Filtrar por género
Najeriya a Yau

- 958 - Halin Kunci Da Matan Da Aka Yi Garkuwa Da Su Ke Tsintar Kansu A Ciki
Send us Fan Mail So da yawa matan da aka yi garkuwa dasu kan shiga halin kunci ko da bayan sun kubuta. Yayin da kadan daga cikinsu ke komawa gudanar da rayuwarsu yadda ta kamata, wasu da dama kan tsinci kansu cikin halin damuwa da tagayyara. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokacin ya yi duba ne kan wannan batu da irin shawarwarin da za a basu don fita daga irin wannan kangi.
Fri, 15 May 2026 - 957 - Yadda Wasu Al'ummomi Suke Kare Kansu Daga Ambaliyar Ruwa
Send us Fan Mail Ambaliyar ruwa na cigaba da salwantar da dukiyoyi da rayukan al’ummomi da dama a sassa daban-daban na Najeriya. Ko a farkon makon nan, hukumomi sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar samun ambaliyar a jihohi akalla 11. Sai dai wasu alummomin tuni suka dauki matakai don rage barnar da ambaliyar ka iya yi musu. A kan wadannan matakai shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari.
Thu, 14 May 2026 - 956 - Yadda Talauci Ke Hana Shayar Da Yara Nonon Uwa Zalla A Najeriya
Send us Fan Mail Ga alama kwalliya ba ta biyan kudin sabulu a fafautukar da ake yi ta ganin iyaye mata sun shayar da jariransu nono Zalla a wata shida na farko. Rahotanni sun ce duk da dadewar da aka yi ana wayar da kai har yanzu matan da suke shayar da yara nono uwa Zalla ba su haura kashi 29 cikin dari ba. Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suke hana mata shayar da ‘ya’yan su nono zalla na watanni shida.
Fri, 08 May 2026 - 955 - ''Yadda Cutar Amosanin Jini Ta Hana Ni Cimma Buri Na''
Send us Fan Mail Cutar amosanin jini wacce aka fi sani da cutar sikila na cigaba da barazana ga rayukan masu dauke da ita. Wannan cuta na saka masu ita da ‘yan uwan su cikin halin ha’ula’i, a wasu lokutan ma tana haifar da rasa rayukan wasu dake dauke da ita. Rahotannin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun nuna cewa, kusan yara 300,000 ne ake haifa da cutar Sikila a duk shekara a fadin duniya, inda yankin Kudu da Sahara a Afirka ke dauke da kashi 75% na wannan yawan. A ...
Thu, 07 May 2026 - 954 - Yadda Raguwar Maniyyatan Najeriya Ke Tasiri Ga Aikin Hajji
Send us Fan Mail A kwanakin nan ana samun raguwar kujerun maniyyata aikin Hajji daga Najeriya, abin da ya jawo fargaba ga masu shirin zuwa kasa mai tsarki da kuma masu hidimar su. A da, Najeriya na samun kujeru sama da dubu casa’in daga gwamnatin Saudiyya, amma cikin shekaru kadan da suka gabata adadin ya ragu zuwa kusan dubu sittin da biyar. Ko yaya kara raguwar kujerun maniyyatan Najeriya ke kara tasiri ga Najeriya? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan ...
Tue, 28 Apr 2026 - 953 - Matsalolin Da Suke Tarnaki Ga Kananan Yara A Najeriya Da Hanyoyin Magance Su
Send us Fan Mail Najeriya tana cikin ƙasashen da suka fi yawan yara a duniya, a cewar Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF). Sai dai a cewar Hukumar ta UNICEF, kusan rabin wadannan yara suna fuskantar kalubale, kama daga cin zarafi zuwa rashin samun kulawa da dai sauran su. Wadannan matsaloli da yara suke fuskanta dai sun dade suna ci wa masu ruwa da tsaki tuwo a kwarya. Yayin da ake bikin Ranar Yara, shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi...
Mon, 27 Apr 2026 - 952 - Yawan Kudaden Da Ake Bukata Wajen Samar Da 'Yan Sandan Jihohi
Send us Fan Mail Batun samar da ‘yansandan jihohi na ƙara ɗaukar hankalin ‘yan Najeriya, musamman a dai-dai lokacin da matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a sassa daban-daban na ƙasar nan. Sai dai, samar da ‘yansandan jihohi ba abu ne mai sauƙi Kamar yadda wasu ke tunani ba. Gwamnatocin jihohi na buƙatar abubuwa masu yawa kafin su iya ɗaukar wannan nauyi, banda batun samar da dokar samar da wadannan ‘yansanda, akwai batun samar da kayan aiki da horo da sauran abubuwa da ake bukata d...
Tue, 21 Apr 2026 - 951 - ‘Halin Kunci Ya Sa Muke Zama A Baca A Abuja’
Send us Fan Mail Halin matsin tattalin arziki ya tilasta da yawa daga cikin mutane zama a bacoci a garin Abuja da wasu biranen Najeriya. Mutane a birane kamar Abuja da Legas Da Fatakwal na cikin halin matsi sakamakon rashin ingattaccen muhalli. Ko wannen irin rayuwa irin wadannan mutanen ke yi? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai a yau da ake bikin ranar muhalli ta duniya.
Fri, 17 Apr 2026 - 950 - Yadda Ake Juya Ababen Hawa Zuwa Masu Amfani Da CNG
Send us Fan Mail Galibin ’yan Najeriya ba su san amfanin da sauya ababen hawansu daga masu amfani da man fetur zuwa masu amfani da iskar gas ta CNG ke da shi ba, musamman a wannan lokaci da ake fama da tsadar man fetur. ’Yan Najeriya da dama dai suna amfani da man fetur ne saboda karancin wuraren sauya ababen hawan da sauran dalilai. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kan irin abubuwan da ya kamata ’yan Najeriya, musamman m...
Thu, 16 Apr 2026 - 949 - Abun Da Ya Sa Matan Arewa Ke Gujewa Karantar Ilimin Kimiyya
Send us Fan Mail Mata a Arewacin Najeriya na fuskantar kalubale da dama a fannin karantar kimiyya. Akwai darussan da a mafi yawan lokuta ba mata kadai ba, har da mazan na kaurace musu. Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari ne kan dalilan da suka sa matan Arewacin Najeriya ke tsoron karantar ilimin kimiyya.
Tue, 14 Apr 2026 - 948 - Ko Wa'adi Daya Ya Isa Wanda Aka Zaba Cika Alkawuran Da Ya Dauka?
Send us Fan Mail Duk bayan shekaru hudu, Najeriya na kara yin zabe kuma ko wanne lokaci 'yan takara kan dauki alkawurika. Ko shekaru nawa wadanda ake zabe ke bukata don cika alkawuran da suka dauka? wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Fri, 10 Apr 2026 - 947 - Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Da Aka Canzawa Halitta GMO
Send us Fan Mail Alamu na nuna cewa galibin manoma a Najeriya suna da shakku a kan amfani da irin da aka sauya ƙwayoyin halittarsa. Hakan dai na faruwa ne duk da bayanan da wasu masana suka yi game da alfanun wannan iri wanda ake kira GMO ko Genetically Modified Organism a turance. Tuni dai wasu masanan, waɗanda suka shirya wani taron bita ga manema labarai, suka yi gargaɗi game da illolin irin. Ko mece ce gaskiya game da amfani da wannan iri na GMO?
Thu, 09 Apr 2026 - 946 - Shin Ya Kamata A Samar Da Dokokin Da Za Su Sa Ido Kan Amfani Da AI?
Send us Fan Mail Tun bayan bayyanar kirkirarrriyar basira wato AI ne dai wasu mutane suke amfani da ita ta hanyar da da bai kamata ba. Wasu sukan yi amfani da ita wajen saka hoto ko kirkirar faifan bidiyo wanda zai nuna wani yana yin abun da bai kamata ba. Hakan dai ya sa wasu suna ganin ya kamata a samar da dokokin da za su rinka lura da yadda ake amfani da kirkirarriyar basirar. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan dacewar sanya doka gane da yadd...
Tue, 07 Apr 2026 - 945 - Yadda Masu Yi Wa Kasa Hidima Za Su Ci Arzikin Yankunan Da Suke AIki
Send us Fan Mail Bayan hadin kai da karfafa fahimtar juna wadanda hidimar kasa take kawowa, akan samu wasu masu hidimar da sukan yi amfani da duk wata dama da suka samu don neman na sakawa a bakin salati. Yayin da wasu masu hidimar kasa sukan kama sana’a ko su saka hannun jari a inda aka tura su, wasu kuwa komawa garuruwansu suke yi bayan sun kammala. Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan irin damar da masu yi wa kasa hidima suke da ita a garuruwan da aka...
