Filtrar por género
Wasanni

- 113 - Tagomashin da tawagar Flamingos ta samu bayan lashe kofin duniya
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci ya maida hankali ne kan nasarar lashe kofin duniya na mata ƴan ƙasa da shekaru 17 da tawagar Flamingos ta Najeriya ta yi, bayan da ta lallasa takwararta ta Japan a wasan ƙarshe da ci 2-1. Tuni dai shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya gwangwaje ƴan matan da kyautar naira miliyan Ɗari-ɗari.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.............
Mon, 16 Nov 2026 - 112 - Bamuji ɗaɗin irin rabuwar da aka yi tsakanin Ronaldo da Portugal ba - Ra'ayoyi
Shirin na duniyar wasanni a wannan lokaci yayi duba ne game da bankwana da tawagar Portugal da Ronaldo yayi. A cikin wani saƙon bidiyo da ya wallafa a shafinsa, lamarin da ke kawo ƙarshen shekaru fiye da 20 da ya shafe yana wakiltar ƙasar shi a matakin ƙwallon ƙafar duniya. Cikin saƙon na Ronaldo, ya ce bayan nutsuwa cikin tsananki ya fahimci cewa lokaci ya yi da zai kawo ƙarshen wakiltar ƙasar shi kodayake ya ce Portugal za ta ci gaba da kasancewa a zuciyar shi.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh..............
Mon, 09 Nov 2026 - 111 - Sharhi akan kyautar Ballon d'Or ta 2026 wadda Harry Kane ya lashe
Shirin 'Duniyar Wasanni' tare da Khamis Saleh zai maida hankali ne kan kyautar Ballon d’Or da aka bayar a ranar Litinin ɗin data gabata. Kyaftin ɗin tawagar Ingila Harry Kane ya lashe kyautar a bana, inda ya zamo ɗan wasan ƙasar na farko daya lashe ta cikin shekaru 25, wato tun bayan Michael Owen a shekarar 2001.
Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin...........
Mon, 02 Nov 2026 - 110 - Sharhi kan yadda ta kaya a wasan El-Clasico da aka yi a ƙarshen mako
Shirin Duniyar Wasanni a wannan mako ya maida hankali kan wasan El-Clasico da aka yi tsakanin Barcelona da Real Madrid. Shi dai wasa tsakanin waɗannan ƙungiyoyi ba wai wasa bane na gama gari, domin yanada ɗinbin tarihi ganin cewa an faro shine a shekarar 1902, kuma wancan lokacin Barcelona ce ta fara samun nasara kan Madrid da ci 3-1. Sai dai a wasan na daren jiya Lahadi Madrid ce ta samu nasara da ci 2-1.
Sakamakon wannan wasa ya bada mamaki matuƙa, domin dai an yi tunanin Barcelona za ta yi wa Madrid Kukkunge ne, kasancewar tana gida tare da goyon bayan mutane dubu 62,650 da suka taru a filin wasan Spotify Camp Nou, domin ganin yadda zata kaya.
Haka nan ƙungiyar ta kwashe sama da shekara guda ba tare da tayi rashin nasara a filin ba, domin rashin nasara ta ƙarshe da tayi a nan ita ce a hannun Villarreal a ranar 18 ga watan Mayun shekarar bara, gashi kuma tayi nasara a wasanni 6 cikin 7 na haɗuwarsu.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh..............
Mon, 26 Oct 2026 - 109 - Nasarar tawagar ƙwallon ƙafar mata ta Najeriya akan Comoros
Shirin 'Duniya Wasanni' a wanan mako tare da Khamis Saleh zai dubu ne kan nasarar da tawagar Super Falcons ta samu kan Comoros, inda a makon da ya gabata ne aka kammala wasa na biyu na zagaye na biyu na neman zuwa gasar Olympics da aka yi tsakanin tawagar mata ta Super Falcons ta Najeriya da takwararta ta Coromos.
An dai buga dukkanin wasanni biyu ne a filin wasa na Remon Star da ke garin Ikenne na jihar Ogun, inda a wasan farko Super Falcons ta samu nasara da ci 2 da nemam sannan a wasa na biyu aka tashi 5 da nema, a jumlace gida da waje Najeriya ta jefa kwallaye biyar da nema a ragar Comoros.
