Nach Genre filtern

ADPlusHausa | Podcast

ADPlusHausa | Podcast

ADPlusHausa | Podcast

Sashen podcast na Afrika 🎙 Fagen tattaunawa…Batutuwa da suka shafi al'adu… Muna bawa mazauna Afrika masu magana da harshen Hausa muhimmanci a dukkan lamuran rayuwarsu…Shiri ne da ke karkashin kafafen sadarwa na Afrika.

84 - 57 | SHIN AURE MAKABATAR SOYAYYA NE? | MAL. LAWAN ADAM GIGINYU
0:00 / 0:00
1x
  • 84 - 57 | SHIN AURE MAKABATAR SOYAYYA NE? | MAL. LAWAN ADAM GIGINYU

    IYALI SU NE GINSHIƘIN AL’UMMA; IDAN GIDA YA GYARU, AL’UMMA MA ZA TA SAMU GYARA.

    GINA IYALI NAGARI BA YA TSAYAWA GA SAMUN KUƊI KO ZAMA TARE KAWAI, A’A, YANA BUƘATAR SOYAYYA, FAHIMTAR JUNA, MUTUNTA JUNA, HAƘURI, AMANA DA KYAKKYAWAR TARBIYYA.

    A YAU ZA MU TATTAUNA MUHIMMAN RUKUNAN DA AKE BUƘATA WAJEN GINA IYALI NAGARI, DA KUMA WASU ƘALUBALEN DA KAN KAWO RASHIN JITUWA TSAKANIN MA’AURATA DA SAURAN ’YAN UWA.

    BABBAN BAƘO: MAL. LAWAN ADAM GIGINYU, MASANIN KIMIYYAR ZAMANTAKEWA A NAKJERIYA.

    MAI GABATARWA: DR. SANI MOUSSA MAGAWATA.

    Sun, 23 Aug 2026 - 3h 40min
  • 83 - 56 | SHIN RASHIN TARBIYYA NE KE RUSHE SHUGABANCI A NAJERIYA DAMA AFRIKA? | PROF. USMAN BUGAJE

    “Shugabanci na Gari a Tsarin Dimokuraɗiyya.” Shugabanci ba mulki kawai ba ne, illa amana ce, nauyi ne, da kuma hidima ga jama'a. A tsarin dimokuraɗiyya, ana bai wa 'yan ƙasa damar zaɓar shugabanninsu, amma tambayar ita ce: ta yaya za mu tabbatar da cewa wannan zaɓe yana haifar da shugabanci mai adalci, gaskiya, amana da bin doka? A yau za mu duba ginshiƙan shugabanci na gari, rawar shugabanni da jama'a, da kuma manyan ƙalubalen da ke hana samun kyakkyawan shugabanci a Najeriya da Afirka.

    Sun, 09 Aug 2026 - 45min
  • 82 - 55 | ZUBA JARI A TSARIN MUSULUNCI DA ABIN DA YA KAMATA KA SANI | DR. NABIL BELLO SA'ID, MD KONOOZ

    A yau mutane da dama suna son su zuba jari domin su ƙara samun kuɗi, amma rashin ilimi yana sa wasu su yi asara ko kuma su faɗa cikin hanyoyin da ba su dace ba.

    A wannan shiri na Rumfar Africa Podcast Hausa, kashi na (55) za mu tattauna muhimman ƙa'idojin da ya kamata kowane mai son zuba jari ya sani, tare da ƙwararren masani a fannin tattalin arziki, zuba jari da Islamic Finance, Dr. Nabil Bello Sa'id, Manajan Darakta na Konooz Investments.

    Ku kasance tare da mu har zuwa ƙarshe, domin wataƙila wannan tattaunawa za ta canja yadda kuke kallon zuba jari baki ɗaya.

    Domin neman karain bayani a Konooz Investments:- +2347063829915 | +2349069968666 | +2349015995200

    Sun, 26 Jul 2026 - 3h 43min
  • 81 - 54 | MATASA DA SON YIN KUƊI A GAGGAUCE: HANYAR ARZIKI KO TARKO? | PROF. MUNIR ABDULLAHI KAMBA

    MATASA DA SON YIN KUƊI A GAGGAUCE: HANYAR ARZIKI KO TARKO?Domin yin nazari a kan wannan batu, muna tare da babban baƙonmu, Farfesa Munir Abdullahi Kamba, wanda zai yi mana bayani kan tushen wannan matsala, illolinta, da kuma hanyoyin da matasa za su bi wajen gina arziki cikin hikima da dorewa.

    Sun, 12 Jul 2026 - 2h 08min
  • 80 - 53 | YAƘI KO SULHU? MAKOMAR RIKICIN IRAN, AMURKA DA ISRA'ILA | DR. RAYA'UDDEEN ZUBAIR MAITAMA

    Shin ana iya warware wannan rikici ta hanyar yaƙi, ko kuwa mafita tana cikin tattaunawa da diflomasiyya?

    -------------------------------------A yau duniya na ci gaba da sa ido kan rikicin da ke tsakanin Iran, Amurka da Isra'ila. Tashin hankali na ƙaruwa, hare-hare na ci gaba, yayin da duniya ke tambayar kanta: Shin wannan rikici zai tsaya a nan, ko kuwa zai rikide zuwa babban yaƙin yanki? Mene ne mafita? Kuma wane tasiri wannan rikici zai iya yi ga tattalin arzikin duniya, tsaron ƙasashe, har ma da rayuwar al'ummar Afirka?

    A wannan shirin na Rumfar Africa Podcast Hausa, za mu yi nazari cikin natsuwa tare da baƙo na musamman domin fahimtar tushen rikicin, matsayinsa a siyasar duniya, da hanyoyin da za su iya kai ga zaman lafiya.

    Sun, 05 Jul 2026 - 3h 45min
Weitere Folgen anzeigen