Nach Genre filtern
- 309 - Yadda matsalar tsuntsayen Jan Baki ta addabi manoma a jihar Jigawa
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan mako ya yi duba ne kan matsalar tsuntsayen jan baki da ke lalata gona komai girmanta a duk lokacin da suka durfafeta a jihar Jigawa da ke Arewacin Najeriya, wadda ta yi ƙamarin da har wasu manoma na cewa, dabarun da suka daɗe suna amfani da su wajen korar tsuntsayen sun kasa magance matsalar, lamarin da ya tilasta musu neman wasu sabbin hanyoyi.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nasiru Sani...........
Sat, 03 Oct 2026 - 308 - Hukumar NIMET a Najeriya ta yi hasashen yiwuwar ambaliya a jihoh 13 na ƙasar
A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan duba sabon hasashen da Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya ta yi, game da yiyuwar samun matsalar ambaliyar ruwa a wasu jihohi 13 na kasar a wannan damunar.
A baya-bayan nan, hukumar hasashen yanayi ta Nigeria wato NIMET, ta sake fito da wani sabon hasashen yiyuwar ambaliyar ruwa a cikin watan Agustan wannan shekara, tsakanin ranar 11 zuwa 20 ga watan na Agusta, a wasu jihohi 13 na kasar.
Cikin sanarwar da ta bayar, hukumar ta NIMET, ta bayyana cewa hasashen nata, ya dogara ne kan adadin ruwan saman da ake fatan samu, da yanayin kasa tare da girman magudanan ruwa da kuma yawaitar madatsun ruwa.
Sat, 26 Sep 2026 - 307 - Matsalar ambaliyar ruwa da ake samu duk lokacin damina a ƙasashen Afrika
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan mako ya yi duba ne kan matsalar ambaliyar ruwa da ake fuskanta kowace shekara lokacin damina a sassan ƙasashen Afrika.
Kamar kowace shekara, a bana ma ana hasashen samun ambaliyar ruwa a wasu kasashen yammacin Afrika, inda akan samu rasa rayuka da dukiya mai tarin yawa. A Najeriya, an sha samun hasarar rayuka a sanadin matsalar ambaliyar ruwan, da kan rutsa da wasu yankunan kasar.
Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Sat, 19 Sep 2026 - 306 - Alfanun gandun daji wajen baiwa muhallin ɗan Adam kariya daga gurɓacewa
Shirin Muhallinka Rayuwarka tare da Nasiru Sani a wannan mako ya mayar da hankali ne kan gudunmawar Gandun daji ga ci gaban Muhalli a wani yanayi da duniya ke ganin ta'azzarar matsaloln da ke illa ga muhalli walau na kai tsaye ko kuma wanda ɗan adam kan haddasa.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Sat, 12 Sep 2026 - 304 - Ƙarancin yashin gini na haddasa rikici tsakanin jama'a da illa ga muhalliSat, 15 Aug 2026
- 302 - Yadda dazuka ke taimakawa wajan kare muhalliSat, 08 Aug 2026
- 301 - Matakan da manoman Nijar ke ɗauka a lokutan da aka fuskanci ƙarancin ruwan samaSun, 02 Aug 2026
- 300 - Illolin karancin gonaki kusa da jama'a da yadda ya shafi burin bunkasa samar da abinci
Sau da dama, masu burin shiga harkokin noma a Nigeria kan canza tunaninsu, sakamakon rashin samun gonakin da za su noma kusa da gari, lamarin da kan tilasta su jingine aniyarsu ta yin noma.
Gwamnatin Nigeria dai, ta sha kira ga ‘yan kasar da su koma gona, la’akari da yadda Allah ya albarkaci kasar da wadatattun filayen noma da kuma yanayi mai kyau da za a iya noma kowane irin nau’in kayan abinci.
Sat, 25 Jul 2026 - 299 - Matsalar ambaliyar ruwa da kan dagula lamuran al’uma a NajeriyaSat, 20 Jun 2026
- 298 - Masana na ci gaba da tsoratar da al'umma game da illolin da ke tattare da gurɓatacciyar iska
A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan tasirin gurɓatacciyar iska ga lafiyar halittu da muhalli wato air pollution a turance.
Iska na gurɓa ta ne ta hanyoyi da dama, kama daga hayaƙin na’urori wato injina a masana'antu, zuwa tarkacen bola ko kuma ƙone wasu abubuwa, wanda su ke kawo cikas ga yanayin muhalli tare kuma da kawo tazgaro ga lafiyar ɗan Adam.
Sat, 13 Jun 2026 - 297 - Kananan manoma a Najeriya na nan kan tsarin noma na kaka da KakanniSat, 06 Jun 2026
- 296 - Yawaitar takin jabu ya zamewa Manoman Najeriya ƙalubale a banaSat, 23 May 2026
- 295 - Sauyin Yanayi ya jefa Manoma cikin ruɗani kan lokacin da ya dace su fara shuka
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon ya tattauna na a kan yadda samun saukar Ruwan Sama na farko a bana ya jefa manoma a jihohin Arewacin Najeriya cikin ruɗani dangane da lokacin da ya dace su fara shuka.