Mon, 19 Oct 2026 - 108 - Messi ya yi bankwana da tawagar Argentina bayan doka wasanni 208
Shirin "Duniyar Wasanni" tare da Khamis Saleh a wannan mako, zai dubu ne kan bankwanan da Lionel Messi ya yi da tawagar Argentina.
A farkon watan Oktoban nan da muke ciki ne kyaftin ɗin tawagar ƙasar Argentina Lionel Messi, yayi bankwana da tawagar bayan kwashe tsawon shekaru 21 tana wakiltar ƙasar a wasannin matakin ƙasa da ƙasa.
Messi ya fara bugawa Argentina wasanni ne a ranar 17 ga watan Agustan shekarar 2005 a wani wasan sada zumunci da suka yi da Hungry, inda ya samu nasarar buga wasanni 208, kafin murabus ɗinsa a ƙarawarsu da Benin a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2026.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin..
Mon, 12 Oct 2026 - 107 - Yadda ƴan wasa ke dawowa gida don buga wasannin sada zumunci a lokacin hutu
Shirin a wannan mako ya yi duba ne kan yadda ƴan wasan da ke taka leda ke dawowa gida don buga wasannin sada zumunci a lokacin da suke hutu.
A duk lokacin da aka kammala wasannin lig-lig a kan tafi hutu a kowace shekara musamman a nahiyar Turai da lig ɗin su ya fi jan hankali, wanda hakan kuma ke buɗe wani babi na wasanni a yankuna daban-daban da ƴan wasan ke fitowa domin nuna bajintarsu a zahiri a wasannin sada zumunta da a ke shirya musu.
Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Mon, 05 Oct 2026 - 106 - An kammala gasar tseren Keke ta ƙasa karo na 6 a Jamhuriyyar Nijar
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan yadda aka gudanar da gasar tseren keke a jihar Maradi da ke Jamhuriyar Nijar. Wannan ne dai karo na 6 da ake gudanar da gasar da ta haɗa masu wannan wasa daga jihohi 8 na ƙasar, da nufin samun gwarazan shekara sannan kuma a zaɓa ƴan wasan da za su rinƙa wakiltar ƙasar a gasanni daban daban kama daga nahiyar Afirka dama matakin duniya idan dama ta samu.
Ku latsa alamar sauto don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh...............
Mon, 28 Sep 2026 - 105 - Duniyar Wasanni: Wace waina ake toyawa a gasar Frimiya Lig ta IngilaMon, 21 Sep 2026
- 104 - Ƙananan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a matakin Unguwanni sun fara cinikayyar ƴan wasa
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan yadda ake cinikayyar ƴan wasa a matakin ƙananan ƙungiyoyin Unguwanni. A yanzu dai ƙananan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da ke buga wasanni a matakin Unguwanni a jihar Kaduna, tuni suka rungumi tsarin cinikayyar ƴan wasa domin ƙarawa ƙungiyoyinsu ƙarfi.
Wasu daga cikin masu horas da irin waɗannan ƙungiyoyi sun ce wannan tsarin cinikayya ya taimaka wajen kawo ƙarshen rigingimu da a ke samu kan ƴan wasa, sannan kuma ana gudanar da ita ne kan kuɗin da suka fara daga naira dubu 30 zuwa sama.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh............
Mon, 07 Sep 2026 - 103 - Shugabanni hukumar NFF sun yi murabus bayan kiraye-kirayen ƴan Najeriya
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan murabus ɗin da shugaban hukumar kwallon ƙafa ta Najeriya NFF Alhaji Ibrahim Gusau da wasu daga cikin mambobin kwamitin zartarwarsa suka yi, bayan matsin lambar da suka fuskanta kan koma bayan da tawagogin ƙasar suka samu a manyan gasanni na duniya, ciki har da gaza samun gurbin da tawagar mata ta ƙasar ta yi a gasar lashe kofin duniya da za a yi a shekara mai zuwa.
A cewar rahotanni, 8 daga cikin mambobin kwamitin 13 ne suka yi murabus daga jagorancin hukumar ta NFF, lamarin da ya haifar da shakku gameda zaɓen shugabannin hukumar da za a yi nan ba da jimaba.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh............
