep 2026 - 103 - Shugabanni hukumar NFF sun yi murabus bayan kiraye-kirayen ƴan Najeriya
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan murabus ɗin da shugaban hukumar kwallon ƙafa ta Najeriya NFF Alhaji Ibrahim Gusau da wasu daga cikin mambobin kwamitin zartarwarsa suka yi, bayan matsin lambar da suka fuskanta kan koma bayan da tawagogin ƙasar suka samu a manyan gasanni na duniya, ciki har da gaza samun gurbin da tawagar mata ta ƙasar ta yi a gasar lashe kofin duniya da za a yi a shekara mai zuwa.
A cewar rahotanni, 8 daga cikin mambobin kwamitin 13 ne suka yi murabus daga jagorancin hukumar ta NFF, lamarin da ya haifar da shakku gameda zaɓen shugabannin hukumar da za a yi nan ba da jimaba.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh............
Mon, 31 Aug 2026 - 102 - An fara yunƙurin rushe kwamitin ƙoli na hukumar NFF a Najeriya
Shirin Duniyar Wasanni na yau ya mayar da hankali kan dambarwar da ta kunno kai a sashen wasanni na Najeriya bayan da hukumar wasannin ƙasar ta baiwa mambobin kwamitin ƙolin NFF wa’adin sa’o’i 24 tun a juma’ar da ta gabata kan su ajje aiki.
Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.
Mon, 24 Aug 2026 - 101 - Manyan kalubalen da tawagogin ƙwallon ƙafar Najeriya ke fuskanta a harakar wasanniMon, 17 Aug 2026
- 100 - Yadda ba a samun sabbin ƙasashen da ke lashe Gasar Kofin DuniyaMon, 27 Jul 2026
- 99 - Spain ta lashe kofin duniya karo na biyu a tarihiMon, 20 Jul 2026
- 97 - Sharhin yadda wasannin kwata final na gasar cin kofin duniya suka gudana
Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya mayar da hankali kan wasannin gab da na kusa da ƙarshe na gasar cin kofin duniya da aka kammala tsakanin ƙasashe 8 wanda kuma kawo yanzu ya rage ƙasashe 4 a wannan tafiya wadda ta faro da ƙasashe 48.
A wasannin dai Faransa ta yi waje da Morocco yayinda Spain ta yi waje da Belgium kana Ingila ta yi waje da Norway yayinda Argentina mai kare kambun gasar ta yi waje da Switzerland.
Hankula sun karkata ga wasannin ƴan huɗu da suka rage a wannan gasa don ganin waɗanda zasu kai wasan ƙarshe.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin....
Mon, 13 Jul 2026 - 96 - Tawagogin ƙasashen Afirka 7da aka yi waje dasu bayan sun tsallaka zagayen ƴan 32
Bayan nasarar da tawagogin ƙasashen Afrika 9 suka yi na kaiwa zagayen ƴan 32 a gasar lashe kofin duniya, wani lamari da ya sanya nahiyar ta kafa tarihin samun yawan wakilai a wannan zagaye, sai dai kuma ana iya cewa murna ta koma ciki domin dai tuni aka yi waje da 7 daga cikin 9.
Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.........
Mon, 06 Jul 2026 - 95 - Irin rawar da ƙasashen Afirka suka taka a gasar Kofin Duniya ta 2026
Shirin a wannan lokaci zayyi duba ne kan yadda irin rawar da ƙasashen Afrika suka taka a wasannin rukuni a gasar lashe kofin duniya.
A ƙarshen mako ne dai aka kammala wasanni rukuni, abinda ke nuna cewar an buga wasanni 72 daga cikin 104 da za a yi a wannan gasa.
Sakamakon waɗannan wasani da aka yi ya nuna cewar anyi waje da tawagogin ƙasashe 16 daga cikin 48 dake fafatawa a gasar, inda ƙasashe 32 suka yi saura.
Nahiyar Afrika da ke da wakilcin ƙasashe 10, 9 daga cikin su sun samu nasarar kaiwa wannan zagaye, waɗanda suka haɗa da Afrika ta kudu da Senegal da Morocco da Ghana Ivory Coast da DR Congo da Algeria da Masar da kuma Cape Varde, inda Tunisia ta yi adabo da gasar.
Mon, 29 Jun 2026 - 94 - Muhimman abubuwan da suka faru a Gasar lashe Kofin Duniya kawo yanzuMon, 22 Jun 2026
- 93 - Dalilan da ya sa ƴan Afirka suka juyawa tawagar Afirka ta Kudu bayaMon, 15 Jun 2026
- 92 - Shiri na musamman kan shirye-shiryen fara gasar lashe kofin duniya
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan gasar lashe kofin duniya da za a fara a wannan makon. Ita dai wannan gasa ta lashe kofin duniya da aka faro a shekarar 1930, Hukumar Kwallon Ƙafa ta Duniya FIFA ce ke shiryata duk bayan shekara 4, sai dai a shekarun 1942 da kuma 1946 an samu tsaikon gudanar da gasar sakamakin yaƙin duniya na biyu.