Thu, 02 Apr 2026 - 944 - Yadda Matasa Ke Bada Gudunmawar Cigaban Al’ummarsu
Send us Fan Mail Samun matasan dake bada gudunmawa a alummomin da suke rayuwa a cikin ta yana da matukar wuya a wannan zamani. Amma duk da haka, wasu matasa sun sadaukar da rayuwarsu wajen bada gudunmawarsu wajen cigaban alummarsu. Shirin Najeirya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan irin gudunmawar da matasa ke badawa wajen cigaban alummarsu
Fri, 27 Mar 2026 - 943 - Yadda Na Rasa 'Ya'ya Na Ga Guban Abinci
Send us Fan Mail Cin guba ta hanyar abinci (food poisoning) wata cuta ce da ke faruwa idan mutum ya ci abinci ko ya sha abin sha da ya gurɓace. Gurɓacewar abincin na iya fitowa daga ƙwayoyin cuta kamar Salmonella, E. coli, ko Listeria, ko kuma daga ƙwayoyin cutar virus, ƙwari (parasites), ko sinadarai masu guba. Alamomin cutar sun haɗa da ciwon ciki, amai, zazzabi, gudawa, da rashin jin daɗin jiki. A wasu lokuta masu tsanani, cutar na iya kai mutum asibiti ko ta yi barazana ga rayuwa, ...
Thu, 26 Mar 2026 - 942 - Daga Alkawari Zuwa Mulki, Yadda Siyasa Ke Sauya Manufa
Send us Fan Mail Duk bayan shekaru hudu, Najeriya na kara yin zabe kuma ko wanne lokaci 'yan takara kan dauki alkawurika. Ko shekaru nawa wadanda ake zabe ke bukata don cika alkawuran da suka dauka? wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Tue, 24 Mar 2026 - 941 - Abubuwan Da Za Su Kwadaita Muku Azumtar Sitta Shawwal
Send us Fan Mail Alqurani mai girma a cikin suratul Baqarah Allah ya wajabta wa musulmi da suka cika wasu sharudda azumtar watan Ramadana. Kamar yadda malamai suka sha fadi, wannan wata na dauke da wasu falala maras misaltuwa da bawa kan samu idan ya maida kai wajen ibada don samun rabauta daga ubangiji. Kazalika hadisai sun ruwaito kan falalar azumtar kwanaki shidda na watan shawwal, watan dake biye da Ramadan. Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan falalar dake akwai ...
Mon, 23 Mar 2026 - 940 - Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi?
Send us Fan Mail Ko kun san sunan dabinon da kuka fi so ku ci a lokacin shan ruwa? Dan Agadas ne, ko Ruwa-Ruwa, ko Annakhiyl? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai ya yi nazari ne kan nau’ukan dabino da alfanunsa ga dan’Adam, musamman mai azumi.
Fri, 13 Mar 2026 - 939 - Kalubalen Dake Tattare Da Samar Da ‘Yansandan Jihohi A Najeriya
Send us Fan Mail Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sha nanata muhimmancin samar da ’yan sandan jihohi a Nigeria, yana mai cewa hakan na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar sassa daban-daban na kasar. Shugaban ya bayyana cewa tsarin ’yan sanda da ke karkashin gwamnatin tarayya kadai ba zai iya biyan bukatun tsaro na kasa mai yawan jama’a da fadi kamar Najeriya ba. A wani mataki na ci gaba da duba yiwuwar aiwatar da wannan tsari, Sufeto Janar na ...
Fri, 06 Mar 2026 - 938 - Yadda Cutar Zazzabin Lassa Ke Kisa Da Hanyoyin dakile Ta
Send us Fan Mail A yayin da Najeriya ke fuskantar kalubale daban-daban a fannin lafiya, cutar zazzabin Lassa ta sake ɗaga kai a wasu jihohin ƙasar. Cutar wadda ake dangantawa da berayen da ke ɗauke da ƙwayar cutar, tana yawaita ne musamman a lokutan sanyi zuwa farkon damina, lamarin da ke jefa al’umma cikin fargaba a kowace shekara. Rahotanni daga hukumar dake hana yaduwar cututtuka ta Najeriya sun nuna cewa tun daga farkon shekarar 2026, an samu daruruwan mutane da suka kamu da cutar a jihoh...
Thu, 05 Mar 2026 - 937 - Yadda Ake Kamuwa Da Basir Da Hanyoyin Magance Ta
Send us Fan Mail Cutar basir na daga cikin cututtukan da mutane da dama ke da mabanbantan ra’ayoyi akan ta. A lokuta da dama za ka ji yadda mutane ke fadin dalilai daban daban da ke janyo cutar basir, yayin da wasu ke ganin yawan zama ne ke kawo ta, wasu kuwa gani suke yi zaki da maiko ne ke kawo ta. Wannan shine abun da da yawa daga cikin mutane suka sani kan wannan cuta, sai dai masana kiwon lafiya na da nasu fahimtar daban kan wannan cuta. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai t...
Wed, 04 Mar 2026 - 936 - Yadda Azumi Ke Inganta Lafiyar Jiki
Send us Fan Mail Alumma na yin azumi ne bisa dalilan addini don samun lada kamar yadda Allah ya umurta a cikin Qurani mai girma. Sai dai daga baya binciken masana kimiyya ya gano cewa bayan lada da ake samu daga yin azumi, akwai wasu alfanu da mai azumi ke samu ga lafiyar jikin shi da suka hada da inganta karfi da zurfin tunani zuwa fitar da gurbatattun abubuwa da jiki baya bukata. A takaice dai, ba kawai lada mai azumi ke samu ba, har da samun lafiyar jiki da na kwakwalwar sa. ...
Tue, 03 Mar 2026 - 935 - Falalar Bude Baki Cikin Iyali A Lokacin Azumi
Send us Fan Mail Hadisi ya tabbatar da yadda cin abinci tare yake kara dankon zumunci da kaunar juna da albarka a tsakanin al’umma. Mai yiwuwa wannan ne ya sa akan samu Karin kusanci da shakuwa a tsakanin duk iyalan da kan zauna su ci abinci. Ko kafin watan azumi dai, wasu magidantan kan mayar da cin abinci tare da tare da iyalin su al’ada. Shin ko mene ne matsayin bude-baki tare da iyali a watan Ramadana? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan iri...
Fri, 27 Feb 2026 - 934 - Me Nadin Sabon Sufeton 'Yansanda Ke Nufi Ga Tsaron Cikin Gida Najeriya?
Send us Fan Mail Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa sabon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP), matakin da ya sake jawo hankalin al’umma kan makomar tsaro da gyaran harkokin rundunar ‘yan sandan ƙasar nan. Naɗin sabon jagoran rundunar ya zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar ƙalubale daban-daban na tsaro, ciki har da satar mutane, ta’addanci, da rikice-rikicen cikin gida a wasu sassan ƙasa. Sabon Sufeton ana sa ran zai ɗora kan nasarorin da aka samu a baya tare da kawo sababbin tsare-t...
Thu, 26 Feb 2026 - 933 - Shin Da Gaske An Fara Samun Ɓaraka Tsakanin Atiku Abubakar Da Peter Obi A Tafiyar ADC?
Send us Fan Mail Rahotanni daga sassa daban-daban na siyasar Najeriya na nuna cewa ana fara samun ɓaraka a tsakanin manyan jiga-jigan haɗakar tafiyar ADC, musamman tsakanin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi. Ko da yake har yanzu babu wata sanarwa ta hukuma da ke tabbatar da wannan saɓani, majiyoyi na nuni da cewa sabanin ra’ayi kan jagoranci, tsarin tafiya, da kuma makomar zaɓen 2027 na iya zama tushe...
Tue, 24 Feb 2026 - 932 - Falalar Sallan Tarawih Ga Alummar Musulmi A Watan Ramadan
Send us Fan Mail A duk lokacin da watan azumin Ramadan ya kama, al’ummar Musulmi kan cika masallatai domin gudanar da sallar Tarawihi cikin karsashi da himma. A kwanakin farko, ana ganin sahu sun cika, zuciya cike da nishadi da kwadayin lada. Sai dai abin takaici, bayan wasu kwanaki, wasu kan fara ja da baya — wani saboda gajiya, wani saboda shagaltuwa da harkokin yau da kullum, ko kuma rashin juriya. Wannan yanayi na nuna bukatar tunatarwa kan muhimmanci da falalar sallar Tarawihi, domin i...
Fri, 20 Feb 2026 - 931 - Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta
Send us Fan Mail Cututtuka da dama suna Kamari a Najeriya wanda a mafi yawancin lokuta ma wadanda ke dauke da irin wadannan cututtukan basu da masaniyar suna dauke da su. Kamar yadda majalisar dinkin duniya ta bayyana, zaman lafiya, rashin matsalar kwakwalwa, da samun wadata na daga cikin abubuwan dake tabbatar da lafiyar bil’adama. Wata cuta da ta addabi da yawa daga cikin al’umma itace cutar Hawan jini wacce take daya daga cututtuakan dake sanadiyyar mutuwar akalla mutum miliy...