Mon, 31 Aug 2026 - 102 - An fara yunƙurin rushe kwamitin ƙoli na hukumar NFF a Najeriya
Shirin Duniyar Wasanni na yau ya mayar da hankali kan dambarwar da ta kunno kai a sashen wasanni na Najeriya bayan da hukumar wasannin ƙasar ta baiwa mambobin kwamitin ƙolin NFF wa’adin sa’o’i 24 tun a juma’ar da ta gabata kan su ajje aiki.
Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.
Mon, 24 Aug 2026 - 101 - Manyan kalubalen da tawagogin ƙwallon ƙafar Najeriya ke fuskanta a harakar wasanniMon, 17 Aug 2026
- 100 - Yadda ba a samun sabbin ƙasashen da ke lashe Gasar Kofin DuniyaMon, 27 Jul 2026
- 99 - Spain ta lashe kofin duniya karo na biyu a tarihiMon, 20 Jul 2026
- 97 - Sharhin yadda wasannin kwata final na gasar cin kofin duniya suka gudana
Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya mayar da hankali kan wasannin gab da na kusa da ƙarshe na gasar cin kofin duniya da aka kammala tsakanin ƙasashe 8 wanda kuma kawo yanzu ya rage ƙasashe 4 a wannan tafiya wadda ta faro da ƙasashe 48.
A wasannin dai Faransa ta yi waje da Morocco yayinda Spain ta yi waje da Belgium kana Ingila ta yi waje da Norway yayinda Argentina mai kare kambun gasar ta yi waje da Switzerland.
Hankula sun karkata ga wasannin ƴan huɗu da suka rage a wannan gasa don ganin waɗanda zasu kai wasan ƙarshe.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin....
Mon, 13 Jul 2026 - 96 - Tawagogin ƙasashen Afirka 7da aka yi waje dasu bayan sun tsallaka zagayen ƴan 32
Bayan nasarar da tawagogin ƙasashen Afrika 9 suka yi na kaiwa zagayen ƴan 32 a gasar lashe kofin duniya, wani lamari da ya sanya nahiyar ta kafa tarihin samun yawan wakilai a wannan zagaye, sai dai kuma ana iya cewa murna ta koma ciki domin dai tuni aka yi waje da 7 daga cikin 9.
Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.........
Mon, 06 Jul 2026 - 95 - Irin rawar da ƙasashen Afirka suka taka a gasar Kofin Duniya ta 2026
Shirin a wannan lokaci zayyi duba ne kan yadda irin rawar da ƙasashen Afrika suka taka a wasannin rukuni a gasar lashe kofin duniya.
A ƙarshen mako ne dai aka kammala wasanni rukuni, abinda ke nuna cewar an buga wasanni 72 daga cikin 104 da za a yi a wannan gasa.
Sakamakon waɗannan wasani da aka yi ya nuna cewar anyi waje da tawagogin ƙasashe 16 daga cikin 48 dake fafatawa a gasar, inda ƙasashe 32 suka yi saura.
Nahiyar Afrika da ke da wakilcin ƙasashe 10, 9 daga cikin su sun samu nasarar kaiwa wannan zagaye, waɗanda suka haɗa da Afrika ta kudu da Senegal da Morocco da Ghana Ivory Coast da DR Congo da Algeria da Masar da kuma Cape Varde, inda Tunisia ta yi adabo da gasar.
Mon, 29 Jun 2026 - 94 - Muhimman abubuwan da suka faru a Gasar lashe Kofin Duniya kawo yanzuMon, 22 Jun 2026
- 93 - Dalilan da ya sa ƴan Afirka suka juyawa tawagar Afirka ta Kudu bayaMon, 15 Jun 2026
- 92 - Shiri na musamman kan shirye-shiryen fara gasar lashe kofin duniya
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan gasar lashe kofin duniya da za a fara a wannan makon. Ita dai wannan gasa ta lashe kofin duniya da aka faro a shekarar 1930, Hukumar Kwallon Ƙafa ta Duniya FIFA ce ke shiryata duk bayan shekara 4, sai dai a shekarun 1942 da kuma 1946 an samu tsaikon gudanar da gasar sakamakin yaƙin duniya na biyu.
