Filtrar por género

Ilm Lectures Hausa

Ilm Lectures Hausa

IlmQS

Islamic lectures in Hausa language from from world renowned scholars.

26 - Fatawowin Rahama: NASIHA GAME DA ZAƁE - Prof. Sani R/Lemo
0:00 / 0:00
1x
  • 26 - Fatawowin Rahama: NASIHA GAME DA ZAƁE - Prof. Sani R/Lemo

    Fatawoyin Rahma


    Asabar 1 /4/1448 - 12/9/2026


    Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON


    Shimfida : Nasiha ga Al’uma game da Zaɓe da Waɗanda za a Zaɓa!

    Tambayoyi da Amsoshi:


    1. In mutum ya ta shi daga bacci da Asuba, dole sai yayi wanka kafin yayi Sallah?

    2. hukuncin walimar haihuwa!

    3. Direba ya na tuƙa mota sai wani ya buge shi, sanadiyar hatsari ya rasu ( wanda ya dake mai motar)!

    4. Hukuncin ma’akacin da in an aike shi sayo kaya, sai yake ƙara kuɗin akan yadda ya sayi kaya!

    5. Matafiyi zai iya haɗa Sallallin da ake haɗasu yayi su a ƙasaru; sannan in ya je massallacin ya bi liman, ya cika Sallah?

    6. Matafiyi zai iya yin Rawatib!

    7. Mutum da ya yiwa Mace ciki sannan ya aureta daga baya, ɗan da aka samu zai ci gado?

    8. Yaya iddar matar da tayi ɓari bayan kwana biyar da rasuwar mijinta

    9. Wanene maraya a Musulunci

    10. Yaya matsayin wanda bai yi nafila bayan Ɗawafi saboda ba a Sallar nafila bayan La’asar.

    11. Wace irin cuta ce take zama annobar da take ɗaukar hukuncin annoba a sharia!

    Tue, 22 Sep 2026 - 52min
  • 25 - Youth and Challenges of Modern Era - Prof. Bashir Aliyu Umar

    Public Lecture Topic: Youth And The Challanges Of Modern Era


    Tare da

    *Prof. Bashir Aliyu Umar OON*


    Daga Mahmud Tukur New Theatre, Bayaro University, Kano.


    01-4-1448 13-09-2026

    Thu, 17 Sep 2026 - 1h 13min
  • 24 - Fatawowin Rahama: ADDININ MUSULUNCI BAYA KARƁAR BIDI’A - Prof. Sani R/Lemo

    Fatawoyin Rahma


    Ranar Asabar - 23/3/1448H – 5/9/2026


    Tara da Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON


    Shimfiɗa: Addinin Musulunci Ba Ya Karɓar Bidi’a


    Tambayoyi da Amsoshi:


    1. Wanda ya yi Istikhara, amma ya kasa cire son yarinyar da ya yi Istikharar a kanta daga zuciyarsa; menene hukuncin Istikhrarsa?


    2. Hukuncin amfani da fasahar AI wajen ƙirƙirar bidiyo daga hotunan mutane domin sarrafa su.


    3. Hukuncin yawan mafarkin mutuwa ga mace mai juna biyu.


    4. Shin ya halatta mutum ya bawa Makocinsa Kirista aron abin hawa domin zuwa coci?


    5. Mene ne hukuncin bashin da Gwamnatin Najeriya take bin ɗalibi har ya mutu bai samu aiki ba?


    6. Shin ya kamata a yi jam’i na biyu a masallacin da yake da limami Ratibi?


    7. Hukuncin matan da suke cire mayafi a wuraren bukukuwa a gan DJs!


    8. Hukuncin wanda yake fama da lalura, ta yadda duk lokacin da ya yi tsarki sai wani abu ya fito daga gabansa.


    9. Mene ne hukuncin taimaka wa ɗalibai wajen satar amsa don kar su faɗi Jarrabawa?

    Tue, 15 Sep 2026 - 52min
  • 23 - Fatawowin Rahama: Q&A 30-08-2026 - Prof. Sani R/Lemo

    Fatawowin Rahma


    Ranar Lahadi


    17/3/1448 - 30/8/2026


    Tambayoyi tare da Amsoshi tare da *Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON*