Thu, 19 Feb 2026 - 930 - Yadda Masu Larurar Ulcer Za Su Gudanar Da Azumin Ramadan Ba Tare Da Matsala Ba
Send us Fan Mail A duk lokacin da watan azumi ya zo, Musulmai da dama sukan karɓe shi da murna da shauƙi, suna shirya ibada da ƙara kusanci da Allah. Sai dai ga wasu, musamman masu fama da larurar gyambon ciki wato ulcer, watan azumi kan zo da wani yanayi na damuwa da fargaba. Yayin da wasu ke jin daɗin azumi, su kuma suna cikin ƙalubalen yadda za su iya jure yunwa da ƙishirwa ba tare da cutar ta tashi ko ta jawo musu matsananciyar wahala ba. Ciwon ulcer na haddasa zafi a ciki, tashin zuciy...
Tue, 17 Feb 2026 - 929 - Yadda Muka Yi Asarar Miliyoyin Naira A Kasuwar Singa Muna Ji Muna Gani
Send us Fan Mail ‘Yan kasuwa da dama a jihar Kano sun kwana sun tashi da juyayi da alhinin gobara da ta faru ta kuma lashe musu dimbin dukiyarsu suna ji suna gani ba tare da sun iya tabuka komai ba. Gobarar da ta tashi a kasuwar singa dake jihar Kano, ta fara ne da misalin karfe 4:30 na ranar asabar ta kuma cigaba da ci har zuwa wayewar garin ranar lahadi. Wannan gobara ta yi sanadiyyar raba ‘yan kasuwa da dama da hanyar cin abincin su, inda ta jefa su da iyalansu cikin halin kunci. Ko wa...
Mon, 16 Feb 2026 - 928 - Ya Kamata Najeriya Ta Samar da Dokoki Kan Amfani da AI?
Send us Fan Mail Tun bayan bayyanar kirkirarrriyar basira wato AI ne dai wasu mutane suke amfani da ita ta hanyar da da bai kamata ba. Wasu sukan yi amfani da ita wajen saka hoto ko kirkirar faifan bidiyo wanda zai nuna wani yana yin abun da bai kamata ba. Hakan dai ya sa wasu suna ganin ya kamata a samar da dokokin da za su rinka lura da yadda ake amfani da kirkirarriyar basirar. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan dacewar sanya doka game da yadd...
Fri, 13 Feb 2026 - 927 - Hanyoyin Magance Laifukan Da Matasa Ke Aikatawa A Cikin Al'umma
Send us Fan Mail Masu iya magana kan ce banza ba ta kai zomo kasuwa. In ba haka ba, me ya kai matasan da ake zargi da aikata manyan laifuffuka ofishin ’yan sanda, suka kuma fit oba tare da wani ya harae su ko ya yi mutsu tsawa ba, balle ya saka su a cell? ’Yan sandan dai sun ce wannan wata dabara ce ta yakar aikata manyan laifuka irin su sata da fashi da makami da kwacen waya da fyade kai har ma da satar mutane don kudin fansa a tsakanin matasa. Ko yaya wannan dabara take aiki? ...
Thu, 12 Feb 2026 - 926 - Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Samun Wadataccen Abinci
Send us Fan Mail A wannan zamani, ’yan Najeriya da dama ba sa samun wadataccen abinci a yini. Magidanta da dama, musamman, sun tsallake sun bar iyalansu sun shiga bariki don neman na sanyawa a bakin salati. Mene ne dalilin hakan, kuma yaya za a yi a kauce wa fadawa cikin irin wannan yanayi? Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan halin da galibin ’yan Najeriya suka tsinci kansu a ciki na rashin samun abinci yadda ya kamata
Tue, 10 Feb 2026 - 925 - Dabarun Bunkasa Kasuwanci A Intanet
Send us Fan Mail Masu iya magana kan ce “zamani riga”. Sauyin zamani ya kawo sauye-sauye da dama a yadda ake gudanar da harkoki, ciki har da kasuwanci. A yanzu haka, zamani, intanet na taka muhimmiyar rawa wajen tallata haja ko saye da sayarwa. Shrin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan dabarun da za ku iya amfani da su don bunkasa kasuwancinku ta hanyar amfani da intanet.
Mon, 09 Feb 2026 - 924 - Tasirin Yankan Al’aura A Rayuwar 'Ya'ya Mata
Send us Fan Mail A tsakanin al’ummomi daban-daban akan samu wasu al’adu na yanke wani bangare na al’aurar ’ya’ya mata saboda wasu dalilai. A kasar Hausa akan yi abin da ake kira yankan angurya da nufin rage wa mace sha’awa, musamman kafin ta yi aure. Ko menene tasirin wannan al’ada a rayuwar ’ya’ya mata? Albarkacin Ranar Yaki da Yankan Al’aurar Mata ta Duniya, shirin Najeriya A Yau zai yi nazari a kan wannan batu.
Fri, 06 Feb 2026 - 923 - Hanyoyin Mallakar Gida Ga Mai Karamin Karfi
Send us Fan Mail Mallakar muhalli na cikin burace-buracen kusan kowanne dan Najeriya. Sai dai wadannan burace-burace, a galibin lokuta, ba sa cika – musamman ga masu matsakaitan samu. Amma wasu masana suna ganin akwai dabarun da marasa karfi ma za su iya amfani da su don su mallaki nasu muhallin, daidai ruwa daidai tsaki. A kan wadannan dabaru shirin Najeriya A Yau zai yi nazari..
Thu, 05 Feb 2026 - 922 - Abin Da Ya Kamata Ku Yi Yayin Takaddama Da ’Yan Sanda
Send us Fan Mail Babban alhakin da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya dora wa Rundunar ’Yan Sanda shi ne kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa. Sai dai a lokuta da dama, akan samu fito-na-fito sakamakon zargin ’yan sanda da wuce gona da iri wajen gudanar da aiyyukan nasu. Shirin Najeriya a Yau ya tattauna a kan yadda abubuwan da ya kamata ’yan kasa su yi idan ’yan sanda suka nemi cin zalinsu.
Tue, 03 Feb 2026 - 921 - Rayuwar Mazan Da Ba Sa Haihuwa
Send us Fan Mail Rashin haihuwa matsala ce da ka iya wargaza gidajen aure musamman a wannan zamani. Da an samu shekara biyu zuwa uku bayan an daura aure ba tare da an samu karuwa ba za a fara yamadidi da matar a kan ba ta haihuwa. Sai dai likitoci sun ce maza ma ka iya fama da wannan larura saboda wasu dalilai. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan wadannan matsalolin da suke hana maza haihuwa.
Mon, 02 Feb 2026 - 920 - Radadin da masu amosanin jini suke shaWed, 28 Jan 2026
- 919 - Inda Aka Mike Da Inda Aka Kauce Tun Bayan Dawowa Mulkin Dimokuraɗiyya A Jamhuriya Ta Hudu
Send us Fan Mail Kamfanin yaɗa labarai na Media Trust ya daɗe yana taka muhimmiyar rawa wajen buɗe tattaunawa masu ma’ana kan manyan al’amuran da suka shafi tafiyar da ƙasa da dimokuraɗiyya a Najeriya. Daga cikin fitattun shirye-shiryensa akwai muhawarar shekara-shekara da kamfanin ke shirya wa, wadda ta zama wani dandali na musamman da ke haɗa masana, ‘yan siyasa, masana doka, da masu ruwa da tsaki domin nazari da tantance halin da ƙasa ke ciki. A bana, wannan muhawara ta kai karo na 23, i...
Fri, 23 Jan 2026 - 918 - Nasarori Da Kalubalen Da Bankin Musulunci ke Fuskanta A Najeriya
Send us Fan Mail A Jamhuriya ta Hudu a Najeriya, wadda ta fara a shekarar 1999, an samu sauye-sauye masu yawa a bangaren tattalin arziki da harkokin kuɗi, ciki har da tasowar bankunan Musulunci. Wannan tsari na banki ya samo asali ne daga buƙatar samar da hanyoyin mu’amala da kuɗi da suka dace da koyarwar addinin Musulunci, wato hanyoyin da ba su ƙunshi riba, da zamba, ko rashin tabbas ba. A farkon lokaci, ra’ayin kafa bankunan Musulunci ya fuskanci muhawara da adawa daga wasu ɓangaror...
