Podcasts by Category
Najeriya a Yau
- 570 - Dalilan Da Ake Yi Wa Mutum Kutse A Soshiyal Midiya
Masu amfani da shafukan sada zumunta kan fada hannun masu dandantsa inda sukan yi kutse a shafin mutum har ya rasa iko da shi.
Kwararru sun ce ana yi wa wasu hakan domin bata suna ko kuma neman kudi da damfara.
Shirin Najeriya a Yau ya tattauna da kwararru a fannin samar da matakan tsaro a soshiyal midiya game da dabarun inganta tsaron shafukanku.Fri, 03 May 2024 - 569 - “Tabbas Muna Biyan Ma’aikatan Borno Albashin N7,000, Amma...”
Shafukan sada zumunta na ta girgiza bayan da wani labari ya bayyana game da yanayin walwalar ma’aikata da albashinsu a jihar Borno.
Ma’aikata da dama sun yi ta yada hoton albashinsu na N7,000; wasu N8,000 ko N13,000 ko N15,000 ga ma’aikatan lafiya.
Shirin Najeriya a Yau ya gano gaskiyar abin da ya sa gwamnatin jihar Borno ke biyan irin wannan albashi da wasu suka ce bai taka kara ya karya ba.Thu, 02 May 2024 - 568 - Yadda Wahalar Fetur Ke Jigata ’Yan Najeriya
Karancin man fetur na neman tsayar da al'amura cak ga al'umma a wasu sassan Najeriya. Da dama sun ce lamarin ya shafe su kaitsaye kuma sakamakon haka suna dandana kudarsu.
Shin yaushe wannan lamari zai zo karshe, musamman idan yi la’akari da cewa tun a Kamafanin Mai Na Kasa (NNPC) ya ce ya maganace matsalar?
A shirin Najeriya a Yau mun tattauna da wadanda abin ya shafa sannan mu ji ta bakin masu ruwa da tsaki kan yiwuwar samun mafita nan kusa.Tue, 30 Apr 2024 - 567 - Abin Da Ya Sa Gwamnonin Arewa Suka Je Amurka Taron Tsaro
Gwamnonin Arewacin Najeriya da ake fuskantar kalubalen tsaro na kokarin lalubo ko ta wace hanya a samu dabarar dakile matsalar.
Tafiyar gwamnoni 9 daga arewacin Najeriya zuwa Amurka a kwanan nan domin halartar taron tsaro ya nuna yadda suke kokarin daidaita lamarin har a matakin kasashen ketare.
Saidai lamarin na zuwa ne a lokacin da wasu ke ganin an yi makamancinsa a Najeriya ba tare da halartar wani gwamna daga jihohin da suke fama da matsalar tsaron ba.
Shirin Najeriya a Yau ya duba tasirin da taron zai yi wajen magance matsalar yankunan.Mon, 29 Apr 2024 - 566 - Dalilin Da Fasfo Ya Zama Wajibi Ga Ɗanƙasa Ko Ba Don Tafiya Ba
Shin ka taba tunanin damammakin da za ka iya rasawa saboda rashin mallakar fasfon dan kasa a Najeriya?
Yawancin mutane basu maida hankali wajen mallakar fasfo domin a tunaninsu sai idan kana kokarin ketare kasa ya zama wajibi a gare ka, amma kuma akwai damammaki da za ka iya rasawa saboda rashin mallamar shi.
To ku biyo mu cikin Shirin Najeriya a Yau domin jin irin amfanin da mallakar fasfo zai iya muku da kuma damarmakin da za ku iyya rasawa.Fri, 26 Apr 2024 - 565 - Da Gaske Haƙa Rijiyoyin Burtsatse Na Haifar Da Matsala A Anguwanni?
Ana cikin matsanancin karancin ruwa a yankuna daban-daban a Najeriya.
Lamarin ya sa a 'yan shekarun mutane ke ta kokarin samar da rijiyoyin burtsatse wato 'Borehole' a turance. Sai dai a cewar masana yawanci yanzu rijiyyoyi na kafewa da kuma haifar da zaizayar kasa.
Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda ko haƙa bohol-bohol zai iya haifar da matsala ga muhalli da kuma al'umma a anguwanni?Thu, 25 Apr 2024 - 564 - Me Ya Sa Ake Ɓoye Wa Mata Wasu Abubuwa Idan Za Su Yi Aure?
Akwai abubuwan da ya kamata a rika bayyana wa mata idan za su yi aure amma kunya tana hanawa.
Wasu sai sun je gidan aure suke tarar da abubuwan da ya kamata ace sun sani daga magabata, amma sai dai su tsinta a wajen kawayensu.
Shirin Daga Laraba ya duba dalilan da ya sa ake kin bayyanawa mata wasu mahimman abubuwan da ya kamata su sani idan za su yi aure.Wed, 24 Apr 2024 - 563 - Yadda Tsananin Zafi Zai Iya Cutar Da Dalibai A Makarantu
Hukumomi sun bayyana jihohin da za a samu matsanancin zafi a Najeriya.
Lamarin ya zo daidai lokacin da makarantu ke komawa hutu, inda ake fargabar yiwuwar yaduwar cututtuka a azuzuwa masu cunkuso.
Shin ta wace hanya makarantu za su kauce wa yaduwar cututtuka masu alaka da matsanancin zafi? Shirin Najeriya a Yau na da karin bayaniTue, 23 Apr 2024 - 562 - Rawar Da NNPP Ke Takawa A Dambarwar Dakatar Da Ganduje
Dambarwa ta siyasa ci gaba da daukar hankali game da dakatar da shugaban jam’iyar APC na kasa
Ana ta takaddama da zargin juna tsakanin jam’iyyun siyasa musamman na Kano da gwamnati mai ci a can.
Toh amma wa ke wasa da hankalin wani ko rura wutar rikicin dakatar da Ganduje a jam’iyar APC, Shirin Najeriya a Yau na da karin bayani a kai.Mon, 22 Apr 2024 - 561 - Dalilin Da Kotuna Ke Yanke Hukunci Mabambanta Kan Shari’a Iri ƊayaFri, 19 Apr 2024
- 560 - Me Ya Sa ‘Yan Kasuwa Suka Ƙi Karya Farashi Duk Da Karyewar Dala?Thu, 18 Apr 2024
- 559 - Wa Ke Da Ikon Dakatar Da Ganduje A Jam’iyar APC?
An shiga saƙe-saƙe game da mutanen da suka yi ikirarin dakatar da Ganduje daga jam’iyar APC tun daga matakin mazaba.
Sai dai uwar jam’iyar ta yi watsi da hakan, inda kuma daga bisani suka zargi jami’iyar adawa.
