Filtrar por gênero
- 225 - Matsalar yoyon iskar gas yayi sanadiyyar gurbacewar ruwan sha yankin Delta
Shirin na wannan mako zai yi dubi ne akan yadda al'ummar karamar hukumar Obagi na jihar RIVERS dake yankin NIGER DELTA tarayyar Najeriya suke fama da matsalar yoyon iskar gas sanadiyar fashewar bututun da aka samu tun a watan Yunin shekarar 2023 wanda yayi sanadiyyar gurbacewar ruwan sha, wanda ya sa al'ummar ke kamuwa da cutar amai da gudawa har zuwa wannan lokaci.
Sat, 04 May 2024 - 224 - Matakan da gwamnatin Najeriya ke dauka don magance matsalar tsuntsaye a gonakiSat, 20 Apr 2024
- 223 - Yadda tsananin zafi ya ci karo da lokacin azumin watan Ramadana
Shirin a wannan mako zai ba da hankali ne akan tsananin zafin da ake fama da shi a wasu yankuna na Nahiyar Afirka, a wannan shekarar ya tsananta inda a wasu sassa na tarayyar Najeriya lamarin ya dan wuce misali.
Jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya, jiha ce da tun asali aka sani da tsanantar kowane juyin yanayi na Zafi ko na Sanyin Hunturu ko ma na yawan saukar Ruwan sama.
Sai a latsa alamar sauti domin sauraron shirin.
Sun, 07 Apr 2024 - 222 - Kaddamar da shirin inganta harkokin noma a jihar Niger
Shirin na wanna makon zai yi dubi ne akan katafaren shirin zamanantar da aikin noma da gwamnatin jihar Nejan Najeriya ta kaddamar. Masana na ganin Jihar a matsayin wadda idan aka tattala kasar noma da take da ita, a cikinta kadai za a iya noma abincin da zai iya ciyar da kasar har ma a iya fitarwa zuwa kasashen ketare.
A wannan aikin da aka kaddamar, gwamnatin jihar ta ce ta samar da kayan aikin fasahar noma na zamani tare da tanadar da dabarun noma daga kwararru.
Ku latsa alamar sauti dn sauraron cikakken shirin tare da Nasiru Sani.......
Sun, 31 Mar 2024 - 221 - Najeriya ta kasance kan gaba a fagen noman masara a yankin yammacin Afrika
Shirin wannan mako zai ba da hankali ne a kan yadda Najeriya ta kasance akan gaba a fagen noman masara a daukacin yankin yammacin Afrika, inda kasar ke samar da sama da kashi 48 na masarar da ake nomawa a yankin.
Mafi yawan masarar da ake nomawa a kasar, na fitowa ne daga yankin arewacin kasar, musamman jihohin Bauchi, Kaduna, Borno, Naija da Taraba da kuma wasu ‘yan kalilan din jihohin kudu maso yammacin kasar.
Sat, 23 Mar 2024 - 220 - Shiri na musamman kan yadda bangaren noma ya fuskanci matsaloli a Najeriya
Shirin "Muhallinka Rayuwarka" a wannan mako na musamman ne, domin kuwa ya yi dubi ne a kan matsaloli da dama suka addabi bangaren noma a Najeriya, wanda ake ganin su suka hana kasar samarwa kanta abincin da zai wadata jama'arta musamman a wannan lokaci da ake fuskantar tsadar sa a kasuwanni.
Shirin na dauke da rahotanni da kuma hirarraki daga sassa dagan daban na kasar.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nasiruddeen Muhammad.....
Sat, 16 Mar 2024 - 219 - Yadda wasu suka rungumi sana'ar kiwon Dodon kodi a yankin Naja Delta
Shirin mu na wannan mako zai yi duba ne a kan batun yadda wasu suka rungumi sana'ar kiwon Dodon kodi a yankin Naja Delta da ke tarayyar Najeriya musamman a jahar Cross River.
Wakilin mu dake yankin MURTALA ADAMU ya kai ziyara a wa ta Gona da ake wannan kiwon kuma ya zanta da wadanda suke sana'ar, wa ta da ta rungumi sana'ar ta yi bayani dalla dalla yadda ake fara tsara kiwon da kuma abubuwa da suka dace a tanada.
Sat, 24 Feb 2024 - 218 - Halin da yankunan da suka gamu da iftila’in ambaliya ke ciki a Najeriya
Shirin awannan mako zai maida hankali ne kan batun halin da yankunan da suka gamu da iftila’in ambaliya ke ciki a Najeriya, tare da duba matakan da suke dauka na kare kai anan gaba.