Bayan kammala gasar da ƙasar Qatar ta karɓi baƙunci a shekarar 2022, jumullar ƙsashe 80 ne suka taɓa fafatawa a cikinta, inda aka buga wasan ƙarshe har 22 sai kuma ƙasashe 8 ne kawai suka taɓa lashe ta, inda Brazil ke da 5, Argentina da ke rike da kofin na da 4, Jamus da Italiya na da 3-3 sai Faransa da Uruguay da ta fara karɓar baƙuncin gasar ke da 2-2, yayinda Ingila da Spain kowaccensu ta lashe so guda-guda.
Ku latsa alamar sauti don sauaron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.............
Mon, 08 Jun 2026 - 91 - PSG ta lashe Gasar zakarun ta Turai a karo na biyu
Shirin Duniyar Wasanni a wannan mako tare da Khamis Saleh ya yi duba kan yadda aka gudanar da wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai tsakanin ƙungiyar PSG da kuma Arsenal, inda PSG ɗin ta samu nasarar lashe gasar a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan da aka ta shi 1-1.
Danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin........
Mon, 01 Jun 2026 - 90 - Sharhi kan nasarar lashe gasar Premier League da Arsenal ta yi a bana
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci ya yi duba ne kan nasarar lashe gasar Firimiyar Ingila da Arsenal ta yi a kakar wasan bana, bayan kwashe tsawon shekaru 22 batare da tayi tozali da kofin ba. A Lahadin nan ne aka miƙawa Arsenal kofin bayan buga wasanta na ƙarshe a gasar a wannan kaka tsakaninta da Cystal Palace, inda aka tashi 2-1.
Tun kafin wasan na jiya ne dai aka nasarar da Arsenal a matsayin zakarar gasar, bayan tashi 1-1 da aka yi a karawar da akayi tsakanin Manchester City da Bournemouth.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh....................
Mon, 25 May 2026 - 89 - Yadda aka lashe mafi akasarin gasannin lik-lik na nahiyar Turai
Shirin Duniyar Wassani a wannan lokacin yayi duba ne kan yadda aka lashe mafi akasarin gasannin lik-lik na nahiyar Turai, in banda gasar Firimiyar Ingila. Barcelona ta lashe gasar La liga a Spain, a Inter Milan ta lashe gasar Serie A na Italiya, ita kuwa Bayern Munich ta ɗauke kofin Bundesliga na ƙasar Jamus, yayin da PSG ta lashe gasar League 1 ta Faransa.
A yanzu haka dai gasar Firimiyar Ingila ce ake dakon jirar ƙungiyar da za ta lashe tsakanin Arsenal da Manchester City, waɗanda kowaccensu ke da ragowar wasanni biyu-biyu.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh..........
Mon, 18 May 2026 - 88 - Yadda aka gudanar da gasar Super 4 ta a Najeriya
A ranar juma’ar data gabata ne dai aka kammala gasar gasar Super 4, wacce aka fafata tsakacin ƙungiyoyi 4 da suka haɗa da Sporting Lagos da Inter Lagos da Ranchers Bees ta Kaduna sai kuma Doma United, da suka zama zagaru a rukunoninsu na gasar NNL, gasa ta biyu mafi daraja a Najeriya.
An gudanar da gasar ne a yanayin yadda ake gudanar da gasar lik-lik, inda kowa ya kara da kowa ganin cewa kowaccensu za ta haska a gasar Firimiyar Najeriya a kakar baɗi.
A wasannin ƙarshe da aka aka yi, Sporting Lagos ta sha kashi da ci ɗaya mai banshi a hannun Inter Lagos, amma sai dai hakan bai hanata lashi gasar ba da ban-bancin ƙwallaye, domin kowaccensu ta ƙare ne da maki 6.
Wannan ne karo na farko da Sporting Lagos ta taɓa lashe kofin tun bayan samar da ita a shekarar 2022.
Mon, 11 May 2026 - 87 - Matsalolin da suka dabaibaye ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Jigawa Golden Stars
A wannan mako shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh ya mayar da hankali ne kan halin da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Jigawa Golden Stars ke ciki, wanda ya haddasawa ƙungiyar gagarumin koma baya.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Jigawa Golden Stars, ta kasance guda cikin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar ƙwararru da ake ji da su a shekarun baya daga yankin Arewacin Najeriya, wadda ta shafe tsawon shekaru tana gwagwarmaya a gasar firimiyar ƙasar wato NPFL.