To amma ko da ace za a dauki irin wannan matakin, wa ke da hurumin dakatar da shugaban jamiyar APC na kasa a dokance? Shirin Najeriya a Yau na da karin bayani.Tue, 16 Apr 2024 - 558 - Albashin Da Ya Kamata A Riƙa Biyan Ma’aikaci A Wannan Yanayi
Yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa ya sa komai ya sauya amma banda albashin ma’aikata.
Akwai mahimman abubuwan da masu daukar albashi ba su iya yi saboda ma’aikatu da hukumomi sun kasa matsawa da albashinsu gaba.
Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan abin da ya kamata mutum ya fara dubawa ta fannin albashi kafin karbar aiki.Mon, 15 Apr 2024 - 557 - Shin Ya Dace Mace Ta Fara Sitta-Shawwal Kafin Biyan Bashin Ramadan?
Wane lokaci ya fi dacewa mutum ya fara azumin sitta-shawwal?
Ana yawan shiga rudani kan hakan, da kuma tunanin cewa mace wadda ake binta bashin azumin Ramadan ko ya kamata ta dauki azumin kafin biyan bashi?
Shirin Najeriya a Yau na dauke da karin bayani da wasu batutuwan da ya kamata ku sani game da azumin na kwanaki shidan bayan karamar Sallah.Fri, 12 Apr 2024 - 556 - ‘Da Ƙyar Muka Iya Cefanen Sallah Bayan An Sauko Idi’Thu, 11 Apr 2024
- 555 - Wani Tela Ya Tsere Saboda Rashin Gama Ɗinkunan Sallah
Teloli iyayen haɗa gwarama! An saba kai ruwa rana a kowace Sallah idan teloli suka sha ta fi karfinsu.
Sai dai ba saban ba, wani telan da muka zanta da shi ya ce ya kammala dinkunan da ya karba kakaf yayin da wani ya tsere ya bar masu kaya da wayyo!
Shin wadanne dabaru ya kamata tela ya yi amfani da su wajen ganin ya sallami kowa? Shirin Najeriya a Yau na dauke da karin bayani.Tue, 09 Apr 2024 - 554 - Mutanen Da Aka Haramtawa Cin Zakkar Kono
Shin a wane lokaci aka yi umarnin fitar za Zakkar Fidda Kai?
Malamai sun ce wannan Zakka tana da matukar mahimmanci ga masu hali kuma akwai lokacin da aka kayyade a fitar da ita; in ba haka ba kuma ta zama sadaka.
Shirin Najeriya a Yau ya duba matakan fidda Zakatul-Fitr da mutanen da aka haramtawa cin ta.Mon, 08 Apr 2024 - 553 - Me Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Tsarin Raba Wutar Lantarki?
Tun bayan da aka kara kudin wutar lantarki mutane ke ta korafi game da yadda aka rarraba tsarin.
Amma har yanzu wasu na cewa ba su fahimci yadda tsarin yake tafiya ba da kuma yadda lamarin ke neman shafar rayuwarsu matuƙa.
Shirin Najeriya a Yau ya tattaun kan abubuwan da ya kamata ku sani game da sabon tsarin rabon lantarkin.Fri, 05 Apr 2024 - 552 - Yadda Za Ku Gane Daren Lailatul-Ƙadri Cikin Sauƙi
Akwai abubuwa na musamman da aka fi son a roƙa a irin wannan dare.
Yawanci an fi maida hankali a ranakun wutiri daga 25 zuwa 29, duk da yake malamai na ba da shawarar a yi ibada sosai a dukkanin ranakun goman karshe.
Shirin Najeriya a Yau ya tattauna da malamai gameda alamomin gane daren lailatul-ƙadri da abin da aka fi son bawa ya roƙa a ciki.Thu, 04 Apr 2024 - 551 - Matakan Kariya Daga Ɓata Gari A Lokacin Zuwa Tahajjud
Yanayin tsaro na jefa fargaba a zukatan wasu Musulmi da ke zuwa sallar dare ta Tahajjud.
Wasu ɓata gari kan yi amfani da wannan damar da mutane ke fita tsakar dare domin aikata musu abin da bai dace ba.
Shirin Najeriya a Yau ya duba wasu matakai na tsaro da za ku dauka domin kare kanku daga fadawa matsala.Tue, 02 Apr 2024 - 550 - Mutuwar Zuciya Ce Ta Jefa Matasa Harkar Kirifto
Shin a ganinku me ya sa matasa 'yan soshiyal midiya suka dukufa a harkar nan ta kirifto musamman 'mining' ?
A yanzu haka da dama ne cikin matasan ke jiran ta fashe domin su kudance, sai dai akwai masu yi wa irin wadannan matasa kallon masu raunin zuciya.
Shirin Najeriya a Yau ya tattauna da masu harkar mining da kuma masana kirifto kan abin da ya kamata ku sani kafin ku fara hakowa.Mon, 01 Apr 2024 - 549 - Illolin Yawaita Amfani Da Soshiyal Midiya A Ramadan
Yawan amfani da Soshiyal Midiya na haifar da gane-ganen abubuwan da ba su kamata ba.
A lokacin Ramadaan yana da kyau mutum ya yi kokarin kaucewa duk wani abin da zai raunana mishi azumi.
Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan abin da zai faru da ku idan kuka yawaita amfani a da soshiyal midiya a lokacin Ramadan.Fri, 29 Mar 2024 - 548 - Makomar Mutanen Da Aka Wanke Daga Zargin Alaƙa Da Boko Haram
Mutum sama da 300 aka saki ga gwamnatin jihar Borno a satin nan bayan wanke su daga zargin kungiyar Boko Haram.
An dade ana tsare da su tsawon shekaru amma sai yanzu aka gano ba su da hannu. To amma me dokar kasa tace game da irin wannan tuhuma bayan an gano gaskiya?
Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari kan halin da aka jefa su da kuma yadda doka za ta yi musu adalci.Thu, 28 Mar 2024 - 547 - "Shekara 8 Ina Tara Kuɗin Hajji Amma Yanzu Dole Na Fasa Zuwa"
Za a iya cewa aikin Hajji a Najeriya sai ga mai rabo, domin tun bayan bullar labarin hukumar alhazan Najeriya NAHCON na cewa an yi ɗori kan kudin da aka ware a baya ake ta ƙorafi.
Tuni wasu maniyyatan suka ce sun cire rai a yanzu, amma kuma hukumar ta ce akwai dalilan da babu yadda ta iya da su ne.
Shirin Najeriya a Yau ya duba matakin, da wasu suka ce yana neman hana talakan Najeriya zuwa aikin Hajji.Tue, 26 Mar 2024 - 546 - Yadda Gwamnati Ta Kasa Miƙa Ɗaliban Kuriga Ga Iyayensu
An shafe tsawon wunin jiya Lahadi ana zaman jira da dakon isowar daliban Kuriga da gwamnatin jihar Kaduna tace ta ceto.
Saidai daga bisani, ba tare da wani cikakken bayani ba an umarci iyayen yaran su sake dawowa a yau Litinin domin amsar ‘ya’yan nasu.
