Nach Genre filtern

Usman Kabara

Usman Kabara

Usman Kabara

Ni Dan Jarida ne da ke tattaunawa da Hausawa a kasashen waje game da gwagwarmayar rayuwa.

36 - KAMALUDDEEN KABIR: Yadda ya sami karatu a Birtaniya
0:00 / 0:00
1x
  • 36 - KAMALUDDEEN KABIR: Yadda ya sami karatu a Birtaniya

    Dakta Kamaluddeen Kabir, dan asalin jigar Katsina ne mai digirin digirgir wanda yayi karatunsa a tsakanin Najeriya da Birtaniya sannan kuma Malami ne yanzu haka a jami'ar Umaru Musa 'YarAdua da ke jihar ta Katsina.

    --- Send in a voice message: https://podcasters.spotify.com/pod/show/usmankabara/message
    Fri, 17 Feb 2023 - 57min
  • 35 - NA’IMA IDRIS: Ta shiga sahun manyan gobe a Afirka

    Na'ima Idris Usman, cikakkiyar Likita ce da ke jihar Kanon Najeriya, ta yi karatun a tsakanin Najeriys da China. Ta bamu labarin rayuwarta daga kuruciya zuwa girmanta, da ma yadda aka yi ta fara ilimantar da mata ta kafafen sada zumunta game da lafiyar jikinsu duk da cewa furta kalmomin da ke da alaka da al'aura abu ne mai cike da kalubalen a kasar Hausa. Da kuma yadda karshe ta buge da zuwa shirin horar da shugabanci ga matasan Afirka a Amurka da a turance ake kira da Mandela Washington Fellowship da aka fi sani da Young African Leaders Initiative (YALI) na shekarar 2022.

    --- Send in a voice message: https://podcasters.spotify.com/pod/show/usmankabara/message
    Mon, 01 Aug 2022 - 14min
  • 34 - AISHA HASSAN: 'Yar Najeriya da Birtaniya gwanar daurin dan-kwali

    Aisha Hassan matashiya ce 'yar asalin jihar Neja a Najeriya da ta girma a Ingila, sannan ta yi karatu mai zurfi a fannin hada-hadar kasuwanci. Bugu da kari ba a barta a baya ba wajen shiga fagen kafafen sadarwar zamani inda take koyar da salon sa sutura da daurin dan-kwali a shafukanta na yanar gizo. AISHA HASSAN: 'Yar Najeriya da Birtaniya gwanar daurin dan-kwali

    --- Send in a voice message: https://podcasters.spotify.com/pod/show/usmankabara/message
    Mon, 01 Aug 2022 - 30min
  • 33 - SOJABOY: Bahaushen da Amurkawa suka fi sani

    Usman Umar da aka fi sani da SojaBoy mawaki ne, dan wasan kwaikwayon zahirin rayuwa da ya fito a tauraron wani shirin wasan talbijin a Amurka mai suna 90DayFiance wanda ake bibiyar saurayi da budurwa don ganin yadda alakarsu ta soyayya ke tafiya. --- Send in a voice message: https://podcasters.spotify.com/pod/show/usmankabara/message

    Mon, 01 Aug 2022 - 35min
  • 32 - HALIMA ALI SHUWA: ‘Yar Najeriyar da aka karrama a Birtaniya

    An karrama Halima da lambar yabon gama digirin digirgir a matsayin dalibar da ta yi wa sa’o’inta fintinkau a fanni binciken sojojin garkuwar jikin bil’adama. Bugu da kari kuma sai ga wani babban kamfanin hada magunguna a duniya ya bata aiki sakamakon fahimtar amfanin abin da ta kware a fannin binciken kwayar halitta.

    --- Send in a voice message: https://podcasters.spotify.com/pod/show/usmankabara/message
    Fri, 01 Jul 2022 - 1h 11min
Weitere Folgen anzeigen