Tue, 09 Jun 2026 - 917 - Tasirin Siyasar Matasa A Najeriya Tun Bayan Dawowar Jamhuriya Ta Hudu
Send us Fan Mail Shekaru kafin a sanya hannu kan dokar Not Too Young To Run, siyasar matasa a Najeriya na fuskantar ƙalubale masu tarin yawa. Duk da cewa matasa su ne mafi rinjaye a yawan al’umma da kuma masu katin zaɓe, an dade ana kallonsu ne a matsayin masu ɗaukar tutoci, da yaɗa saƙonni ko kuma masu tayar da tarzoma a lokacin zaɓe, ba tare da ba su cikakkiyar dama ta tsayawa takara ko shiga manyan matakan yanke shawara ba. Sai dai a shekarar 2018, bayan sa hannu kan dokar bai wa matasa ...
Tue, 20 Jan 2026 - 916 - Yadda Siyasar Ubangida Ta Yi Tasiri Ga Siyasar Najeriya A Jamhuriya Ta Hudu
Send us Fan Mail Tun bayan dawowar mulkin farar hula a shekarar 1999, siyasar Najeriya ta kasance karkashin inuwar wasu ’yan tsiraru da ake kira iyayen gidan siyasa. Wannan tsari ya ginu ne a kan karfin mutum guda ko rukuni, inda su ke rike da makullin jam’iyya, su tsara wa’adi, su zabi ’yan takara, su kuma yanke hukunci ba tare da la’akari da ra’ayin mafi yawan mambobi ko jama’a ba. A Jamhuriya ta Hudu, siyasar ubangida ta zama tamkar al’ada da aka amince da ita, inda dimokuraɗiyya ta haki...
Mon, 19 Jan 2026 - 915 - Untitled EpisodeSat, 17 Jan 2026
- 914 - Abun Koyin ‘Yan Siyasa Da Matasa Kan Jarumtar Goodluck Jonathan A 2015
Send us Fan Mail Kiran wayan da tsohon Shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya yi wa marigayi Muhammadu Buhari ta bar tarihi mai muhimmanci a Najeriya. Waya da ta kwantar da hankalin kasa, ta kuma dakatar da fargabar tashin hankali. A ranar da sakamakon zaben shekarar 2015 ya fara bayyana, tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Ebele Jonathan, ya zabi zaman lafiya a kan mulki, ya kuma zabi Najeriya a kan kansa. Maimakon ya tada jijiyar wuya, ko ya kalubalanci sakamakon da zai iya haddasa rik...
Fri, 16 Jan 2026 - 913 - Bayan Shekaru Sittin, Me Ya Sa Har Yanzu Ake Tunawa Da Su Sardauna?
Send us Fan Mail A tarihin kowace ƙasa, akwai wasu mutane da ba lokaci ko sauyin zamani ke iya gogewa daga ƙwaƙwalwar al’umma ba. A Najeriya, waɗannan su ne founding fathers — jagororin da suka tsaya tsayin daka wajen jagorantar gwagwarmayar neman ’yancin kai, kafa tubalan dimokuraɗiyya, da shimfiɗa tsarin ƙasa tun kafin a haifi Jamhuriyar Tarayya ta Najeriya. Gudunmawarsu ba ta tsaya kawai ga siyasa ba; sun bayar da rayuwarsu, tunaninsu domin tabbatar da cewa Najeriya ta zama ƙasa mai cikakk...
Thu, 15 Jan 2026 - 912 - Zabukan Da Aka Gudanar Lokacin Dawowar Mulkin Farar Hula A Jamhuriya Ta Hudu
Send us Fan Mail Bayan kusan shekaru goma sha shida na mulkin soja, Najeriya ta dawo kan tafarkin mulkin farar hula a shekarar 1999, abin da ya buɗe sabon babi a tarihin siyasar ƙasar. Zaɓen da aka gudanar a wannan lokaci shi ne zaɓen farko na Jamhuriya ta Huɗu, inda aka gudanar da zaɓukan kananan hukumomi, majalisun dokoki, gwamnoni da kuma shugaban ƙasa a ƙarƙashin kulawar Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, wato INEC. Duk da cike da ƙalubale kamar ƙarancin kayan aiki, rashin cikakken shiri, zarge-zarg...
Tue, 13 Jan 2026 - 911 - Waiwaye Kan Yadda Jam’iyyun Siyasa Suka Kafu A Jamhuriya Ta Hudu
Send us Fan Mail Jamhuriya ta Huɗu a Najeriya ta fara ne a ranar 29 ga Mayu, 1999, bayan kawo ƙarshen mulkin soja, inda ƙasar ta koma tafarkin dimokuraɗiyya bisa Kundin Tsarin Mulki na 1999. A wannan lokaci ne aka kafa manyan jam’iyyun siyasa kamar PDP, wadda Alex Ekwueme, Solomon Lar da wasu tsofaffin ‘yan siyasa suka jagoranci kafuwarta; APP (daga baya ANPP) ƙarƙashin jagorancin Mahmud Waziri da Abubakar Rimi; da kuma AD, wadda Bola Ige da Abraham Adesanya suka jagoranta, musamman daga yank...
Mon, 12 Jan 2026 - 910 - Lokacin Da Ya Kamata A Fara Yakin Neman Zaben 2027
Send us Fan Mail A siyasar Najeriya, akwai ka’idoji da dokoki da ke tsara yadda ake gudanar da zaɓe, ciki har da lokacin da doka ta amince a fara yaƙin neman zaɓe. Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, wato INEC, ita ce ke da alhakin bayyana jadawalin zaɓe da kuma ranar da ‘yan takara za su fara neman goyon bayan al’umma a hukumance. Sai dai duk da waɗannan tanade-tanade, ana ci gaba da ganin alamu da ayyuka da ke nuna cewa wasu ‘yan takara suna fara yaƙin neman zaɓe tun kafin a buga gangar siyasa. Wa...
Thu, 08 Jan 2026 - 909 - Yaya Matsayar Katsalandar Din Da APC Tace Nyesom Wike Na Yi A Jam’iyyar?
Send us Fan Mail A cikin ‘yan kwanakin nan, siyasar Najeriya ta sake daukar sabon salo, bayan barkewar takaddama tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, da manyan shugabannin jam’iyyar (APC). Jam’iyyar APC na kallon yadda Wike — wanda ba cikakken ɗan jam’iyyar ba ne amma ke rike da mukami a karkashin gwamnatinta — ke yin katsalandan a harkokin jam’iyyar, musamman a matakin jihohi, a matsayin barazana ga tsarin jam’iyya da ikonta na cikin gida. Wannan lamari ya haifar da ...
Wed, 07 Jan 2026 - 908 - Yadda ‘Yan Bindiga Suka Yanka ‘Yan Kasuwa A Jihar Neja
Send us Fan Mail Harin da wasu ‘yan ta’adda suka kai kasuwar Daji da ke karamar hukumar Borgu a Jihar Neja ya sake jawo hankalin al’umma kan matsalar rashin tsaro da ke kara ta’azzara a yankunan karkara na Arewa ta Tsakiya. Kasuwar Daji, wadda ke zama cibiyar hada-hadar kasuwanci ga manoma, ‘yan kasuwa da mazauna kauyuka makwabta, ta kasance wuri na zaman lafiya kafin wannan mummunan lamari da ya girgiza mazauna yankin. Batutuwa da dama daga kafafen yada labarai da dama sun bayyana mabanban...
Tue, 06 Jan 2026 - 907 - Sharuddan Da Jam'iyya Za Ta Cika Kafin A Kira Ta Babbar Jam'iyyar Adawa
Send us Fan Mail A fagen siyasar Najeriya a halin yanzu, ana ta ce-ce-ku-ce kan wacce ce babbar jam’iyyar adawa da za ta iya tsayawa ƙafada da ƙafada da jam’iyyar APC mai mulki. Wannan takaddama ta fi karkata ne tsakanin jam’iyyar PDP, wacce ta dade tana taka rawa a matsayin babbar jam’iyyar adawa bayan ficewarta daga mulki a 2015, da kuma jam’iyyar ADC, wacce a ‘yan shekarun nan ta fara samun karɓuwa sakamakon shigar wasu manyan ‘yan siyasa da kuma ƙoƙarin gina sabuwar haɗaka a matsayin mada...
Fri, 02 Jan 2026 - 906 - Yadda Ya Kamata Ku Gudanar Da Rayuwa A Shekarar 2026
Send us Fan Mail Shekarar 2026 ta zo a wani lokaci da ’yan Najeriya da dama ke fuskantar matsin tattalin arziki, da sauye-sauyen siyasa, da kuma ƙalubalen rayuwa da ke bukatar sabon tunani. Wannan ba lokaci ba ne na fatan samun sa’a kawai, lokaci ne na tsara hanya, da ɗaukar matakai, da yin gyara a rayuwar yau da kullum. A wannan shiri, za mu duba yadda ya kamata ’yan Najeriya su fara sabuwar shekara ta 2026 ta hanyoyi masu ma’ana—daga kula da yadda zasu sarrafa kuɗi da sana’a, zuwa kiwon laf...