Shirin Najeriya a Yau ya duba abin da ya sa gwamnatin ta dauki wannan mataki ba tare da wani cikakken bayani ba.Mon, 25 Mar 2024 - 545 - ‘Kimiyya Ake Buƙata A Fannin Shari’a Ba Ƙarin Albashin Alkalai Ba’
Fannin shari'a musamman alkalai a matakin tarayya sun samu kari kan albashinsu na baya.
Ana ganin hakan zai samar da sauyi ga fannin shari'a da kuma dakile cin hanci ta wasu fannin, ko da yake wasu na ganin ba abin da ake bukata a fannin a yanzu ba kenan.
Shirin Najeriya a Yau ya duba sauyin da karin albashin zai iya haifarwa a kasar.Fri, 22 Mar 2024 - 544 - Illar Shiga Jerin Sunayen Masu Ɗaukar Nauyin Ta'addanci
'Yan kasa sun jima suna kalubalantar gwamnatin tarayya ta ayyana sunayen masu daukar nauyin ta’addanci.
Watakila gwamnatin ta duba wannan batu domin kamar yadda wasu suka ji a labari, ta bayyana sunan Tukur Mamu na jihar Kaduna da wasu mutane 14 waɗanda ɓaro-ɓaro ba za a iya cewa ta ambaci suna ba.
Shirin Najeriya a Yau ya duba matakan doka kan ayyana sunan wanda aka samu da daukar nauyin ta’addanci.Thu, 21 Mar 2024 - 543 - Me Ya Sa Mutane Suka Daina Shafa Turarukan Kamshin Jiki?
Da alama mutane sun fara kauda kai daga kula da wasu turarukan kamshin jiki.
Tsadar rayuwa ta sa mutane yanzu na cewa dole su nemi wasu dabarun, lura da yadda farashin irin wadannan kayayyaki na kula da tsaftar jiki ke kara tsada.
Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan yadda mutane suka daina amfani da wasu kayan tsaftar jiki.Tue, 19 Mar 2024 - 542 - Dabarun Samun Sadarwa Da Intanet A Lokacin Da Aka Samu Tangarɗa
A makon da ya gabata da dama daga cikin yan kasa sun fuskanci tangardar sadarwa musaman na intanet.
A cewar wasu ‘yan Najeriya ya taba kasuwancinsu da dama da harkokin yau da kullum ga shi basu samu mafita ba, duk da hukumomi sun ce hakan ya faru ne sanadiyyar lalacewar wasu bututun karkashin ruwa ne.
Shirin Najeriya a Yau ya lalubo muku hanyoyin da za ku samo mafita kafin a kammala irin wadannan gyare-gyare.Mon, 18 Mar 2024 - 541 - Matakan Kauce Wa Kamuwa Da Ciwon Ƙoda
Ƙoda na daga cikin sassan jikin dan adam da ke da mahimmanci wajen rayuwa mai lafiya da kwanciyar hankali.
A haka kuma, wasu ke siyar da kodar tasu guda daya duk da yike masana kiwon lafiya na cewa ganganci ne yin hakan.
A shirin Najeriya a Yau mun duba yadda za ku gane alamomin cutar koda da hanyoyin magance ta.Fri, 15 Mar 2024 - 540 - 'Kalaman Buhari Na Yabon Gwamnatin Tinubu Ba Su Dace Ba'Thu, 14 Mar 2024
- 539 - Yadda Za Ku Yi Girke-giken Ramadan Da Kuɗi Kaɗan
Yanayin tsadar rayuwa da ake ciki ya sa dole a yi tattalin kudin da ake kashewa.
An saba da Ramadana ana yawan yin girke-girke da kayan buda baki iri-iri, amma kuma wannan azumin ya zo cikin yanayi na tsadar kayan masarufi.
Shirin Najeriya a Yau ya duba hanyoyin da za ku yi girke-girken da yawa yadda aka saba cikin sauki ba tare da kashe makudan kudade ba.Tue, 12 Mar 2024 - 538 - ‘Yawan Karanta Littafai Na Sa Mutum Ya Fita Daban'
A wannan zamanin ba kowa ke da juriyar karanta littafai ba ko da kuwa ta waya ne, amma na alakanta hakan da shigowar fasahohin zamani da kimiyya.
Masana na cewa yawaita karance-karance na taimakawa basirar dan adam musamman littafai na zahiri.
Shirin Najeriya a Yau ya duba alfanun karanta littafai da wallafe-wallafe da ake yi wajen habaka kwazo da fikirar dan adamMon, 11 Mar 2024 - 537 - Ranar Mata Ta Duniya: ‘Hakikanin Abin Da Mata Suke Bukata’
Irin wannan rana ta 8 ga watan Maris Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar mata ta duniya domin duba rawar da suke takawa a fannoni daban-daban.
Wasu na ganin mata da dama da ke yiwa junan su hassada ya sa ba a samun ci gaban da ya kamata. yayinda ake ganin ya kamata a rika tallafawa ci gaban mata da kuma habaka tunaninsu.
Majalisar Dinkin Duniya, ta ce akwai mata kusan miliyan 342 da ke cikin barazanar fadawa kangin talauci nan da shekarar 2030. Sai dai ta ya za a kaucewa hakan?
Shirin Najeriya a Yau ya yi duba kan wannan rana da kuma yadda za a tallafi matan a fannoni daba-daban.
Fri, 08 Mar 2024 - 536 - Yadda Rashin Wutar Lantarki Ke Kassara Sana'o'i
Sana’o’i na samun cikas da koma baya a wasu sassan Najeriya sakamakon rashin wutar lantarki. A yan kwanakin nan ana yawan kokawa da yadda wutar lantarki ke ƙara tabarbarewa.
Masu sharhi na ganin da ace za a samu ingattaciyar wutar lantarki a Najeriya, to da cigaban da za a samu ya wice misali.
Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda rashin lantarki ke durkusar da kasuwanci a kasar.Thu, 07 Mar 2024 - 535 - Yadda Jama'a Ke Shan Wahalar Haɗa Lambar NIN da BVN a Bankuna
Tun bayan da CBN ta ba da umarnin a hada lambar NIN da BVN da asusun bankuna mutane ke ta turuwa domin ganin ba a kulle asusunsu ba.
Masana na ganin wannan mataki zai yi tasiri sosai wajen matakan tsaro a Fannin hada-hadar kudade.
Shirin Najeriya a Yau ya duba tasirin matakin da CBN ta yi umarni da yadda mutane ke shan wahalar gameda hakan.Tue, 05 Mar 2024 - 534 - Abin Da Ya Kamata Ku Sani Kafin Bayar Da Gudummawar JiniMon, 04 Mar 2024
- 533 - Yadda Za Ku Mori Rayuwa Kafin Ku Wuce Shekara 30
A lokacin da matashi ke cikin kuruciya a tsakankanin shekara 30, ana sa ran ya cimma wasu burika a rayuwarsa.