Ƙungiyar ta shahara wajen horas da matasan ƴan wasa daga Arewacin Najeriya da kuma fafatawa da manyan ƙungiyoyi a ƙasar. A baya dai ƙungiyar ta Jigawa Golden Stars duk da namijin ƙoƙari da ta ke yi, ta taɓa shafe kusan shekaru bakwai ba tare da zuwa gasar Firimiyar Najeriya, kafin daga bisani ta sake komawa babbar gasar.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Mon, 04 May 2026 - 86 - NPFL: Saura mako 3 a ƙarƙare amma har yanzu ba a san zakaran bana ba
Shirin awannan mako ya leƙa gasar Firirmiyar Najeriya ne wadda ke gab da ƙarƙarewa, amma kuma haryanzu ba a san maci tuwon ba.
Yanzu haka dai an kammala wasannin mako na 35 a gasar Firimiyar Najeriya, wadda ya rage mako 3 kacal a kammala gasar a kakar wasa ta bana, amma sai dai haryanzu ƴar manuniya bata nuna ƙungiyar da za ɗauki gasar ba tsakanin ta saman teburi harzuwa wadda take a mataki na huɗu, saboda gajeruwar tazarar da ke tsakani, haka kuma abun yake a matakin ƙasan tebur inda nan ma ƙungiyar Wikki ce kadai kawo yanzu ake ganin da wahala ta tsallake, ya yinda ƙungiyoyin da ke mataki na 11 har zuwa matakin 19 kowaccen su bata da tabbas.
Mon, 27 Apr 2026 - 85 - Sharhi kan wasannin dab dana kusa dana ƙarshe a gasar zakarun Turai
A makon daya gabata ne aka kammala wasannin zagayen dab dana kusa da na ƙarshe na gasar zakarun Turai, inda Bayern Munich ta cire Real Madrid, Atletico Madrid ita kuma ta doke Barcelona, Arsenal ta fidda Sporting CP, yayinda PSG ita kuma ta samu galaba kan Liverpool.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh...............
Mon, 20 Apr 2026 - 84 - Matakan da CAF ke dauka don warware dambarwar da ke tsakanin Morocco da SenegalMon, 13 Apr 2026
- 83 - Hasashe game da rawar da ƙasashen Afirka za su taka a gasar lashe Kofin DuniyaMon, 06 Apr 2026
- 82 - Amurka ta gargaɗi masu aniyar maƙalewa idan suka je kallon gasar cin kofin duniya
Shirin Duniyar Wassani a wannan lokaci yayi duba ne kan yadda Amurka ta fara gargaɗin ƴan Ghana da ke da aniyar maƙalewa idan suka je ƙasar don kallon gasar cin kofin duniya da ƙasashen Amurka da Canada da kuma Mexico za su karɓi baƙunci a watan Yuni mai zuwa.
Ganin irin matakan da dama gwamnatin Amurka ke ɗauka kan shigar baki ƙasar tuni ofishin Jakadancin ƙasar da ke Ghana ya fara gargaɗin masu shirin halartar gasar da su guji wuce wa’adin da aka basu.
Jakadan Amurka a Ghana Rolf Olson ya ce saɓawa dokokin shige da fice na ƙasar na iya haifar da mummunan sakamako, gami da rashin sake samun damar shiga ƙasar a nan gaba.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh..............
Mon, 09 Mar 2026
Podcasts similar to Wasanni
Herrera en COPE COPE
La Linterna COPE
Dante Gebel Live Dante Gebel
Es la Mañana de Federico esRadio
La noche de Cuesta esRadio
La Trinchera de Llamas esRadio
Hondelatte Raconte Europe 1
Affaires sensibles France Inter
LEGEND Guillaume Pley
El colegio invisible OndaCero
La Rosa de los Vientos OndaCero
Les grands dossiers de l'Histoire par Franck Ferrand Radio Classique
Espacio en blanco Radio Nacional
Enquêtes criminelles RTL
Entrez dans l'Histoire RTL
Le grand récit RTL
Les Grosses Têtes RTL
L'Heure Du Crime RTL
Parlons-nous RTL
SER Historia SER Podcast
Todo Concostrina SER Podcast
Un Libro Una Hora SER Podcast
L'After Foot RMC
Super Moscato Show RMC
Rothen s'enflamme RMC
Les nuits du Cazarre enchaîné RMC
Les Grandes Gueules du Sport RMC
El Partidazo de COPE COPE
Stephen Brunch RMC
Basket Time RMC
Radio Foot Internationale RFI
RMC Poker Show RMC
El Larguero SER Podcast
On refait le match RTL
After Foot : Les archives mythiques RMC
Bartoli Time RMC
RMC Running RMC
PARIS CENTRAL - PSG PODCAST Paris Central
Entre les potos RMC
COURIR MIEUX - Progresser en trail avec la science, par Cyril Forestier Cyril Forestier
Complètement Foot RTBF
After Espagne RMC