Wannan na zuwa ne a yayin da hukumar hasashen Yanayi ta Najeriya wato NIMET, da uma wasu masana ke gargaɗi game da yiwuwar ɗaukewar ruwan saman da wuri, lamarin da zai yi janyo tafka hasarar akasarin amfanin gonar da aka shugka da wuri.
Sat, 16 May 2026 - 294 - Yadda saukar ruwan sama na farko ya jefa manoma cikin ruɗani
A yau wannan shiri zai ba da hankali ne akan yadda Ruwan sama na farko da aka samu a baya-bayan nan ya jefa manoma a jihohin Arewacin Najeriya cikin ruɗani da fargaba, yayin da hukumar hasashen yanayi ta ƙasa, NiMet, da masana ke gargaɗi game da tsagaitawar ruwan saman da wuri wanda zai iya lalata duk wani amfani da aka yi a wannan lokaci.
Sat, 09 May 2026 - 293 - Matsalar karancin tsaftataccen ruwa, na ci gaba da addabar iyalai a sassan Nigeria
Matsalar nan ta karancin tsaftataccen ruwa, na ci gaba da addabar miliyoyin iyalai a sassan Nigeria, kila ko saboda rashin samun damar jan ruwan famfo a gidajensu, ko kuma rashin samun ruwan daga hukumomin samar da ruwan famfo na jihohinsu, duk da makudan kudin da gwamnatocin jihohin ke warewa, da sunan samar da ruwa wa jama’arsu.
Wannan matsala ba kawai ta tsaya kan iyalai da kan rasa ruwan amfanin yau da kullum a gidajensu ba, har ma tana shafar ingancin muhalli, kasancewar a kan muhallin a kan dawo, don neman ruwan a karshe.
Sat, 02 May 2026 - 292 - Karfafa gwiwa ga jama'a su koma noma a jamhuriyar Nijar
Shirin muhallinka rayuwarka na wannan mako zai maida hankali ne kan yanda ake karfafa gwiwa ga jama'a su koma noma don ita ce babbar hanyar dogaro da kai ta fuskar abinci.
Tun bayan halin matsin da jama'ar Jamhuriyar Nijar suka shiga biyo bayan juyin milkin soja da ta haddasa karamcin da tsadar abinci a cikin kasar aka rika zaburar da mutane su kama aikin noma musamman abincin da aka shigo da shi daga ketare Wanda ba a nomawa a cikin kasar irinsu shinkafa. Aka dai ce da rashin tayin ake barin arha, ganin yanda gwamnati ta kyautata wuraren da za a iya aikin noma a sassan kasar daban daban, mutane da yawa sun fada noman kuma hakika kwalliya ta fara biyan kudin sabulu.
Sat, 25 Apr 2026 - 291 - Matasan kasashe 11 da ke cikin tsarin shingen kare Hamada suka kai rangadi a Nijar
A yau shirin zai leka jamhuriyar Nijar ne inda matasa daga kasashe 11 da ke cikin tsarin shingen kare Hamada da zaizayewar kasa don mayar da yankin tsanwa suka kai rangadi a Nijar musaman a Jihohi 5 na kasar da suka hada da Tillaberi Niamey, Dosso, Maradi da Zinder don duba irin cigaban da Nijar ta samu a wannan fannin da nufin kwaikwayonsa don kaddamar da shi a kasashensu.
Sun, 19 Apr 2026 - 290 - Dalilan da suka sanya Manoma Albasa a Nijar fuskantar ƙalubale a bana
Shirin 'Muhallinka Rayuwarka' na wannan makon, ya yi tattaki zuwa Jamhuriyar Nijar, inda aka fuskanci ƙalubale kan noman Albasa a shekarar bana.
Bayanai daga ƙasar ta Nijar na cewa a halin da ake ciki, Manoma da dama sun shiga halin ƙaƙa-ni-kayi saboda rashin samun kuɗaɗen shiga, la'akari da irin rawar da noman na Albasa ke taka wa wajen sama musu abin kashewa.
Tue, 14 Apr 2026 - 289 - Yadda sare itace a Nijar ke haifar da koma baya wajen samun amfanin gona
Shirin, ‘Muhallinka Rayuwarka a wannan makon ya yi duba ne kan yadda ake samu canjin yanayi ta hanyar saran icen "Gawo" barkatai daga Makiyaya da su kansu Manoman, wanda ake ganin ke haifar da koma baya wajen samun yalawar abinci kamar, bakamar yadda aka saba ba a shekarun baya a cikin gonaki na Jamhuriyar Nijar.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson..........
Sat, 04 Apr 2026 - 288 - Hukumar NIMET ta yi hasashen samun saukar ruwa da wuri a daminar bana a Najeriya
Shirin ‘Muhalinka Rayuwarka’ a wannan makon ya yaɗa zango ne a Tarayyar Najeriya, inda ya mayar da hankali kan hasashen ruwan sama da Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya NIMET ta yi, gabanin kamawar daminar bana, inda ta bayyana cewa damina za ta sauka da wuri a jihohi irin su Kano da Niger da Rivers da wasu jihohi 12 na ƙasar.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson..............