Toh amma a wannan yanayi da ake ciki, ta yaya matashi zai iya jin dadin rayuwarsa ta tafi kan tari kafin ya haura 30?
Shirin Najeriya a Yau na tafe da shawarwarin mafita ga wadanda su ka wuce shekaru 30 amma babu kwakkarar madafa.Fri, 01 Mar 2024 - 532 - Abin Da Zai Sa Farashi Ya Riƙa Sauka Bayan Ya Tashi
Yan kasa na kokawa kan yadda farashin komai ke hauhawa yayinda samun al’umma bai cika karuwa ba.
Ya riga ya zama al’ada da zarar farashin wani abu a Najeriya ya hau sama, ba lallai ya sauko kasa ba.
Shirin Najeriya a yau ya maida hankali kan sauyawar farashi abubuwa a Najeriya da yadda za a dauki matakin dakatar da hakan.Thu, 29 Feb 2024 - 531 - Alaƙar Da Ta Rage Tsakanin Ecowas Da Nijar, Mali Da Burkina Faso
Bayan daukar lokaci ana kai ruwa rana tsakanin ECOWAS da Nijar, Mali da Burkina Faso, daga kashe kamar yadda watakila wasun ku ke da masaniya an janye takunkuman kasashen.
Ana ganin cire takunkuman da aka yiwa kasashen dake karkashin mulkin soji zai dawo da ‘yar alakar da ta rage a tsakaninsu duk da yake wasu na ganin shin alaƙa kamar irin ta da za ta ɗore a yanzu?
Shirin Najeriya a yau ya duba matakan da za su taimaka kyakkyawar alaka ta dore tsakanin kasashen da Ecowas.Tue, 27 Feb 2024 - 530 - Abin Da Yasa Dala Ke Wahalar Da 'Yan NajeriyaMon, 26 Feb 2024
- 529 - Tallafin Da 'Yan Najeriya Ke Bukata
'Ƴan Najeriya sun samu kansu a yanayi na tsadar rayuwa sakamakon cire tallafin man fetur.
Wane tallafi 'ƴan Najeriya suka fi bukata a yanzu?
Wasu na bayyana tallafin kayan abinci da Gwamnatin Najeriya ke cewa tana bayarwa ba shine abin da ƴan ƙasar ke buƙata ba.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya dubi wannan batu.Fri, 23 Feb 2024 - 528 - Hanyoyin Samun Karin Kudin Shiga Baya Ga Albashi
A shekarun baya, idan mutum ya samu aikin albashi har murna ake taya shi, dan ana zaton ya kai tudun mun tsira, amma a ýan shekarun nan, masu daukar albashi na cikin wani hali domin kuwa duk karshen wata wani lokaci na biyan bashin da aka ci a tsakiyar watan, wani lokacin ma sai an ciyo wani bashin a iya biyan wani.
Ko kun san akwai wadansu hanyoyi halastattu da mai daukar alabshi zai iya samawa kansa mafita a wannan yanayi na tsadar rayuwa da rashin darajar Naira?
Ku biyo shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci domin jin wadannan halastattun hanyoyi na samun karin kudin shiga.Thu, 22 Feb 2024 - 527 - Yadda Za a Ceto Najeriya Daga Mawuyacin HaliTue, 20 Feb 2024
- 526 - Hanyoyin Kauce Wa Manyan Cututtuka A Lokacin ZafiMon, 19 Feb 2024
- 525 - Abin da Zai Faru da Tattalin Arzikin Najeriya
Tsadar rayuwa sakamakon karyewar darajar Naira da tashin farashin Dala, da kuma cire tallafin man fetur na cigaba da gasawa ýan Najeriya aya a hannu.
A tunaninku mene ne zai faru da tattalin arzikin kasar nan idan aka cigaba a haka?
Wani dan kasuwa ya bayyana mana hasashensa, kuma mun ji ta bakin wani masanin tattalin arziki. Ku biyo mu sannu a hankaliFri, 16 Feb 2024 - 524 - Bincike: Yadda Mayanka A Abuja Ke Samar Da Nama Mai Ƙazanta
Yana da kyau a kowane lokaci mu yi nazarin tsaftar naman da muke ci. Ta iya yiwuwa ba ku taɓa damuwa da sanin yadda ake sarrafa naman dabbobi a mahautu ba.
Za ku yi mamakin irin ƙazantar da bincikenmu ya banƙado ana yi da yaɗa cututtukan ga naman da mutane ke siya daga mahautu.
Shirin Najeriya a Yau ya maida hankali kan yadda wasu mahauta a birnin tarayya Abuja ke gudanar da aikinsu ba tare da tsafta kula da naman dake shiga gari ba.Thu, 15 Feb 2024 - 523 - Yadda Tasirin Rediyo Ya Sauya Al’ummar DuniyaTue, 13 Feb 2024
- 522 - Hanyoyin Haɗa Kan 'Yan Najeriya Ta Wasan Ƙwallo
Faɗin ƙasa da yawan kabilun da ke Najeriya sun sa zaman 'yan ƙasar uwa ɗaya uba ɗaya masu ƙawazucin juna gagara tun samun ƴancin kai.
Ko kun san hanyoyin da ya kamata abi domin haɗa kan ƴan ƙasar wuri guda masu so da ƙaunar juna domin ciyar da ƙasar gaba ta hanyar ƙwallon ƙafa?
Lura da goyon baya da fatan alkhairin da 'yan Najeriya suka nuna wa tawagar ƙwallon ƙafar Najeriya a gasar AFCON, mun dubi hanyoyin da za a bi domin samar da ƴan kasa masu haɗin kai da ƙawazucin juna.Mon, 12 Feb 2024 - 521 - AFCON: Yadda Za Ku Kauce Wa Bugun Zuciya Yayin Kallon Kwallo
Rahotanni sun tabbatar da mutuwar 'yan Najeriya uku sakamakon firgita da suka yi bayan an baiwa kungiyar kwallon kafar kasar bugun da ga kai sai mai tsaron gida yayin wasan su da takwararta ta Afirika ta Kudu.
Mene ne ke sanya zuciya bugawa har ta kai ga ajali ko mummunan jinya?
Mun binciko yadda wadannan bayin Allah suka gamu da ajalinsu yayin kallon wasan, mun kuma ji ta bakin wani likita kan hanyoyin kaucewa bugun zuciya.
Fri, 09 Feb 2024 - 520 - Matsalolin Da Ke Damun Arewacin Najeriya
Labarun da ke fitowa daga Arewacin Najeriya na nuna yadda yankin ya koma baya sakamakon ta'adancin Boko Haram, ýan bindiga masu satar mutane da karbar kudin fansa, ya janyo karuwar rashin aikin yi da rashin karatu a tsakanin jamaár yankin.