Idan ba a manta ba dai Shekara guda kenan da faruwa mummunar ambiyar ruwa a wasu jihohin Najeriya, kuma jihar jigawa dake arewacin kasar na cikin jihohin da ambaliyar tayiwa barna
Sat, 10 Feb 2024 - 217 - Gwamnatin Najeriya ta kudiri aniyar amfani da noman alkama don samar da aikin yi
A wannan mako shirin zai yi dubi ne akan shirin gwamnatin Najeriya na bunkasa noman alkama domin yaki da talauci da kuma wadata kasar da abinci.
A wani mataki na kawar da matsalar zaman kashe wando da magance rashin aikin yi musamman tsakanin matasa, gwamnatin Nigeria ta kuduri aniyar amfani da noma wajen samar da guraben aikin yi wa dubban matasan da basa da abin yi a fadin kasar.
Mon, 29 Jan 2024 - 216 - Hasarar da manoma suka samu a yayin girbin kayayyakin da suka noma a Najeriya
Hasarar da manoma suka samu a yayin girbin kayayyakin da suka noma a Najeriya wadda gwamnatin kasar tace yakan kai sama da Nera triliya 3 a kowacce shekara .
Sashen Hausa na Radio France International ya yi tattaki zuwa jihar Kano a Najeriya inda muka gana da masu ruwa da tsaki domin jin yadda ta kaya a wannan karowandada suka kuma bayyana cewa anfi samun asarar mafi girma akan kayan lambu amma hakan bai tsaya a bangare guda ba domin hatsi ma ba a barshi a baya ba
Sat, 20 Jan 2024 - 215 - Hukumar hasashen yanayin Najeriya ta ce za a fuskanci bahagon yanayi a kasar
Shirin wannan mako zai yi dubi ne yadda Hukumar da ke kula da harkokin hasashen yanayi ta Nigeria, ta yi hasashen samun wani gagarumin sauyin yanayi a yankunan arewa maso gabas da arewa ta tsakiya cikin ‘yan kwanaki masu zuwa. Bugu da kari hukumar, ta bayyana cewa shima yankin kudancin Nigeria zai shiga yanayi na zafin rana da wasu alamun hadari, kana yankunan da ke kusa da ruwa, za su shiga yanayi na hazo da ganin alamun hadari.
Jihohin kudancin Nigeria irin su Lagos, Delta, Rivers da Bayelsa, ana sa ran samun yanayin hadari da tsawa a wadannan kwanaki.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nasiru Sani ............
Mon, 15 Jan 2024 - 214 - Yadda manoman Najeriya suka tafka hasara a daminar bana
A yau wannan shiri zai ba da hankali ne akan batun hasarar da manoma suka samu a yayin girbin kayayyakin da suka noma a Najeriya wadda gwamnatin kasar tace yakan kai sama da Nera triliya 3 a kowacce shekara .
Sashen Hausa na Radio France International ya yi tattaki zuwa jihar Kano a Najeriya inda muka gana da masu ruwa da tsaki domin jin yadda ta kaya a wannan karo, Ado Hassan yakasai shine mataimakin sakatare janar na kungiyar manoman shinkafa ta kasa RiFAN, reshen jihar Kano ya kuma bayyana cewa anfi samun hasarar mafi girma akan kayan lambu amma hakan bai tsaya a bangare guda ba domin hatsi ma ba a barshi a baya ba.
Sun, 31 Dec 2023 - 213 - Koma bayan da manoman Najeriya suka samu a kakkar girbi na Shekara ta 2023
Shirin a wannan karo zaiyi dubi ne akan wasu bayanan kididdiga da suka yi nuni da cewa kakar noma ta shekara ta 2023, na daga cikin lokaci mafi muni ga mafi yawan manoman Nigeria a sakamakon matsalar sauyin yanayi da ta haifar da karancin ruwan sama.
A halin yanzu dai, wata babbar kungiyar kasa da kasa mai suna Action Aid, ta bayyana cewa irin hasarar da manoman Nigeria suka dibga a bana ta haura Nera Trilion 3, a daidai lokacin da ake fama da tsadar kayan abinci a kasar.
Sat, 18 Nov 2023 - 212 - Amurka da Norway za su tallafawa manoman Afirka da dala miliyan 70
Shirin "Muhallinka Rayuwarka" tare Nasiru Sani, a wannan mako ya yi dubi ne a kan gidauniyar kudade daya kai dalar amurka miliyan 70 da kasar Amurka da Norway zasu samar don inganta harkan noma a nahiyar Afrika.