Thu, 01 Jan 2026 - 905 - Siyasa Da Tsare-tsaren Gwamnati Da Suka Dabaibaye 2025
Send us Fan Mail Yayin da muke bankwana da shekarar 2025, siyasar Najeriya ta kasance cike da sauye-sauye, rikice-rikice, da kuma manyan al’amura da suka shafi iko, jam’iyyu da shugabanci. Shekarar ta shaida sauyin sheƙa na ‘yan siyasa, rikicin cikin gida a wasu jam’iyyu, da kuma fafutukar karɓar ragamar mulki a jihohi da matakin tarayya, lamarin da ya ƙara zafafa siyasar ƙasa. A bangaren tsare-tsaren gwamnati kuwa, 2025 ta kasance shekara mai ɗauke da tsauraran manufofi da suka shafi tattali...
Tue, 30 Dec 2025 - 904 - Waiwaye Kan Manyan Kalubalen Tsaro Da Suka Faru A 2025
Send us Fan Mail A shekarar 2025, Najeriya ta fuskanci manyan ƙalubalen tsaro da suka fi daukar hankali, musamman hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane, da ta’addanci a jihohin Arewa kamar Zamfara, da Katsina da Sokoto da Kaduna da kuma Borno. Hare-haren sun yi sanadin rasa rayuka, da rufe makarantu, da kaura daga gidaje, da kuma durkushewar harkokin tattalin arziki a wasu yankuna. Wadannan matsaloli suka sa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro, do...
Mon, 29 Dec 2025 - 903 - Yadda Kiristoci Ke Gudanar Da Bikin Kirsimeti A Cikin Musulmi
Send us Fan Mail A duk faɗin Arewacin Najeriya, ana gudanar da bukukuwan Kirsimeti cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna, duk da kasancewar Musulmai ne suka fi rinjaye a yawancin yankuna. Kiristoci kan yi bukukuwansu cikin mutunta al’adar Musulmai, yayin da Musulmai kuma ke nuna goyon baya ta hanyar gaisuwa, da tsaro, da mu’amala ta zamantakewa. A wurare da dama kamar Kaduna, Jos, Zaria, Minna da wasu sassan jihar Kano, ana ganin Kiristoci suna zuwa coci ba tare da tsangwama ba, yara...
Fri, 26 Dec 2025 - 902 - 'Halin Kunci Da Muke Ciki A Sansanin Gudun Hijira Yayin Bikin Kirsimeti'
Send us Fan Mail A yayin da al’ummar Kirista a sassa daban-daban na ƙasar nan ke gudanar da bukukuwan Kirsimeti cikin walwala, da annashuwa da haɗuwa da iyalai, akwai kuma waɗanda wannan lokaci ya zo musu cikin ƙunci da jimami. Waɗannan su ne mutanen da matsalolin tsaro—kamar hare-hare da rikice-rikice—suka tilasta musu barin gidajensu da muhallansu. A maimakon shagulgula a cikin gidajensu, suna gudanar da bikin ne a sansanonin gudun hijira, inda rayuwa ta cika da ƙalubale, da rashin ...
Thu, 25 Dec 2025 - 901 - Yadda Farashin Kayayyaki Suke Gabanin Bukukuwan Kirsimeti
Send us Fan Mail Gabannin bukukuwan Kirsimeti, kasuwanni a sassan ƙasar nan sun cika sun bunkasa. Jama’a na ci gaba da zirga-zirga domin sayen kayan bukukuwa, yayin da ‘yan kasuwa ke kokarin jawo hankalin masu saye ta hanyar daidaita farashi. A wannan shekarar, alamu sun nuna ba a samu hauhawar farashin kayayyaki a yawancin kasuwanni ba, sai dai wasu na kokawa da rashin kudaden saye. Ko yaya hakikanin farashin kayayyakin suke a wasu kasuwannin Nnajeriya? Wannan shine batun da ...
Wed, 24 Dec 2025 - 900 - Cushe-cushen Da Ake Zargin An Yi A Sabbin Dokokin Haraji
Send us Fan Mail Takaddama mai zafi ta dabaibaye sabbin dokokin haraji da Majalisar Tarayya ta amince da su, bayan zarge-zargen cewa an samu sauye-sauye a cikin dokokin bayan an kammala dukkan matakan amincewa da su a majalisa. Batun da ya taso ya jawo cece-kuce daga ‘yan majalisa, jam’iyyun adawa da kungiyoyin fararen hula, inda suke tambayar sahihancin abin da aka mika wa Fadar Shugaban Kasa domin aiwatarwa. Masu suka na cewa sauye-sauyen da ake zargin an yi ba tare da amincewar majalisa ...
Tue, 23 Dec 2025 - 899 - Irin Asarar Da Aka Tafka A Kasuwar Kafintoci Dake Kano
Send us Fan Mail Gobara a irin wannan yanayi na iska musamman a kasuwanni da gidaje ba sabon abu bane kuma ba abun mamaki ba. Wasu kafintoci dake aiki a kasuwar lale dake unguwar Tal’udu a karamar hukumar Gwale dake jihar Kano sun wayi gari da alhinin gobarar da ta yi sanadiyyar raba su da hanyar abincinsu. Wannan gobara da ba’a san musabbabinta ba ta janyo asarar miliyoyin Naira tare da jefa wadanda abun ya shafa cikin mawuyacin hali. Ko wanne irin hasara aka yi a wannan gobara? Wann...
Mon, 22 Dec 2025 - 898 - Darasin Da Za a Yi Koyi Dashi Cikin Takaddamar Dangote Da Farukh Ahmed
Send us Fan Mail Murabus din da Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Mai ta kasa Ahmed Farukh ya yi daga mukaminsa ya sa ‘yan Najeriya da dama na ta tofa albarkacin bakinsu musamman a bangaren harkokin mai. Murabus din na zuwa ne bayan doguwar takaddama tsakaninsa da Shugaban Rukunin Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote kan batutuwa da dama. Shin ko wanne darasi za a koya daga wannan takaddama da ta kai ga murabus din shugaban. Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai...
Fri, 19 Dec 2025 - 897 - Yadda Takunkumin Amurka Zai Shafi Tattalin Arzikin ‘Yan Najeriya
Send us Fan Mail Takunkumin da Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, ya sanya wa wasu ‘yan Najeriya ya sake jawo hankali kan irin tasirin manufofin ƙasashen waje ga rayuwar mutane da tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya. Wannan takunkumi, wanda ya haɗa da hana shiga Amurka, da toshe kadarori ko hana mu’amala da wasu hukumomi da kamfanonin Amurka, ba wai hukunci ne ga mutum ɗaya kaɗai ba, kazalika yana da tasiri mai zurfi ga harkokin kasuwanci, zuba jari da martabar ƙasa a idon duniya. Ko ta...
Thu, 18 Dec 2025 - 896 - Ce-ce Ku-ce Da Ya Dabaibaye Dauke Shalkwatar Bankin Masana’antu Zuwa Legas
Send us Fan Mail Batun matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na mayar da shalkwatar Bankin Masana’antu zuwa jihar Legas ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin ’yan Najeriya. Wannan mataki ya tayar da mabanbantan ra’ayoyi daga bangarori daban-daban na al’umma, inda wasu ke kallonsa a matsayin shawara mai ma’ana da za ta karfafa harkokin masana’antu da jawo jarin cikin gida da na kasashen waje. Sai dai a daya bangaren kuma, akwai masu sukar wannan mataki, inda suma suka bayyana irin tasu damuwa ...
Tue, 16 Dec 2025 - 895 - Yadda Matsalar Tsaro Ke Hana Mu Tafiye-tafiyen Kirsimeti
Send us Fan Mail A ’yan shekarun nan, lokaci na bukukuwan ƙarshen shekara—wanda a da ake ɗauka a matsayin lokacin farin ciki, da haɗuwa da iyalai, da tafiye-tafiye—ya fara sauya salo ga mutane da dama. Maimakon shirye-shiryen ziyartar ’yan uwa ko halartar bukukuwa a garuruwa daban-daban, mutane da yawa yanzu suna cike da fargaba da damuwa. Babban dalilin hakan shi ne ƙalubalen tsaro da ke ƙara tsananta a sassa daban-daban. Rahotanni na hare-haren ’yan bindiga, da sace-sace a kan manyan hany...