    1. Wacce hanya mutum zai bi ya zama ɗalibin ilimin hadisi!


    2. Wanda ya samu raka’a ta ƙarshe a Sallar Magriba, yaya zai kammala Sallarsa?


    3. Hukuncin wanda ya rikice ya kasa tuna raka’a nawa yayi?


    4. Lamarin wadda in za ta yi Sallah sai ta ji kamar wani abu zai faɗo mata?


    5. Hukuncin mutuwa a wurare masu falala?


    6. Laifin wanda ya taimaka wajen zubar da ciki dai dai yake da wanda ya kashe wanda aka haifa?


    7. Mutum zai iya yafewa wanda yake bi bashi da ya mutu ba sai ya fadawa iyalan mamacin ba?


    8. Ya hallata mutum yayi sadaqa ga iyayensa da suka rasu!


    9. Yaya mutum zai sa riba ga kayan da yake sayarwa!


    10. Idan aka gina coci a Fili ba tare da izininsa mai filin ba, yaya magada za su yi?


    11. Sallar ƙasaru ga matafiyi!


    12. In mutum zai cutu a hanyar sa ta zuwa massallaci, zai iya Sallah a gida sannan kuma ya samu ladan wanda ya je massallaci?


    13. Mamu zai iya ƙin bin liman da ya hada Sallah in mamun yana ganin sharuɗɗan haɗa sallolin ba su cika ba?


    14. Yaya hukuncin Tela da yake aiki a shagon da wutar lantarki da aka janyo zuwa shagon ta sata ce?


    15. Akwai addu’ar rufe gida ko daki?


    16. Ana iya tofi da shafawa yaro yayin yi masa addu’a safe da yamma?


    17. Mace za ita iya Sallah da zani da hijabi da ya rufe jikinta, ko da bata da riga?


    18.kashin kaji najasa ne?


    19. Hukuncin mutumin da aka bawa bashi da riba amma yake musun haka?


    20. Hukuncin Wucewa gaban mamu ta kofar da aka bar ta a bude domin wucewar mutane!


    21. Mace za ta iya Sujjadar Tilawa ba tare da hijabi ba?


    22. Mutum zai iya azumin domin ya samu lada sannan ya rage kiba?


    23. Mutumin da yayi alwala, yayi Azkar din bacci sannan ya sadu da iyalansa, sai ya sake Azkar?


    24. Mutumin da yake Sallar dare, an ina ya kamata yayi addu’oinsa?


    25. Yaya ya kamata musulmi ya gaishe da manya?


    26. Akwai hadisin da ya ce za a fara sahu daga tsakiyar sahu?

    Thu, 10 Sep 2026 - 52min
  • 22 - Fatawowin Rahama: BACIN AQIDAR ‘HUMANITY’ - Prof. Sani R/Lemo

    FATAWOYIN RAHMA


    Ranar Asabar


    16/3/1448H – 29/8/2026


    _Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON_


    Shimfiɗa – ```Bacin Aqidar “Humanity”``


    Tambayoyi da Amsoshi -


    1. Menene hukuncin neman ruwa daga wurin wanda ba Musulmi ba domin yin alwala.


    2. Shin mutum zai iya yin addu’a a Tahiya ta farko?


    3. Menene matsayin addu’ar da ake yi bayan Tahiya?


    4. Menene hukuncin fitar maziyyi ga mai azumi?


    5. Mutumin da ya samu sallar jana’iza bayan an riga an yi kabbara ta farko ko ta biyu, daga wace kabbara zai shiga cikin sallar?


    6. Menene hukuncin matafiyin da ya haɗa Sallar Azahar da La’asar a lokacin Sallar Azahar?


    7. Menene hukuncin matafiyin da bai yi Sallar Azahar a ƙasaru ba har sai da ya dawo gida a lokacin Sallar La’asar? Shin zai yi Sallar Azahar a ƙasaru ne ko cikawa zai yi?


    8. Mutumin da ya karɓi kuɗin ɗan’uwansa, bayan rasuwarsa, shin zai iya amfani da waɗannan kuɗaɗen wajen hidima ga iyalinsa, bisa hujjar cewa yana mayar da haƙƙin mamaci!


    9. Menene hukuncin mutumin da yake karɓar albasa daga wanda suke zama tare, wani lokaci ya mayar, wani lokaci kuma ba ya mayarwa?


    10. Menene hukuncin mutumin da yake yin Sallah a cikin shagonsa, kuma ba ya zuwa Sallar Jam’i?

    Tue, 08 Sep 2026 - 52min
Mostrar más episodios