Kasashen biyu sun sanar da hakan ne a garin New York na kasar Amurka inda sukace kowacce a cikin su zata bada dala miliyan talatin da biyar-biyar, inda kuma suka jaddada cewar yin hakan yazama wajibi ne sabo da barazanar yunwa da ke addabar wasu yankunan Afrika a sanadiyyar matsalolin tsaro ko sauyin yanayi.
Ku danna alamar sauti don sauraren cikakken shirin......
Sat, 04 Nov 2023 - 211 - Yadda aka horas da manoma dabarun yaki da matsalar dumamar yanayi a Najeriya
Shirin "Muhallinka Rayuwarka" tare Nasiru Sani, ya maida hankali ne kan yadda gwamnatin Najeriya karkashin ma'aikatar albarkatun ruwa da Bankin Raya Afrika suka horar da manoman karkara dabarun noma na zamani, wanda za su taimaka wurin yaki da dumamar yanayi da a yanzu duniya ke fama da shi wato Climate Change a turance.Wannan horo da aka baiwa wadannan matasa karkashin shirin na hadin gwiwa da ake kira da PIDACC, ba wannan shi ne karon farko da aka fara gudanarwa ba.
An dauki shekaru sama da goma ana yinsa a wasu kasashen Yammacin Afrika da zummar sauya rayuwar al'ummar kasashen da kogin Niger River Basin ya ratsa.
Ku danna alamar sauti don sauraren cikakken shirin......
Sat, 28 Oct 2023 - 210 - Yadda 'yan kasuwa ke sayen kayan abinci domin jiran kazamar riba
Shirin "Muhallinka Rayuwarka" tare Nasiru Sani, ya maida hankali ne kan yadda 'yan kasuwa a Tarayyar Najeriya musamman arewacin kasar, ke shiga kasuwanni da makudan kudi domin saye kayayyakin abinci, su kuma boye domin jiran lokacin da kayan za su yi tsada a kasuwanni kafin su fara fitowa da su da zummar samun kazamar riba, ba tare da la'akari da matsanancin hali da talakawan kasar ke fama da shi ba.
Ku danna alamar sauti don sauraren cikakken shirin wanda ya zanta da masu ruwa da tsaki......
Sat, 21 Oct 2023 - 209 - Yadda sauyin yanayi ke haddasa wutar daji da kafewar koguna sakamon tsananin zafi
Shirin Muhallinka rauwarka tare da Nasiru Sani ya mayar da hankali ne kan sauyin yanayi wanda ya haddasa tsananin zafin da yanzu haka ya addabi kasashe da dama musamman a yankunan Turai nahiyar Asiya da kuma Afrika wada tuni ya haddasa gagarumar illa ta hanyar kafar da tarin koguna a mabanbantan yankuna.
A bana kadai an ga tarin gobarar daji a kusan dukkanin nahiyoyin 3 wanda ya kone fadin kadada mai tarin yawa, lamarin da ke barazana ga harkokin noma da kiwo dama lalacewar kasar shuka.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin............
Sat, 07 Oct 2023 - 208 - Hasashen daukewar damuna da wuri na shirin haddasa matsala ga Manoman Najeriya
Shirin Muhallinka rayuwarka tare da Nasiru Sani a wannan mako ya mayar da hankali ne kan hasashen masana kan yiwuwar daukewar ruwan damuna da wuri a wasu sassan Najeriya, lamarin da zai haddasa gagarumar matsala a tsarin samar da abinci.
Wannan hasashe dai na zuwa ne a dai dai lokacin da hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin samun kamfar abinci a sassan Najeriya musamman jihohin arewaci wadanda su ne ke samar da abinci ga kusan daukacin jihohin kasar.
Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin............
Sat, 23 Sep 2023 - 207 - Tsadar taki ya haddasa koma baya a harkokin noma a Najeriya
Shirin 'Muhallinka Rayuwarka' na wannan mako zai yi duba ne kan batun matsalar takin zamani da manoma ke fama da shi a Najeriya shekara da shekaru, duk da cewa tsadar takin na bana ba irin wadanda aka saba gani a baya bane.
Matsalar tsadar taki dai a yanzu ita ce ta fi ci wa manoma tuwo a kwarya a Najeriya.
A latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nasiru Sani...
