Filtra per genere

Muhallinka Rayuwarka

Muhallinka Rayuwarka

RFI Hausa

Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).

309 - Yadda matsalar tsuntsayen Jan Baki ta addabi manoma a jihar Jigawa
0:00 / 0:00
1x
  • 309 - Yadda matsalar tsuntsayen Jan Baki ta addabi manoma a jihar Jigawa

    Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan mako ya yi duba ne kan matsalar tsuntsayen jan baki da ke lalata gona komai girmanta a duk lokacin da suka durfafeta a jihar Jigawa da ke Arewacin Najeriya, wadda ta yi ƙamarin da har wasu manoma na cewa, dabarun da suka daɗe suna amfani da su wajen korar tsuntsayen sun kasa magance matsalar, lamarin da ya tilasta musu neman wasu sabbin hanyoyi.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nasiru Sani...........

    Sat, 03 Oct 2026
  • 308 - Hukumar NIMET a Najeriya ta yi hasashen yiwuwar ambaliya a jihoh 13 na ƙasar

    A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan duba sabon hasashen da Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya ta yi, game da yiyuwar samun matsalar ambaliyar ruwa a wasu jihohi 13 na kasar a wannan damunar.

    A baya-bayan nan, hukumar hasashen yanayi ta Nigeria wato NIMET, ta sake fito da wani sabon hasashen yiyuwar ambaliyar ruwa a cikin watan Agustan wannan shekara, tsakanin ranar 11 zuwa 20 ga watan na Agusta, a wasu jihohi 13 na kasar.

    Cikin sanarwar da ta bayar, hukumar ta NIMET, ta bayyana cewa hasashen nata, ya dogara ne kan adadin ruwan saman da ake fatan samu, da yanayin kasa tare da girman magudanan ruwa da kuma yawaitar madatsun ruwa.

    Sat, 26 Sep 2026
  • 307 - Matsalar ambaliyar ruwa da ake samu duk lokacin damina a ƙasashen Afrika

    Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan mako ya yi duba ne kan matsalar ambaliyar ruwa da ake fuskanta kowace shekara lokacin damina a sassan ƙasashen Afrika.

    Kamar kowace shekara, a bana ma ana hasashen samun ambaliyar ruwa a wasu kasashen yammacin Afrika, inda akan samu rasa rayuka da dukiya mai tarin yawa. A Najeriya, an sha samun hasarar rayuka a sanadin matsalar ambaliyar ruwan, da kan rutsa da wasu yankunan kasar.

    Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

    Sat, 19 Sep 2026
  • 306 - Alfanun gandun daji wajen baiwa muhallin ɗan Adam kariya daga gurɓacewa

    Shirin Muhallinka Rayuwarka tare da Nasiru Sani a wannan mako ya mayar da hankali ne kan gudunmawar Gandun daji ga ci gaban Muhalli a wani yanayi da duniya ke ganin ta'azzarar matsaloln da ke illa ga muhalli walau na kai tsaye ko kuma wanda ɗan adam kan haddasa. 

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    Sat, 12 Sep 2026
  • 304 - Ƙarancin yashin gini na haddasa rikici tsakanin jama'a da illa ga muhalli

    A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan yadda aikin gine gine ke haddasa bukatar yashi wanda nemanshi ke zama matsala tsakanin jama'a, da kuma illa ga muhalli da wurin noma da hanyoyin ruwa da sauransu.

    Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

    Sat, 15 Aug 2026
Mostra altri episodi

Altri podcast di Notizie e Politica