Mene ne gaskiyar matsalar wannan yanki?
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya tattauna da masu ruwa da tsaki daga Arewacin Najeriya, ya kuma bankado gaskiyar abin da ke damun yankin a halin da ake ciki.
Thu, 08 Feb 2024 - 519 - Yadda Ƙwai Ke Nema Ya Gagari 'Yan Najeriya
Kwai, daya daga cikin abinci mai gina jiki da ke da arha a da a Najeriya yanzu na shirin fin karfin talaka.
Nawa a ke sayar da kwai a yankin ku?
Kaso 80% cikin 100% na masu harkar kwai a jihar Kano sun bar harkar, wadan da suka rage suna yi sun rage maaikatansu. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya bi diddigin tsadar kwai a Najeriya.Tue, 06 Feb 2024 - 518 - Yadda Talakawa Za Su Biya Karin Da Akan Yi Wa Masu Shigo Da Kaya
Karin da Gwamnatin Najeriya ta yi wa masu karɓar dala domin shigo da kaya a jirgin Kago na ci gaba da shan fassara daga bakin masu ruwa da tsaki.
Ko ka san hanyoyin da manyan 'yan kasuwa za su tatsi kuɗaɗensu daga jikin talakawan ƙasar nan?
Shirin Najeriya A Yau ya dubi wannan batu da idon basira, ya ji ta bakin masu shigo da kaya ta wannan hanyar, ya kuma tattauna da masana.Mon, 05 Feb 2024 - 517 - Da Gaske 'Yan Jarida A Najeriya Na Azuzuta Matsalar Tsaro?
A lokuta da dama ýan siyasa da masu riƙe da madafun iko na bayyana ayyukan ýan jaridar ƙasar nan a matsayin wani yunkuri na azuzuta matsalar tsaron da ƙasar ke fama da shi, wani lokacin ma cewa su ke yi 'yan jaridar na firgita 'yaan wadansu ƙasashen da ke da niyyar saka hannun jari a Najeriya.
Shin da gaske ne ayyukan 'yan Jarida na azuzuta matsalar tsaron Najeriya?
Shirin Najeriya A Yau ya bigi jaki ya bigi taiki.Fri, 02 Feb 2024 - 516 - Abin Da Ya Sa Ba Zan Iya Daina Sa Hijabi Ba
Zamani ya zo da waɗansu ke yi wa mace mai saka hijabi kallon wacce bata cika ba, ko kuma wacce bata waye ba.
Shin ko har yanzu akwai matan da suka ji suka gani kan sanya hijabi?
Shirin Najeriya A YAU na wannan lokaci ya tattauna da waɗansu fitattun mata da suka yi fice a ilimin zamani amma kuma suna saka hijabi, mun tattauna kan dalilansu, mun kuma ji ta bakin malamai kan yadda hijabi yake a addinin Musulunci. Ku biyo mu sannu a hankali.Thu, 01 Feb 2024 - 515 - Yadda Za Ku Danne Fushi Idan Ranku Ya ƁaciTue, 30 Jan 2024
- 514 - Yadda Tsadar Rayuwa Tasa Aka Koma Hawa Jaki A Arewa, Kudu Kuma Tafiyar Kafa.
'Yan Najeriya na ci-gaba da fito da dabarun rayuwa a halin matsanancin haihuwar farashin da ya samo asali daga cire tallafin man fetur a kasar.
Ko kun san a kwai yankunan da Ar wacin Najeriya suka koma sufuri da jakuna a kudu kuma suka koma tafiyar kafa?
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe da karin bayani dangane da yadda rayuwa ke cigaba da canzawa a kasar nan.Mon, 29 Jan 2024 - 513 - Abin Da Ya Kamata Ýan Najeriya Su Tambayi Gwamnatin TinubuFri, 26 Jan 2024
- 512 - Yadda Wata Mata Ta Haihu A Kofar Gida A Mangu Saboda Yaki Bayan Dokar Hana Fita
Hukumomi a Jihar Filato sun bayyana saka dokar ta baci sakamakon rikicin kabilanci da ya rikide ya koma na addini a karamara Hukumar Mangu amma mahara sun ci gaba da kai hare-hare.
Mene ne abin da ya sa har yanzu ba a daina kai hari a Mangu ba?
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya binciko halin da ake ciki. ku biyo mu sannu a hankali.Thu, 25 Jan 2024 - 511 - Halin Da 'Yan Adawa Ke Ciki A Kano Da Filato
Jihohin Kano da Filato na hannun jam'iyyun adawa a matakin ƙasa. Tun bayan hukuncin kotun ƙoli ana ta hasashen ya makomarsu za ta kasance.
Akwai yiwuwar su iya saita alƙiblar gwamnati idan sun yi adawa mai ma'ana, yayinda ake sa ran gwamnati ta tafi da kowa.
Shirin Najeriya a Yau ya duba halin da 'yan adawa ke ciki a waɗannan jihohi.Tue, 23 Jan 2024 - 510 - Dabaru 10 Na Kaucewa Masu Garkuwa Da MutaneMon, 22 Jan 2024
- 509 - Za A Yi Wa Masu Sayar Da Rake Katin Shaida A Jihar Bauchi
Rahotanni daga Jihar Bauchi dake Arewa Maso Yammacin Najeriya sun bayyana cewa, gwamnatin jihar za ta yiwa masu sanaár sayar da rake katin shaidar sanaársu.
Ko mene ne ya yi zafi har ake shirin daukar wannan mataki a daidai wannan lokaci?
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya jiwo ta bakin gwamnatin jihar, dama masu raken.
Domin sauke shirin kai tsaye, latsa nan
Fri, 19 Jan 2024 - 508 - Abin Da Ya Sa Rashin Tsaro Ke Neman Cinye Abuja
A ‘yan kwanakin nan hankali ya koma birnin tarayya Abuja ta fannin tsaro.
‘Yan bindiga da masu garkuwa dan neman kudin fansa suna ta farmakar yankunan birnin da ake ganin wuri mafi tsaro a Najeriya.
Shin me ya sa ‘yan bindigar suka karkato da ayyukansu a yankin?
Shirin Najeriya a Yau ya duba abin da ya sa masu garkuwan suka maida hankali kan birin tarayya Abuja.Thu, 18 Jan 2024 - 507 - Dabarun Cin Jarabawar 'JAMB' Cikin Sauki
A duk lokacin da ɗalibai ke shirin rubuta jarabawar share fagen shiga jami'a wato JAMB a kan karfafa musu gwiwa gameda dagewa da dabarun da za su sa suyi nasara.
Yawanci akan ce ba a cika samun nasarar JAMB a tashin farko ba. To amma akwai wasu dabarun da ya kamata masu shirin jarabawar su bi cikin sauki.