Sat, 16 Sep 2023 - 206 - Kamaru ta sako ruwan madatsar lagdo wanda ya janyo asarar kama daga rayuka da dukiyoyi
A yau shirin zai bada hankali ne akan sakin ruwan madatsar ruwan lagdo da kamaru zata yi, wanda yanzu haka mazauna wasu yankuna da ruwan zai kwaranya ta cikin su a Najeriya ke cikin tashin hankali dangane da irin asarar kama daga ta rayuka har ya zuwa ta dukiyoyi.
A karshe dai, gwamnatin Nigeria, ta tabbatar da cewa makwabciyarta Kamaru, ta sako ruwan da ke tumbatsa daga cikin madatsar ruwan Lagdo, lamarin da kan kasancewa babbar barazana ga dunbin al’ummomin Nigeria.
Sat, 09 Sep 2023 - 205 - Rawar da mata ke takawa a bangaren noma a NajeriyaSun, 20 Aug 2023
- 204 - Bankin raya Afirka na shirin tallafawa manoma a Najeriya
Shirin ya karkata ne akan wani shirin tallafawa manoma a Najeriya wanda Bankin raya Afirka ke tallafawa kan yadda za’a samu inganci da habakar samar da wadataccen abinci a fadin kasar wato agricultural transformation agenda support program karkashin ma’aikatar noma ta kasar wanda aka kaddamar a garin Bunkuren jihar Kano.
Sun, 13 Aug 2023 - 203 - Muhallinka Rayuwarka: Matakin gwamnatin Najeriya kan samar da abinciSat, 22 Jul 2023
- 202 - Matsalar zaizaiyar kasa na ciwa mazauna birnin Calabar tuwo a kwarya
Shirin "Muhallinka Rayuwarka" a wannan makon ya yi duba ne kan matsalolin zaizayar kasa, da ke samu a yankin Niger Delta da ke shiyar kudu maso kudancin Najeriya. Jahar Cross River na daya daga cikin jahohin da ke fama matsalar musamman a wani bangare na babban birnin ta Calabar.
Wannan matsalar dai ta haifar da asarar rayuka da kuma dukiya mai tarin yawa, musamman ga mazauna cikin kwaryar birnin.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nasiru Sani.......
Sat, 24 Jun 2023
Podcasts semelhantes a Muhallinka Rayuwarka
- Health Naturally with Denis Stewart 2NURFM
- ABC News Daily ABC
- Al-Quran Al-kareem Al-Quran Al-kareem
- Kumpulan Shalawat Andri Nugraha
- Ceramah Habib Novel Alaydrus Ceramah Habib -Novel Alaydrus
- CNN Indonesia CNN Indonesia
- KH ANWAR ZAHID OFFICIAL Dakwah NU
- Dakwah Tauhid Dakwah Tauhid
- Dzulqarnain Muhammad Sunusi Dzulqarnainms
- Firanda Andirja Official Firanda Andirja
- Ngaji Bareng Gus Baha Gus Baha
- Ps. Juan Mogi Juan Mogi Official
- K.H. ZAINUDDIN MZ K.H. ZAINUDDIN MZ
- Kumpulan Dakwah Islam Lentera Pagi
- Ludruk Cak Kartolo dkk Ludrukan
- Dongeng Sunda, Dongeng Enteng Mang Jaya Mang Jaya
- Murottal Qur'an Terjemahan Audio Indonesia Muslim
- Ngaji Gus Baha' Ngaji Gus Baha'
- Wayang Kulit Indonesia Raden Ontoseno
- Radio Rodja 756 AM Radio Rodja 756AM
- Squiz Today Squiz Media
- United Stand Podcast United Stand Podcast
- Ustad Das'ad Latif Ustad Das'ad Latif
- Misteri Seru Widya Yudha Utama
Outros Podcasts de Notícias e Política
- Les Grosses Têtes RTL
- Hondelatte Raconte - Christophe Hondelatte Europe 1
- Laurent Gerra RTL
- L'œil de Philippe Caverivière RTL
- C dans l'air France Télévisions
- Enquêtes criminelles RTL
- Bercoff dans tous ses états Sud Radio
- L’heure du crime : les archives de Jacques Pradel RTL
- Hondelatte Raconte - Cote B Europe 1
- Les récits de Stéphane Bern Europe 1
- Global News Podcast BBC World Service
- Lenglet-Co and You RTL
- Gaspard Proust - Les signatures d'Europe 1 Europe 1
- L'Heure des Pros CNEWS
- C ce soir France Télévisions
- LEGEND Guillaume Pley
- Les chroniques d'Arnaud Demanche RMC
- Apolline Matin RMC
- Face à Philippe de Villiers Europe1
- Pascal Praud et vous Europe 1