Bayan kammala gasar da ƙasar Qatar ta karɓi baƙunci a shekarar 2022, jumullar ƙsashe 80 ne suka taɓa fafatawa a cikinta, inda aka buga wasan ƙarshe har 22 sai kuma ƙasashe 8 ne kawai suka taɓa lashe ta, inda Brazil ke da 5, Argentina da ke rike da kofin na da 4, Jamus da Italiya na da 3-3 sai Faransa da Uruguay da ta fara karɓar baƙuncin gasar ke da 2-2, yayinda Ingila da Spain kowaccensu ta lashe so guda-guda.
Ku latsa alamar sauti don sauaron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.............
Mon, 08 Jun 2026 - 91 - PSG ta lashe Gasar zakarun ta Turai a karo na biyu
Shirin Duniyar Wasanni a wannan mako tare da Khamis Saleh ya yi duba kan yadda aka gudanar da wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai tsakanin ƙungiyar PSG da kuma Arsenal, inda PSG ɗin ta samu nasarar lashe gasar a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan da aka ta shi 1-1.
Danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin........
Mon, 01 Jun 2026 - 90 - Sharhi kan nasarar lashe gasar Premier League da Arsenal ta yi a bana
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci ya yi duba ne kan nasarar lashe gasar Firimiyar Ingila da Arsenal ta yi a kakar wasan bana, bayan kwashe tsawon shekaru 22 batare da tayi tozali da kofin ba. A Lahadin nan ne aka miƙawa Arsenal kofin bayan buga wasanta na ƙarshe a gasar a wannan kaka tsakaninta da Cystal Palace, inda aka tashi 2-1.
Tun kafin wasan na jiya ne dai aka nasarar da Arsenal a matsayin zakarar gasar, bayan tashi 1-1 da aka yi a karawar da akayi tsakanin Manchester City da Bournemouth.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh....................
Mon, 25 May 2026 - 89 - Yadda aka lashe mafi akasarin gasannin lik-lik na nahiyar Turai
Shirin Duniyar Wassani a wannan lokacin yayi duba ne kan yadda aka lashe mafi akasarin gasannin lik-lik na nahiyar Turai, in banda gasar Firimiyar Ingila. Barcelona ta lashe gasar La liga a Spain, a Inter Milan ta lashe gasar Serie A na Italiya, ita kuwa Bayern Munich ta ɗauke kofin Bundesliga na ƙasar Jamus, yayin da PSG ta lashe gasar League 1 ta Faransa.
A yanzu haka dai gasar Firimiyar Ingila ce ake dakon jirar ƙungiyar da za ta lashe tsakanin Arsenal da Manchester City, waɗanda kowaccensu ke da ragowar wasanni biyu-biyu.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh..........
Mon, 18 May 2026
Podcasts similares a Wasanni
Herrera en COPE COPE
La Linterna COPE
Es la Mañana de Federico esRadio
La noche de Cuesta esRadio
La Trinchera de Llamas esRadio
Hondelatte Raconte Europe 1
Affaires sensibles France Inter
LEGEND Guillaume Pley
CHRONIQUES CRIMINELLES Jacques Pradel - TF1
El colegio invisible OndaCero
La Rosa de los Vientos OndaCero
Les grands dossiers de l'Histoire par Franck Ferrand Radio Classique
Espacio en blanco Radio Nacional
Entrez dans l'Histoire RTL
Le grand récit RTL
Les Grosses Têtes RTL
L'Heure Du Crime RTL
Nadie Sabe Nada SER Podcast
SER Historia SER Podcast
Todo Concostrina SER Podcast
Un Libro Una Hora SER Podcast
HISTORIAS DE LA HISTORIA VIVA RADIO
L'After Foot RMC
Super Moscato Show RMC
Les nuits du Cazarre enchaîné RMC
Rothen s'enflamme RMC
Les Grandes Gueules du Sport RMC
El Partidazo de COPE COPE
El Larguero SER Podcast
RMC Running RMC
NBA Extra beIN SPORTS France
Basket Time RMC
Entre les potos RMC
El Primer Palo esRadio
First Team First Team
On refait le match RTL
WINAMAX FOOTBALL CLUB Winamax
RMC Poker Show RMC
SANS FILET Winamax
Stephen Brunch RMC
Le Kikadi RMC
Le podcast BasketSession Le podcast BasketSession