Shirin Najeriya a Yau ya yi nazarin matakan da ya kamata masu shirin rubuta jarabawar su bi domin samun nasara.Tue, 16 Jan 2024 - 506 - Mece Ce Makomar Jam'iyyar APC A Jihar Kano ?Mon, 15 Jan 2024
- 505 - Yadda Ake Huce Gajiya Cikin Sauki
Mutane da dama na bayyana rashin samun cikakken hutu koda kuwa sun kwashe lokaci mai tsayi suna bacci, wadansu kuma in sun kwanta sai tunani ya mamayesu har baccin ya gagara.
Shin wadanne hanyoyi mutum zai bi domin ya ware gajiya?
Shirin Najeriya A Yau ya yi nazari kan wannan batu lura da yadda rashin hutu da shan maganin gajiya ke neman zama aláda a tsakanin alúmma.
Fri, 12 Jan 2024 - 504 - Anya Bola Ahmed Tinubu Na Duba Makomar Siyasarsa?
Daukar matakin ba sani ba sabo da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ke yi ya fara janyo ce-ce-ku-ce dangane da makomar siyasarsa.
Shin ko nuna halin ba sani ba sabo da shugaban ke nunawa zai shafi siyasarsa?
Shirin Najeriya A Yau ya yi nazari kan wannan batu ta hanyar tattaunawa da ýan kasar na da kuma masana kimiyyar siyasa da sharhi akan alámuran yau da kullum.
Domin sauyke nshirin kai tsaye, latsa nan.
Thu, 11 Jan 2024 - 503 - Makomar Ministar Jinkai Betta Edu Da Shugabar NSIP Halima Shehu
Tun bayan dakatar da ministar jin kai ta Najeriya Betta Edu a jiya Litinin 8 ga Janairu da kuma Halima Shehu daga matsayin shugabar hukumar bada tallafin dogaro da kai ta kasa kwanaki 6 tsakani 'yan Najeriya sun fara bin kwakkwafin wane hali su ke ciki, kuma mene ne abin da ya sa aka dakatar da su?
Shirin Najeriya A Yau ya binciko cikakken abin da ake zarginsu, ya kuma ji ta bakin masanin shari'a kan makomar wanda ya aikata abin da ake zarginsu da shi.
Tue, 09 Jan 2024 - 502 - Dabarun kauce Wa Talauci A Watan Janairu
Biyo bayan bukukkuwan da ake gudanarwa a karshen shekara musamman a watan Disamba, mutane na fadawa cikin halin yaya zan yi a watan Janairu, sakamakon biyan albashi da wuri da ake yi a watan 12.
Shin kun san hanyoyin da zaku bi domin kaucewa mummunan talauci a cikin wannan watan na Janairu?
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe da karin bayani da shawarwari na musamman, ku biyo mu sannu a hankali.
Mon, 08 Jan 2024 - 501 - Matakan Magance Matsalar Tsaro Kafin 2024 Ta Ƙare
Tun bayan da gwamnatin tarayya ta sha alwashin dakile matsalar tsaro kafin shekarar 2024 ta kare, jama’a ke ta diga ayar tambayar kan salon da take shirin bi.
Wasu na ganin ba lallai su yarda da kalaman gwamnatin ba. Saidai masana tsaro sun yi hasashen wasu matakai da gwamnatin za ta iya dauka idan har gaske tana son magance matsalar tsaro kafin 2024 ta kare.
Shirin Najeriya a Yau ya duba wasu matakai da suka kamata a bi wajen dakile matsalar tsaro kafin shekarar 2024 ta ƙare.Fri, 05 Jan 2024 - 500 - Yadda Injin Rubutu Na 'Braille' Ke Taimakawa Makafi Cimma Buri
Ranar 4 ga watan Junairu ce ranar da Majalisar Dinkun Duniya ta ware albarkacin wane sashe na rayuwar masu lalurar gani a fannin iliminsu
Mutane masu lalurar gani suna amfani da wani inji da ake kira 'Braille' wajen rubutu a madadin allo da alkalami. Yau ita ce ranar da ake kira da 'World Braile day'a turance.Shin ya mahimmancin wannan rana take a garesu, shirin Najeriya a yau ya maida hankali kan hakan.
Thu, 04 Jan 2024 - 499 - Hanyoyin Samun Kuɗi A 2024
Sabuwar shekara tana zuwa da sabbin fata daga al’umma musamman ta fannin tattalin arzikinsu.
Duba da yanayin matsin tattalin arziki, masu fashin baki na shawartar al’umma da su nemi wasu hanyoyin da za su rika samun kudaden shiga fiye da guda daya ko kuma kaucewa dogaro da albashi kaɗai.
Shirij Najeriya a Yau ya duba wasu dabaru da hanyoyin da za ku samu kudaden shiga fiye da daya a 2024.Tue, 02 Jan 2024 - 498 - 2024: Yadda Za Ku Tafiyar Da Sabuwar Shekara Salim-Alim
Shekara sabuwa ba wuya ga mai yawancin rai. Kowacce shekara na zuwa da nata yanayin.
Jama'a na da kyakkyawan fata a wannan shekara ta 2024 miladiyya, duk da yake ana cikin yanayi na matsi. Amma ta yaya za ku gudanar da sabuwar shekarar ku salim-alim?
Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda ya kamata ku saisaita al'amuran yau da kullum domin tafiya bisa tsari.Mon, 01 Jan 2024 - 497 - Dambarwar Siyasar Da Suka Faru A 2023
Shekarar 2023 ta kasance cikin zazzafar siyasa da aka gudanar da babban zaben shugaban kasa da gwamnoni.
Abubuwa da dama sun faru masu daukar hankali da kuma yadda aka samu sauyin salon siyasa a wasu sassan kasar a shekarar dake karewa.
Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari kan wasu mahimman abubuwan da suka faru a fagen siyasa a 2023.Fri, 29 Dec 2023 - 496 - Yadda Aka Sha Fama Da Matsin Tattalin Arziki A 2023
Shekarar 2023 ta fara da yanayi na matsin tattalin arziki a lokacin da gwamnati take gab da karewa.
Ana sa ran ganin sauyi da zuwan sabuwar gwamnati a fannoni daban-daban da suka shafi tattalin arziki da tsadar rayuwa gami da hauhawar farashi. Shin a wane mizani za a auna tattalin arzikin Najeriya a shekarar 2023?
Shirin Najeriya a Yau ya yi waiwaye da nazarin halin da tattalin arzikin kasar ya kasance a 2023.Thu, 28 Dec 2023 - 495 - Tsadar Rayuwa: ‘Ba Mu Da Zarafin Bayar Da Kyautar Kirsimeti A Wannan Shekara’Wannan rana ta washe garin Kirsimeti ce ake kira ‘Boxing Day’ a turance. Rana ce ta raba kyaututtuka ga ‘yan uwa da abokan arziki.