Mon, 15 Dec 2025 - 894 - Alfanu Da Kalubalen Sabon Jadawalin Karatun Makarantu Da Gwamnati Ta Bijiro Dashi
Send us Fan Mail A kwanakin baya, Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da sabon tsarin jadawalin karatu ga makarantun firamare da sakandare. Sabon tsarin, wanda Ma’aikatar Ilimi ta ƙasa ta tsara, yana da nufin inganta koyarwa da koyo, da rage nauyin lodi ga dalibai, da kuma tabbatar da cewa malamai suna da isasshen lokaci don isar da darussa tare da kwarewa. Tsarin ya mayar da hankali kan daidaita ranakun makaranta, da tsara lokutan darussa bisa bukatun shekaru da matakin karatu, da kuma kara aiki ...
Thu, 11 Dec 2025 - 893 - Yadda Abincin Da Mutane Ke Ci Ke Zamewa Guba
Send us Fan Mail A yau al’ummar mu na fuskantar barazana ta wata siga da ba kasafai ake gane ta ba, wato guba da ke shiga jikin ɗan Adam ta hanyar abinci irin su nama, kifi, madara da sauran kayayyakin da muke ci a kullum. Sau da yawa dabbobi ko kifaye suna cin wasu tsirrai, ganye, ko ababen da ke dauke da sinadarai masu haɗari, waɗanda daga baya suke taruwa a jikinsu har su zama guba ga mutum idan aka ci su. Wasu lokuta ma waɗannan gubobi ba daga abincin dabbar suke fitowa ba, sai dai daga...
Tue, 09 Dec 2025 - 892 - Kudaden Da Samar Da ‘Yansandan Jihohi Zai Lashe
Send us Fan Mail Batun samar da ‘yansandan jihohi na ƙara ɗaukar hankalin ‘yan Najeriya, musamman a dai-dai lokacin da matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a sassa daban-daban na ƙasar nan. Sai dai, samar da ‘yansandan jihohi ba abu ne mai sauƙi Kamar yadda wasu ke tunani ba. Gwamnatocin jihohi na buƙatar abubuwa masu yawa kafin su iya ɗaukar wannan nauyi, banda batun samar da dokar samar da wadannan ‘yansanda, akwai batun samar da kayan aiki da horo da sauran abubuwa da ake bukata don gud...
Mon, 08 Dec 2025 - 891 - Abun Da Masu Ruwa Da Tsaki Ke Yi Na Dakile Laifuka A Wurin Matasa
Send us Fan Mail Masu iya magana kan ce banza ba ta kai zomo kasuwa. In ba haka ba, me ya kai matasan da ake zargi da aikata manyan laifuffuka ofishin ’yan sanda, suka kuma fit oba tare da wani ya harae su ko ya yi mutsu tsawa ba, balle ya saka su a cell? ’Yan sandan dai sun ce wannan wata dabara ce ta yakar aikata manyan laifuka irin su sata da fashi da makami da kwacen waya da fyade kai har ma da satar mutane don kudin fansa a tsakanin matasa. Ko yaya wannan dabara take aiki? Wannan...
Thu, 04 Dec 2025 - 890 - Matsalar Kansar Mama Da Hanyoyin Magance Ta
Send us Fan Mail Cutar kansar mama na ɗaya daga cikin manyan cututtukan da ke addabar mata a Najeriya da ma duniya baki ɗaya. An kiyasta cewa mata sama da dubu ɗari biyu na kamuwa da cutar a kowace shekara a Najeriya, yayin da miliyoyin mata a duniya ke fama da wannan cuta. Abin damuwa shi ne cewa yawancin lokuta ana gano cutar ne a kurarren lokaci, wanda hakan ke sa magani ya yi wahala kuma ya rage yiwuwar ceto rayuwar wanda ya kamu da shi. Wannan shine batun da shirin Najeriya A Y...
Tue, 02 Dec 2025 - 889 - Halayen Da Ya Kamata Mutum Ya Mallaka Kafin A Nada Shi Jakada
Send us Fan Mail A mafi yawan ƙasashen duniya, ana ɗaukar jakadu a matsayin fuskar ƙasa kuma ginshiƙan hulɗar diflomasiyya. Saboda haka, akwai muhimman halaye da suke tilas jakadan ƙwarai ya mallaka domin ya wakilci ƙasarsa cikin mutunci, da nagarta da kwarewa. Tun bayan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fitar da sunayen jakadu da yake sa ran majalisar kasa ta tantance ne dai batun ke ta shan suka daga manazarta kan sunayen da ya fitar. Ko wadanne irin halaye ya kamata jakada ya...
Mon, 01 Dec 2025 - 888 - Waiwaye Kan Irin Gudunmawar Da Sheikh Dahiru Bauci Ya Bayar Ga Cigaban Addini
Send us Fan Mail Sheikh Dahiru Usman Bauchi, fitaccen malamin addinin Musulunci, masanin tafsiri, kuma jagoran darikar Tijjaniyya, shahararre ne saboda iliminsa mai zurfi da tasirin da ya yi a fagen addini da tarbiyya a Najeriya da ma ƙasashen Yammacin Afirka. Sheikh Dahiru Bauci ya shafe sama da shekaru saba’in yana koyar da ilimi, ya gudanar da tarukan tafsiri a duk shekara, ya gina makarantu, ya kafa cibiyoyi, kuma ya ba da ilimi ga dubban almajirai hanyoyin da suka taimaka wajen yaɗ...
Fri, 28 Nov 2025 - 887 - Amafani Da Karfin Soji Ko Tattaunawa Ne Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya?
Send us Fan Mail A cikin shekarun nan, matsalolin tsaro a Najeriya kamar ta’addanci, da garkuwa da mutane, da rikicin manoma da makiyaya, da kuma ayyukan ’yan bindiga suna kara ta’azzara, lamarin da ya sanya al’umma da masana tsaro ke tambayar wace hanya ta fi dacewa gwamatani ta yi amfani da shi wajen kawo karshen wadannan matsaloli da suka ki ci suka ki cinyewa tsawon shekaru. Yayin da wasu ke ganin amfani da karfin soji ne kadai hanyar da zai kawo karshen wannan matsala, wasu na ganin ta...
Thu, 27 Nov 2025 - 886 - Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta
Send us Fan Mail Cutar amosanin jini wacce aka fi sani da cutar sikila na cigaba da barazana ga rayukan masu dauke da ita. Wannan cuta na saka masu ita da ‘yan uwan su cikin halin ha’ula’i, a wasu lokutan ma tana haifar da rasa rayukan wasu dake dauke da ita. Rahotannin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun nuna cewa, kusan yara 300,000 ne ake haifa da cutar Sikila a duk shekara a fadin duniya, inda yankin Kudu da Sahara a Afirka ke dauke da kashi 75% na wannan yawan. A ...
Tue, 25 Nov 2025 - 885 - Halin Da Shirin Samar Da Tsaro A Makarantun Najeriya Ke Ciki
Send us Fan Mail A shekarar 2014, bayan tashin hankalin da ya biyo bayan sace ɗaliban Chibok da kuma yawaitar hare-hare kan makarantun yankin Arewa maso Gabas, gwamnatin tarayya tare da haɗin gwiwar ƙasashen duniya ta ƙaddamar da wani muhimmin shiri mai suna Safe School Initiative. Manufar wannan shiri ita ce tabbatar da cewa dalibai suna iya zuwa makaranta cikin tsaro ba tare da fargabar hare-hare daga ‘yan ta’adda ko ‘yan bindiga ba. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi n...
Mon, 24 Nov 2025 - 884 - Ba A Yi Ma Nnamdi Kanu Adalci Ba- Emmanuel Kanu
Send us Fan Mail Hukuncin da kotun tarayya ta Abuja ta yanke wa shugaban haramtacciyar ƙungiyar IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, ya sake tayar da kura a tsakanin magoya bayansa, ‘yan yankin Kudu maso Gabas, da al’ummar Najeriya gaba ɗaya. Yayin da gwamnati ke cewa hukuncin ya biyo bayan dogon shari’a da hujjoji da suka tabbatar da aikata laifukan da ake tuhumarsa da su, wasu na ganin batun na da matuƙar sarkakiya musamman ma yadda iyalansa da magoya bayansa ke kallon wannan hukunci. Shin ko ...
Fri, 21 Nov 2025 - 883 - Halin Kunci Da Matan Da Aka Yi Garkuwa Da Su Ke Tsintar Kansu A Ciki
Send us Fan Mail Mata da dama da aka yi garkuwa da su na shiga wani irin mawuyacin hali yayin da suke hannun wadanda suka sace su, suna fuskantar rayuwar kaskanci, da cin zarafi, da muzgunawa da wasu irin yanayi wanda sai ka tausaya musu. Irin wadannan mata a wasu lokutan basa tsira da rayukansu, a wasu lokutan kuma ko sun tsira, sukan shiga halin ciwon damuwa wanda ke daidaita musu rayuwa, a wasu lokutan ma har sai sun ji kamar su dauki rayuwar su. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci za...