Sat, 14 Mar 2026 - 287 - Yadda cutar tumatiri ta kasara manoma a wasu jihohin arewacin NajeriyaSat, 31 Jan 2026
- 286 - Dalilan da masana suka ce su ke ƙara bayyana sauyin yanayi
Shirin muhallinka rayuwarka na wannan makon ya tattauna ne kan yadda sauyin yanayi ko dai na zafi ko na sanyi ko kuma damina ke bayyana ƙarara, musamman a yankin yammacin Afirka. Ga misali a Najeriya, ɗaya daga cikin sauye-sauyen yanayin da aka shaida shi ne rashin hunturu a shekarar bana, musamman a Yankin arewacin ƙasar, inda aka saba ganin kankamar Yanayin na sanyin mai tsanani daga ƙarshen watan Nuwamba ko farkon Disamba zuwa ƙarshen watan Janairu ko farkon Fabarairu.
Gabanin fuskantar wannan lamari dai hatta yanayin damina da lokacin zuwanta ya sauya daga abinda aka saba da shi, batun da hatta a wasu wuraren da ke yankin Kudu maso yammacin Najeriya ma an shaida hakan.
Tuni dai wannan al’amari na sauyin lokutan yanayin zafi da damina ko kuma sanyi ya zama abin tattaunawa a tsakanin jama’a dangane da dalilan da suka janyo hakan, da dai wasu sauran tambayoyi da ake da ƙishirwar neman amsoshinsu.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare Nura Ado Suleiman............
Sun, 11 Jan 2026 - 285 - Noman rani na fuskanta barazana a Najeriya sabida tsadar kayan noma irinsu taki
Shirin, ‘Muhallinka Rayuwarka’ a wannan makon ya yaɗa zango ne Tarayyar Najeriya, inda ya duba irin barazanar da noman rani ke fuskanta, musamman a wannan lokaci da farashin kayyakin gona suka faɗi warwas a yayin da farashin taki da sauran mahimman kayakin da ake amfaani da su wajen noman suke a can ƙololuwa.
Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Michael Kuduson..........
Sat, 13 Dec 2025 - 284 - Yadda manoman Jamhuriyar Nijar ke fama da ɓarnar makiyaya a ƙarshen damina
Shirin muhallinka rayuwarka na wannan karon zai mayar da hankali ne kan irin fama da ake sha a karshen damina tsakanin manoman da suke tattarar Kayan gona da makiyayan dake dawowa daga kiwo zuwa wuraren da ake aikin noman a wasu sasaan Jamhuriyar Nijar.
A duk karshen damana makiyayan da suka tafi mashekari wurin kiwon dabbobinsu inda ke da isassar ciyawa nesa da gonaki na sabkowa wuraren da ake aikin noma don ganawa da jama'a, sannan da samun sauran tarikicen da manoman suka bari a gonakansu. Sai dai a irin lokacin na komawar makiyayan ana samun rikicin dake faruwa ' tsakaninsu da manoman da ba su ida tattare Kayan da suka noma ba, kuma da yanda wasu makiyayan ke saurin komowa a lokacin da manoman ke tsaka da aiki, duk da an tanadi dokar da ta tsaida komi a kasar ta Nijar.
Sat, 29 Nov 2025
Podcasts ähnlich wie Muhallinka Rayuwarka
Al-Quran Al-kareem Al-Quran Al-kareem
dakwah.me - Ustadz Adi Hidayat dakwahme
KH ANWAR ZAHID OFFICIAL Dakwah NU
Bagong Ndagel Dhiyon Daimonos
Ngaji Bareng Gus Baha Gus Baha
Kumpulan Ceramah Agama Islam IWAN
K.H. ZAINUDDIN MZ K.H. ZAINUDDIN MZ
Ludruk Cak Kartolo dkk Ludrukan
Bodor Sunda Mang Udin
Seni Sunda Wayang Golek Mohamad Rohmat
Murottal Qur'an Terjemahan Audio Indonesia Muslim
Pengajian KH Anwar Zahid Pengajian KH Anwar Zahid
Kumpulan Dakwah Sunnah PodcastSunnah
Wayang Kulit Indonesia Raden Ontoseno
Radio Rodja 756 AM Radio Rodja 756AM
Murotal Metode Ummi Rumah Digital Education (sutego)
Wayang golek SI CEPOT
Spesial Horor Spesial Horor
Sinau Bareng Cak Nun Telat Cerdas
Ustad Das'ad Latif Ustad Das'ad Latif
Al Quran dan Terjemahan wahyu hanan
Ludruk Jawa Timur Yohan Arie Chandra
Kajian Islami Bersama Ustad Abdul Somad Yuda Prawira
Quran Indonesian القرآن الكريم