Sai da a yanayin da ake ciki na matsin tattalin arziki, shin al’umma na da zarafin yin kyautuka kamar yadda aka saba? me ya sa ake mata laƙabi da ‘boxing day’, kuma wace irin kyauta ya kamata a bayar?
Ku biyo mu cikin shirin Najeriya A Yau domin jin yadda wasu mutanen suka tunkari wannan rana a yanayi na tsadar rayuwa.Tue, 26 Dec 2023 - 494 - Kirsimeti: "Mun Kasa Zuwa Ko Ina Saboda Tsadar Rayuwa"
Bikin kirsimetin wannan shekara ya zo a yanayi na matsin tattalin arziki, amma duk da haka wasu na gudanar da shagali yadda aka saba
Ranar 25 ga watan Disambar kowace shekara, mabiya addinin kirista a fadin duniya na gudanar da bikin tunawa da Almasihu, kamar dai yau litinin ta shekarar 2023.
Shirin Najeriya A Yau ya duba yadda mutane ke gudanar da bikin kirsimetinsu da yanayin matsin tattalin arziki da ake ciki.Mon, 25 Dec 2023 - 493 - Dalilin Da Aka Samu Ƙaruwar Masu Taɓin Ƙwaƙwalwa a 2023
Yayinda ake gargarar kammala shekarar 2023, abubuwa da dama sun faru da al’umma masu ban sha’awa da ban mamaki.
Hukumomi sun ce an samu karin kashi 100 na wadanda aka kai asibiti domin duba lafiyar kwakwalwarsu a shekarar 2023.
Shirin Najeriya A Yau ya duba yadda mutane suka tsallake wasu damuwa da kuma abinda masana suke ganin shine ummul haba’isin shigar jama’a cikin dimuwa da rikicewar kwakwalwa.Fri, 22 Dec 2023 - 492 - Zazzaɓin 'Dengue': Haɗarin Da Ya Kamata Ku Sani Gameda Cutar
Hukumar Lafiya ta Duniya ta lissafa zazzaɓin Dengue cikin cutuka masu barazana ga bil'adama a fadin duniya.
A 'yan kwanakin Cibiyar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta ce ana zargin sama da mutum 71 sun kamu da cutar zazzaɓin Dengue, yayin da tuni aka tabbatar cewa mutum 13 sun harbu da ita a jihar Sokoto.
Shirin Najeriya a Yau ya maida hankali kan matakan da ya kamata ku dauka na kariya da wasu abubuwan da ya kamata ku sani kan cutar Dengue.Thu, 21 Dec 2023 - 491 - Yadda Za Ku Gane Kayan Abinci Marasa Inganci Nan Take
Ana yawan cin karo da kayan abinci ko na sha da basu da inganci, kuma ga dukkan alamu sun cika sharuddan sahihanci a ido.
Hukumomi na yawan kama darurwan kwalaben kayan sha da ci na jabu ne amma kuma ga su dauke da lambar dake nuna sahihancin su. Akwai masu kirkirar kayan jabu da dama domin shigar da su kasuwa.
Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda za ku gane kayyakin da ba su da inganci a tashin farko.Tue, 19 Dec 2023 - 490 - Me Ya Sa Ake Daukar Masu Kwarewar Aiki A Bar Masu Digiri?
Jama’a da dama na burin da zarar sun mallaki takardar digiri, za su samu domin sun kammala jami’a.
Saidai a yanzu da alama masu daukar aiki suna yawan tallata neman ma’aikata, amma kuma a cikin sharudda za a ce dole sai mai kwarewa a da sanin makamar aiki a fannin.
Shirin Najeriya a Yau ya duba abin da ya sa masu daukar aiki suka fi sha’awar masu kwarewa fiye da masu kwalin digiri kawai.Mon, 18 Dec 2023 - 489 - Munanan Cututtukan Da Fitsari A Waje Ke HaifarwaFri, 15 Dec 2023
- 488 - Matakin Da Zai Sa Farashi Ya Sauka Bayan Ya Ƙaru
‘Yan kasa na kokawa kan yadda farashin komai ke hauhawa yayinda samun al’umma bai cika karuwa ba.
Ya riga ya zama al’ada da zarar farashin wani abu a Najeriya ya hau sama, ba lallai ya sauko kasa ba.
Shirin Najeriya a yau ya maida hankali kan sauyawar farashi abubuwa a Najeriya da yadda za a dauki matakin dakatar da hakan.Thu, 14 Dec 2023 - 487 - Yadda Ma’aikaciyar Gwamnatin Kano Ta Rasu Saboda Rashin Albashi
Tun bayan da gwamnatin jihar Kano tace ta tantance tare da dawo da wasu ma'aikatan da ta dakatar saboda rashin bin ka'ida, suke ta zura ido domin ganin an biya su hakkokinsu.
Sai dai a yayin da suke jiran, rayuwarsu ta shiga cikin tasku da halin ni 'yasu ta yadda har aka kai ga rasa rai da wasu kalubale da dama.
Shirin Najeriya a Yau ya duba halin da ma'aikatan jihar Kano da aka maida suka shiga saboda rashin biyansu hakkokin nasu.Tue, 12 Dec 2023 - 486 - Yadda Ake Rubutun “Project” A Manyan MakarantuMon, 11 Dec 2023
- 485 - Abin Da Mutumin Da Ya Wuce Shekara 30 Ya Kamata Ya Yi
A Jiya Alhamis cikin shirin Najeriya A Yau mun dubi yadda da zarar an ga shekaru sun dan fara ja ana sa ran a cimma wani buri na rayuwa da zai sa a ga cewa mutum ya fara samun cigaba da zama cikakken mutum. Mun yi amfani da shekaru 30.
Shin ka saurari wannan shirin da ya yi magana kan Matakin Da Ya Kamata Matashi Ya Kai Kafin Ya Cika Shekara 30?
A yau shirin na tafe da shawarwarin mafita ga wadanda su ka wuce shekaru 30 amma babu kwakkarar madafa.Fri, 08 Dec 2023 - 484 - Wane Mataki Ya Kamata Mutum Ya Kai Kafin Shekara 30
Shin kun taba tambayar kanku matsayin da ya kamata matashin da bai wuce shekara 30 ya taka?
Da zarar shekaru sun ja ana sa ran a cimma wani buri na rayuwa da zai sa a kalli cewa mutum ya fara samun cigaba da zama cikakken mutum.
Shirin Najeriya a Yau ya duba matakin da ya kamata a ce mutum ya kai kafin cika shekara talatin a rayuwa.
Thu, 07 Dec 2023 - 483 - Makomar Kakakin Majalisa Ɗan Jam'iyar Adawa A Filato
Ana ta kai ruwa rana a majalisar jihar Filato gameda yadda shugabanci zai kasance daga ɗan jam'iyar adawa da ba su da rinjaye.