Thu, 20 Nov 2025 - 882 - Matsayar Doka Kan Taron Da Jam'iyyar PDP Ta Gudanar
Send us Fan Mail Matsayar doka ta zama babbar abun tattaunawa a Najeriya yayin da jam’iyyar PDP ta gudanar da taron ta na kasa duk da mabanbantan hukunce hukunce daga kotuna biyu. Umarnin kotu guda yana goyon bayan taron, ɗayan kuwa ya haramta shi gaba ɗaya. Wadannan hukunce hukunce ba baiwa jam’iyyar damar yi ko haramta musu taron kadai suka yi ba, harda baiwa hukumar zabe ta kasa umurnin saka ido ko haramta musu wannan dama yayin taron. Duk da wadannan hukunce hukunce, jam’iyyar ta gudana...
Mon, 17 Nov 2025 - 881 - Dalilan Da Ke Hana Manoman Najeriya Noman Rani
Send us Fan Mail A duk shekara bayan girbin damina, ana sa ran manoma su ci gaba da noma a lokacin rani domin tabbatar da wadatar abinci da bunkasar tattalin arziki. Sai dai hakan na fuskantar kalubale da dama da ke hana yawancin manoma shiga noman rani. Kamar yadda masana suka sha bayyanawa, akwai dalilai da dama dake hana manoma shiga noman rani a duk lokacin da aka ce damina ta tattara inata intat. Shin ko wadanne kalubale ne ke hana manoma shiga noman rani bayan damuna ta wuce? Wannan...
Fri, 14 Nov 2025 - 880 - Yadda Raguwar Maniyyatan Najeriya Ke Tasiri Ga Aikin Hajji A Najeriya
Send us Fan Mail A kwanakin nan ana samun raguwar kujerun maniyyata aikin Hajji daga Najeriya, abin da ya jawo fargaba ga masu shirin zuwa kasa mai tsarki da kuma masu hidimar su. A da, Najeriya na samun kujeru sama da dubu casa’in daga gwamnatin Saudiyya, amma cikin shekaru kadan da suka gabata adadin ya ragu zuwa kusan dubu sittin da biyar. Kazalika a yanzu gwamnatin na saudiyya ta bayyana cewa idan har maniyyatan Najeriya basu biya cikakken kudaden hajjin bana ba kafin wa'adi...
Thu, 13 Nov 2025 - 879 - Dalilan Malaman Jami’oi Masu Zaman Kansu Na Shiga Kungiyar ASUU
Send us Fan Mail A yayin da tattaunawa kan makomar ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ke ci gaba da ɗaukar hankali, batun yadda za a haɗa jami’o’i masu zaman kansu cikin tsarin ƙungiyar ya sake tasowa. Wasu na ganin wannan sabon yunƙuri zai iya zama sabuwar hanyar ƙarfafa hadin kai tsakanin malamai, yayin da wasu ke gargadin cewa hakan na iya kawo tsaiko ga karatun wasu dalibai dake kauracewa jami’oin gwamnati sakamakon yawan yajin aiki da suke tsunduma lokaci zuwa lokaci. ...
Tue, 11 Nov 2025 - 878 - Dalilan Yaduwar Cutuka A Irin Wannan Lokaci
Send us Fan Mail Da zarar damuna ta fara bankawana, yanayi na sanyi da zafi kan fara sallama, wanda hakan kan zo da rashin lafiya dake yaduwa a cikin alumma. Ko wadanne dalilai ne suka sa ake samun yaduwar rashin lafiya a wannan lokaci? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Tue, 02 Jun 2026 - 877 - Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Cutar Basir
Send us Fan Mail Cutar basir na daga cikin cututtukan da mutane da dama ke da mabanbantan ra’ayoyi akan ta. A lokuta da dama za ka ji yadda mutane ke fadin dalilai daban daban da ke janyo cutar basir, yayin da wasu ke ganin yawan zama ne ke kawo ta, wasu kuwa gani suke yi zaki da maiko ne ke kawo ta. Wannan shine abun da da yawa daga cikin mutane suka sani kan wannan cuta, sai dai masana kiwon lafiya na da nasu fahimtar daban kan wannan cuta. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai t...
Thu, 06 Nov 2025 - 876 - Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Su A Najeriya
Send us Fan Mail Rashin aikin yi na daya daga cikin manyan kalubalen da najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman la’akari da yanda ake cigaba da samun matasa dake da karfi a jika amma babu aikin yi. Hukumar kididdiga ta kasa ta fitar da bayanan dake baiyana cewa rashin aikin yi ya karu a najeriya da kaso 5.3 a farkon wannan shekarar, kazalika binciken ya baiyana cewa wadanda basu yi karatu mai zurfi ba sun fi wadanda suka yi karatu mai zurfi samun aikin yi. &nb...
Tue, 04 Nov 2025 - 875 - Ko Kawo Dakarun Kasar Amurka Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya?
Send us Fan Mail Ana ta ce-ce- ku-ce kan batun da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na kawo dakarun kasar sa Najeriya don taimakawa wajen yaki da matslar tsaro. Yayin da wasu ke ganin hakan abun san barka ne, wasu kuwa tofin Ala tsine suka yi ga wannan batu. Shin ko me zai faru idan aka kawo dakarun kasar Amurka Najeriya don shawo matsalar tsaro? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Mon, 03 Nov 2025 - 874 - Dalilan Da Daliban Makarantar Kudi Suka Fi Na Gwamnati Kokari
Send us Fan Mail Duk da cewa gwamnati na da dubban kwararrun malamai a makarantunta, har yanzu ana ganin ɗaliban makarantun gwamnati na kasa da na makarantun masu zaman kansu wajen ƙoƙari da kuma sakamakon jarabawa. Wannan matsala ta daɗe tana jawo muhawara tsakanin iyaye, malamai da hukumomin ilimi. Wasu na ganin matsaloli ne da ba za su rasa nasaba da rashin kulawa da watsi da harkar ilimi da gwamnati ta yi ba. Ko wadanne dalilai ne suka daliban makarantun masu zaman kansu suka fi kok...
Thu, 18 Jun 2026 - 873 - Shin Ko Sauya Hafsoshin Tsaro Zai Kawo Karshen Aikin Ta’dda A Najeriya?
Send us Fan Mail Tun bayan sauya hafsoshin tsaro da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ne dai mutane da dama keta tofa albarkacin bakinsu, yayin da wasu ke ganin hakan zai taimaka wajen yaki da rashin tsaro, wasu kuwa na ganin duk jama’ar ja ce. Shin ko sauya hafsoshin tsaro zai kawo karshen fargaban da al’umma ke yi? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari akai.
Mon, 27 Oct 2025 - 872 - Me Dawowar Hare-hare Kan Sojoji Ke Nufi A Arewa Maso Gabas?
Send us Fan Mail A cikin ‘yan watannin da suka gabata, an sake ganin karuwar hare-haren Boko Haram da ISWAP musamman a yankin Arewa maso Gabas. Kazalika, ko a kwanan nan ma anga irin wadannan hare hare. Wadannan hare-haren sun fi karkata kan sansanonin sojoji, inda ake samun asarar rayuka da dama, da kuma lalata kayan aikin gwamnati. Rahotanni daga Borno da Yobe da ma wasu sassan kasar nan sun nuna yadda ‘yan ta’adda suka sake samun karfi wajen kai hare-hare cikin dare, tare da amfani da da...
Fri, 24 Oct 2025 - 871 - Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Haraji Da Zai Fara Aiki A 2026
Send us Fan Mail A ranar 26 ga watan Yuni, shekara ta 2025, gwamnatin tarayya ta sanya hannu kan sabon tsarin haraji wanda za a fara aiwatarwa daga ranar 1 ga Janairu, 2026. Wannan sabon tsarin haraji na daga cikin matakan da gwamnati ke cewa zai taimaka wajen kara samun kudaden shiga da kuma rage dogaro da albarkatun mai. Sai dai, jama’a da dama ba su da cikakken bayani game da irin wadannan sabbin haraji ko menene suke nufi ba. Shin ko ta wadanne hanyoyi ne wannan sabon haraji&nbs...
Thu, 23 Oct 2025 - 870 - Halin Da Muka Shiga Sakamakon Haihuwar ‘Ya Mai Cutar Motsewar Kwakwalwa
Send us Fan Mail Cutar Cerebral Palsy, wadda ake kira Ciwon tsukewar kwakwalwa, na daga cikin manyan matsalolin lafiyar yara da ke tasowa tun daga haihuwa. Wannan cuta tana faruwa ne sakamakon rauni ko lalacewar wani ɓangare na kwakwalwa da ke kula da motsi, magana, da daidaiton jiki. A mafi yawan lokuta, cutar tana bayyana ne tun daga ƙuruciya, a wasu lokutan kuma kamar yadda masana kiwon lafiya suka bayyana, cutar na faruwa ne tun kafin a haifi yaro. Ko ta wadanne irin hanyoyi wannan cu...
