Nach Genre filtern

Al'adun Gargajiya

Al'adun Gargajiya

RFI Hausa

Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam.  Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.

399 - Jamhuriyar Nijar ta gudanar da bikin ranar Hausa ta bana a ƙasar
0:00 / 0:00
1x
  • 399 - Jamhuriyar Nijar ta gudanar da bikin ranar Hausa ta bana a ƙasar

    Shirin Al’adumu na gado a wannan makon ya sake waiwayar baukukuwan ranar Hausa ne ta Duniya, ranar da babban taronta ke gudana a dukkanin ranakun 26 ga watan Agusta duk shekara, to amma kasancewar bikin ya samu karɓuwa a gwamman ƙasashe ya sa bayan babban taron ake gudanar da wasu ƙarin bukukuwan ranar hausar ta Duniya a ƙasashe daban daban, ciki har da Jamhuriyar Nijar, inda aka gudanar da bikin zagayowar ranar hausar ta Duniya a ranar 8 ga watan Satumban da muke.

    Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Nura Ado Sulaiman.

    Tue, 15 Sep 2026
  • 398 - Muhawara kan banbance tsakanin ƙabilun Hausawa da kuma Fulani a Najeriya

    Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon ya mayar da hankali kan zamantakewa da auratayyar ƙabilun Hausawa da Fulani, ƙabilu 2 da suka juye zuwa Hausa Fulani bayan zaman tare na tsawon shekaru musamman a Najeriya.

    A baya-bayan nan muhawara ta fara zafi kan buƙatar banbance ƙabilun biyu zuwa Hausa daban da kuma Fulani zalla, lamarin da ya ci karo da fahimtar wasu daga cikin masana a ɓangaren al'adu.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    Tue, 08 Sep 2026
  • 397 - Batutuwan da bikin 'Ranar Hausa ta Duniya' zai mayar da hankali kai a bana

    Shirin Ala'adunmu na gado a wannan mako ya mayar da hankali ne kan 'Ranar Hausa ta Duniya' 'lokaci na musamman da ake amfani da shi wajen tunatar da muhimmancin harshen Hausa da kuma Al’adun Hausawa.

    Ku danna alamar sautin da ke sama domin sauraron cikakken shirin tare da Abdoullaye Issa...........

    Tue, 25 Aug 2026
  • 396 - Halin da ake ciki game da al'adar 'Yan Kama da ke neman ɓacewa a ƙasar Hausa

    Shirin "Al’adunmu na gado, ya mayar da hankali kan fadi-tashin da ake yi don adana tsohuwar al'adar mawaƙan 'Yan Kama a ƙasar Hausa.

    Waƙoƙin 'Yan Kama salon fasaha ne na musamman da mawaƙan ke amfani da shi domin nishaɗantarwa, inda suke sauya shahararrun waƙoƙi su koma na maganar abinci ko cika tumbi.

    A cikin shirin, masana sun bayyana yadda waɗannan mawaƙa ke da ƙwarewa wajen sarrafa harshen Hausa da sauya salon magana don juyata zuwa nishaɗi.

    Sai dai bincike ya nuna cewa wannan daɗaɗɗiyar al'ada tana dab da ɓacewa gaba ɗaya a wannan zamanin na yanzu.

    Babban dalilin da ya sa sana'ar ke mutuwa shi ne rashin gado, domin kuwa ko da su kansu 'ya'yan mawaƙan na 'Yan Kama ba sa sha'awar ɗaukar wannan sana'a don gadon iyayensu kamar yadda aka saba a baya.

    Tue, 18 Aug 2026
  • 395 - Wane tasiri Chamfi ke da shi wajen gyarawa ko kuma ruguza aure musamman a zamanin baya

    Shirin Al'adunmu na gado na wannan mako zai mayar da hankali ne kan yadda Chamfe-Chamfe ke shafar lamuran auratayya musamman a zamanin baya.

    Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shrin tare da Abdullahi Isa

    Tue, 04 Aug 2026
Weitere Folgen anzeigen

Andere Nachrichten und Politik Podcasts