Filtrer par genre

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau

Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

574 - ‘An Yafe Wa Masu PoS Biyan Harajin Yin Rijista Da CAC’
0:00 / 0:00
1x
  • 574 - ‘An Yafe Wa Masu PoS Biyan Harajin Yin Rijista Da CAC’

    Ga alama nan ba da dadewa ba yanayin sana’ar POS a kasar nan zai sauya. 

    Babban Bankin Najeriya (CBN) ya wajabta wa masu wannan sana’a yin rajista da Hukumar Rajistar Kamfanoni da Kungiyoyi (CAC) zuwa nan da 7 ga watan Yulin 2024.

    To amma ya batun harajin da suke korafi a kai? Ku biyo mu a Shirin Najeriya a Yau don jin matsayar CAC game da biyan kudin.

    Fri, 10 May 2024
  • 573 - 'Za Mu Ɗaure Duk Wanda Bai Yi Gwajin Jini Kafin Aure Ba'

    Sabuwar dokar da gwamnatin jihar Kano ta sanyawa hannu kan yin gwajin lafiya kafin aure na shan yabo da suka.

    A cewar gwamnatin, yawaitar yaduwar cututuka a tsakanin ma’aurata bayan aure shi ne makasudin yin wannan doka. Amma me ya sa za a daure wanda ya taka dokar tsawon shekara 5 ko tarar 500,000? Idan aka samu wanda ya taka dokar miji za a daure ko mata ko madaurin auren?

    Shirin Najeriya a Yau ya zanta da masu ruwa da tsaki da masana shari’a kan wannan doka.

    Thu, 09 May 2024
  • 572 - Abun Da Za A Fara Lura Kafin Shiga Tasi A Abuja

    Yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa ne ya sa kowa ya koma neman kudi da mota don daukar fasinjan a Abuja.

    Sai dai hukumomi sun ce an dauki matakin hana duk wani mutum da bai cika ka'idojin yin tasi ba.

    Shirin Najeriya a Yau ya duba dalilan da suka sa hukumomi ke shirin tabbatar da halascin yin kabu-kabun ga masu zaman kansu ba tare da sun yi fentin ba.



    Tue, 07 May 2024
  • 571 - Ɓarkewar Cutar Ƙyanda: Sakaci Ko Annoba?

    A karshen shekarar 2023 ne dai, hukumar Lafiya ta Duniya WHO da Cibiyar hana yaduwar cututtuka suka yi gargadi cewa cutar kyanda na ci gaba da zama barazana ga yara a Najeriya.

    Sai ga shi kwatsam an samu rahotanni game da barkewar cutar a wasu yankunan Naijeriya har ta kashe wasu mutane da dama.

    Shirin Najeriya a Yau ya mayar da hankali ne kan cutar ta kyanda, da yadda za ku kare yaranku daga annobar.

    Mon, 06 May 2024
  • 570 - Dalilan Da Ake Yi Wa Mutum Kutse A Soshiyal Midiya

    Masu amfani da shafukan sada zumunta kan fada hannun masu dandantsa inda sukan yi kutse a shafin mutum har ya rasa iko da shi.

    Kwararru sun ce ana yi wa wasu hakan domin bata suna ko kuma neman kudi da damfara.

    Shirin Najeriya a Yau ya tattauna da kwararru a fannin samar da matakan tsaro a soshiyal midiya game da dabarun inganta tsaron shafukanku.

    Fri, 03 May 2024
Afficher plus d'épisodes