Tue, 21 Oct 2025 - 869 - Shin Ya Kamata A Saki Shugaban IPOB Nnamdi Kanu?
Send us Fan Mail Tun bayan fara shari’ar Nnamdi Kanu a shekarar 2021 mutane da dama suke bayyana ra’ayoyinsu a kan sake shi ko a kyale shari’a ta yi halinta. Hasali ma har zanga-zanga wasu ‘yan Najeriya suka kira don bayyana bukatar sakin shugaban na ‘yan aware. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan ko ya dace a saki Nnamdi Kanu?
Mon, 20 Oct 2025 - 868 - Yadda Cire Darasin Lissafi Zai Taimakawa Dalibai Shiga Jami’a
Send us Fan Mail Cire darasin Lissafi daga jerin wajibcin da ake buƙata domin samun shiga manyan makarantu ya samu karɓuwa daga wasu ɓangarori na dalibai da malamai. Wasu dalibai sun nuna farin ciki da wannan mataki, suna ganin zai sauƙaƙa musu damar samun shiga jami’a da sauran manyan makarantu ba tare da shan wahalar lissafi ba. Sai dai wasu masana sun bayyana cewa, duk da wannan sauƙin, ya kamata a yi taka-tsantsan saboda lissafi na taka muhimmiyar rawa wajen gina tunani da fahimtar ilim...
Thu, 16 Oct 2025 - 867 - Shin Babu Wata Hanyar Magance Matsalolin ASUU Ne Sai Ta Yajin Aiki?
Send us Fan Mail Shekara da shekaru kungiyar malaman jami’oi ASUU ta kwashe ta na gudanar da yajin aiki ba tare da samun biyan bukata ba. Irin wannan yajin aiki da kungiyar malaman ke shiga ya jefa dalibai da malaman da ma harkar ilimi cikin halin ni ‘yasu a Najeriya. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wasu hanyoyin da kungiyar malaman ASUU za ta iya bi don warware matsalar ta ba tare da dogaro da gwamnatin tarayya ba.
Tue, 14 Oct 2025 - 866 - Kalubalen Da Ke Gaban Sabon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa
Send us Fan Mail A duk lokacin da a ka samu canjin shugabanci, hakan kan zo da kalubale da dama. Muƙamin shugabancin Hukumar Zabe ta kasa na daga cikin mukamai a Najeriya da 'yan kasa ke cece-kuce a kai. Ko wadanne irin Kalubale ne ke gaban sabon shugaban hukumar zabe ta kasa? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari akai.
Fri, 10 Oct 2025 - 865 - Abin Da Dokar Kasa Ta Ce Kan Nada Shugaban Hukumar Zabe
Send us Fan Mail A tsarin mulkin Najeriya, an bai wa Shugaban Ƙasa ikon naɗa shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) tare da sauran mambobinta. Wannan iko yana daga cikin muhimman nauyukan da ke hannun shugaban ƙasa domin tabbatar da cewa ana gudanar da zaɓe cikin tsari, gaskiya da adalci. Sai dai, kafin wanda shugaban ƙasa ya naɗa ya fara aiki, dole ne a nemi amincewar Majalisar Dattawa, domin tabbatar da cewa wanda aka zaɓa ya cancanci rike wannan muhimmiyar kujera. Wannan ts...
Thu, 09 Oct 2025 - 864 - Tasirin Takardun Shaida Na Bogi Ga Rayuwar Al’umma
Send us Fan Mail Takardun shaida na bogi na daya daga cikin matsaloli dake kara addabar Najeriya a fannoni da dama. A wasu lokuta ana samun mutane da ke amfani da takardun makaranta ko na ƙwarewa da ba su cancanta da su ba domin samun aiki, mukami, ko wasu fa’idodi da suka wajaba ne kawai ga waɗanda suka cancanta. Wannan dabi’a ta zama barazana ga ci gaban ƙasa da amincin al’umma gaba ɗaya, domin tana lalata tsarin ilimi, rage darajar masu gaskiya, da haifar da rashin inganci a wuraren aiki...
Tue, 07 Oct 2025 - 863 - ‘Halin Kunci Ya Sa Muke Zama A Baca A Abuja’
Send us Fan Mail Halin matsin tattalin arziki ya tilasta da yawa daga cikin mutane zama a bacoci a garin Abuja da wasu biranen Najeriya. Mutane a birane kamar Abuja da Legas Da Fatakwal na cikin halin matsi sakamakon rashin ingattaccen muhalli. Ko wannen irin rayuwa irin wadannan mutanen ke yi? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai a yau da ake bikin ranar muhalli ta duniya.
Mon, 06 Oct 2025 - 862 - Yadda Fasahar AI Ke Barazana Ga Sana’ar Masu Shagunan Daukar Hoto
Send us Fan Mail A zamanin yau na fasahar zamani, musamman fasahar kirkirarriyar basir ta (AI), harkokin sana’o’i da dama suna fuskantar sauye-sauye masu girma. Daya daga cikin sana’o’in da ke cikin babban hadari shi ne sana’ar ɗaukar hoto musamman irin wadanda ke kashe makudan kudi wajen sayen kyamara da bude katafaren gidajen daukar hoto. A da, mutane kan je shagon daukar hoto domin samun hoto mai kyau na fasfo ko na bikin aure ko bikin suna, ko kuma kowane irin taron biki. Amma yanzu, ma...
Fri, 03 Oct 2025 - 861 - Abin Da Dokar Kasa Ta Ce Kan Takarar Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan
Send us Fan Mail Batun siyasar Najeriya ya sake ɗaukar hankali yayin da jam’iyyar PDP ta bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, zai tsaya mata takarar shugaban ƙasa a 2027. Wannan batu ya tayar da muhawara mai zafi a tsakanin masana, da ‘yan siyasa da ma al’umma. Idan za a iya tunawa dai, an rantsar da tsohon shugaban ƙasan, har sau biyu: a karo na farko a shekarar 2010 bayan rasuwar tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua, sannan kuma a karo na biyu a 2011 bayan ...
Fri, 22 May 2026 - 860 - Me Ya Sa Mutane Suka Dawo Daga Rakiyar Kirifto?
Send us Fan Mail A ’yan watanni da suka gabata, matasa da yawa a Najeriya sun dukufa don ganin hakar su ta cimma ruwa wajen samun kudaden kirifto. Amma alamu na cewa a baya-bayan nan wasu daga cikinsu sun sare sun kuma saduda sun dawo daga rakiyar harkar. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan dalilan wasu matasan na yin watsi da harkar kirifto.
Tue, 23 Jun 2026 - 859 - Hanyoyin Da Dangote, PENGASSAN Ba Su Bi Ba Don Magance Takaddamarsu
Send us Fan Mail Gwamnatin Tarayya ta gayyaci Kungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya (PENGASSAN) da Matatar Dangote don a sasanta a yau. Hakan ya biyo bayan umarnin da ’yan kwadagon suka bai wa mambobinsu ne na shiga yajin aiki bayan da Matatar Dangote ta salami ma’aikata fiye da 800. Sai dai wasu masana suna ganin tun farko bai kamata lamarin ya kai ga haka ba da an bi wasu hanyoyi. Wadannan hanyoyi shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai binciko.
Mon, 29 Sep 2025
Podcasts similares a Najeriya a Yau
Al-Quran Al-kareem Al-Quran Al-kareem
dakwah.me - Ustadz Adi Hidayat dakwahme
KH ANWAR ZAHID OFFICIAL Dakwah NU
Bagong Ndagel Dhiyon Daimonos
Ngaji Bareng Gus Baha Gus Baha
Kumpulan Ceramah Agama Islam IWAN
K.H. ZAINUDDIN MZ K.H. ZAINUDDIN MZ
Ludruk Cak Kartolo dkk Ludrukan
Bodor Sunda Mang Udin
Seni Sunda Wayang Golek Mohamad Rohmat
Murottal Qur'an Terjemahan Audio Indonesia Muslim
Trio Burulu Nusendra Hanggarawan
Pengajian KH Anwar Zahid Pengajian KH Anwar Zahid
Kumpulan Dakwah Sunnah PodcastSunnah
Wayang Kulit Indonesia Raden Ontoseno
Radio Rodja 756 AM Radio Rodja 756AM
Murotal Metode Ummi Rumah Digital Education (sutego)
Wayang golek SI CEPOT
Sinau Bareng Cak Nun Telat Cerdas
Ustad Das'ad Latif Ustad Das'ad Latif
Al Quran dan Terjemahan wahyu hanan
Ludruk Jawa Timur Yohan Arie Chandra
Kajian Islami Bersama Ustad Abdul Somad Yuda Prawira
Quran Indonesian القرآن الكريم