Akwai 'yan majalisar APC da kotu ta baiwa nasara bayan tsige mafi yawancin yan jam'iyar PDP, duk da yake ba a rantsar da su ba amma majalisa tana hutu.
Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda ake tirka-tirka a majalisar dokokin jihar Filato da zargin barazanar tsige kakakinta.Tue, 05 Dec 2023 - 482 - Manyan Cututtukan Da Zazzabin 'Malariya' Ke Iya JanyowaMon, 04 Dec 2023
- 481 - Yadda Ýan Damfara Ke Turawa Mutane “Rasit” Da “Alat” Din Bogi
Ýan damfara kullum na kara kaimu wurin fito da sabbin dabarun cutar jamaá ta hanyoyi daban daban.
Shin ko kun san ana iya tura maka alat da rasit din kudi na bogi?
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya tattauna da wadansu da aka turawa rasit da alat na bogi, ya kuma ji ta bakin wani masani kuma mai sharhi akan dabarun sadarwa ta intanet.Fri, 01 Dec 2023 - 480 - Yadda Mabaratan Zamani Ke Neman Hana Bayar Da Sadaka
Lamarin ya kai da wuya mutum ya fito ya koma gida ba tare da wani ya yi masa ba-zata ya roke shi kudi ko abin ci ba.
Yawancin masu irin wannan rokon sukan fito ne tsaf-tsaf kamar wasu ma’aikata ko ’yan kasuwa.
Shin yaya jama’a ke kallon wannan dabi’a da ta zama ruwan dare?
Shirin Najeriya A Yau na wanna lokaci na tafe da karin bayani.
Thu, 30 Nov 2023 - 479 - Abin Da Ya Sa Masu Zaman Waƙafi Ke Shafe Shekaru Ba Hukunci
Rayuwa ta kan sauya a duk lokacin da mutumin da ke zaman waƙafi a gidan kaso ya shafe dogon lokaci babu hukunci amma daga bisani aka sake shi.
Akwai dubban mutane da ke jiran yanke hukunci a kotuna da kuma waɗanda basu san makomar su ba.
To amma me ya sa ake samun wannan tsaiko? Abin da shirin Najeriya na yau ya duba kenan.Tue, 28 Nov 2023 - 478 - Yadda ‘Yan Najeriya Ke Tafka Asara Saboda Wasa Da LokaciMon, 27 Nov 2023
- 477 - Shin Ko Akwai Lalaci Kan Yadda Wasu Mazan Kan Sakarwa Matan Su Ragamar Gida
Tun dauri a arewacin Naijeriya, Maza aka sani da rike da ragamar gida, ta hanyar fita a nemo abun da za a ciyar da iyali, yayin da mata ke lura da aikace-aikacen gida.
Wasu matan kan yi sana’o’i na gida da niyyar samun kudin kashewa da ba dole sai an tambayi maigida ba.
To a yanzu an shiga yanayin da wasu mazan ke sakarwa mata ragamar gida kacokan.
Shirin Naijeriya A Yau, ya yi duba ne kan wannan ta’ada ta wasu mazajen, da yadda matan ke fama wajen daukar nauyin gida.Fri, 24 Nov 2023 - 476 - Matakan Da Za Ku Kare Lafiyar Ku A Lokacin SanyiThu, 23 Nov 2023
- 475 - Shin Hukuncin Kotuna Kan Gwamnoni Ya Sauya Dimokariɗiyya?
Kotuna da dama sun yanke hukunci mabanbanta a kan kujerun gwamnoni, inda aka soke wasu da suke jam'iyyar adawa da ma jam'iya mai ci.
Ana ganin hakan kamar wani sauyi ne ga dimokraɗiyya wajen yanke hukunci ba sani ba sabo.
Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari kan ci gaban da aka samu ga dimokraɗiyya bayan hukunce-hukuncen kotuna kan kujerun gwamnoni.Tue, 21 Nov 2023 - 474 - Yadda TikTok Ke Lalata Tarbiyyar MatasaMon, 20 Nov 2023
- 473 - Hanyar Da Za A Kaucewa Tsadar Albasa
Buhun albasa a kasuwannin Arewacin Najeriya ya kai sama da Naira Dubu Dari a ýan kwanakin nan.
Shin mene ne abin da ya sa albasa tsada fiye da sauran shekaru a Najeriya?
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya tattauna da manoma, manyan ýankasuwar albasa da kuma wata likitar abinci akan tsadar albasa da amfaninta a jikin dan Adam.
Fri, 17 Nov 2023 - 472 - Yadda Yajin Aiki Ke Shafar Fannin Ilimi
Yajin aikin 'yan ƙwadago ya haɗa har da na malaman jami'o'i a Najeriya, inda aka kulle makarantu a matakai daban-daban.
Hakan yana shafar ɓangaren ilimi da wasu ke ganin za a samu koma baya idan ba a dakatar da yajin aikin ba.
Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari kan tasirin yajin aiki ga fannin ilimi ko akasin haka.Thu, 16 Nov 2023 - 471 - Abin Da Ke Hana Magani Aiki A Jikin Mutum
Mutane da dama kan ce wani magani ya daina yi musu aiki ko kuma baya yi musu aiki bayan a wani lokaci da ya wuce yana yi musu aiki.
Mene ne abin da ke hana magani aiki a jikin mutum?
Shirin namu na wannan lokaci na tafe da tattaunawa ta musamman akan abin da ke hana magani yin aiki a jikin dan-Adam.
Tue, 14 Nov 2023
Podcasts similar to Najeriya a Yau
- Health Naturally with Denis Stewart 2NURFM
- Aa Gym Official Aa Gym Official
- Al-Quran Al-kareem Al-Quran Al-kareem
- CNN Indonesia CNN Indonesia
- dakwah.me - Ustadz Adi Hidayat dakwahme
- KH ANWAR ZAHID OFFICIAL Dakwah NU
- Dakwah Tauhid Dakwah Tauhid
- Dzulqarnain Muhammad Sunusi Dzulqarnainms
- Ngaji Bareng Gus Baha Gus Baha
- Ps. Juan Mogi Juan Mogi Official
- Kajian Ustadz Khalid Basalamah Kajian Islam
- K.H. ZAINUDDIN MZ K.H. ZAINUDDIN MZ
- Kumpulan Dakwah Islam Lentera Pagi
- Ludruk Cak Kartolo dkk Ludrukan
- Merry Riana Merry Riana
- Ceramah Fahrudin Faiz Monkey D Lover
- Murottal Qur'an Terjemahan Audio Indonesia Muslim
- Ngaji Gus Baha' Ngaji Gus Baha'
- Lima Menit Berita Podcast Tempo
- Wayang Kulit Indonesia Raden Ontoseno
- Radio Rodja 756 AM Radio Rodja 756AM
- GUS BAHA sofa bisnis
- Ustad Das'ad Latif Ustad Das'ad Latif
- Misteri Seru Widya Yudha Utama