Filtrar por gênero
Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken kimiya da fasaha da ke neman saukakawa Dan’adam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Bil’Adama. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe, a ku maimata ranar Alhamis.
- 454 - Jigawa ta gabatar da tsarin rage barace-baracen Almajirai a jihar
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan daɗaɗɗen batun nan na yaran da basa zuwa makaranta a Najeriya matsalar da har kawo yanzu ta ƙi ci taki cinyewa.
Wani Rahoton UNICEF ya bayyana jihohin Kano da Jigawa da kuma Katsina a matsayin jihohin da ke da rinjayen yaren da basa zuwa Makaranta, inda a jumlace ƙasar ta yammacin Afrika ke da yara fiye da miliyan 18 da basa zuwa Makaranta, galibinsu a arewacin ƙasar.
Tuni Jihar Jigawa ta ɗaura ɗamarar yaƙi da wannan matsala, inda ta gabatar da wani sabon tsarin mayar da ɗimbin yara makarantu.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Tue, 29 Sep 2026 - 453 - Gwamnatin Kano na shirin tilasta koyar da ilimin Kwamfuta a makarantun Firamare da SakandareTue, 22 Sep 2026
- 452 - Gwamanatin Najeriya na shirin Horas da malamai sama da miliyan gudaTue, 15 Sep 2026
- 451 - Gudunmowa ko kuma illar da shafukan sada zumunta ke yiwa al'adun BahausheTue, 01 Sep 2026
- 450 - Yadda matasa suka ƙera jirgi maras matuƙi mai cin Kilomita 30 a Kano
Shirin a wannan makon ya leka Kanon Najeriya, inda aka gano wani sabon tarihin bunkasar kimiyya da fasaha da matasan yankin ke jagoranta.
Wannan gagarumar bajinta dai wani matashi Abubakar Waiya, wanda ya daɗe yana fafutukar kera na'urorin shawagi ne ya ƙera jirgi maras matuƙi domin taimakawa ɓangaren tsaro da kuma boma.
Jirgin da ya kera a yanzu yana da ikon tashi da kansa har na tsawon kilomita 30 ba tare da ya ɓace ba.
Wannan na'ura tana da aiyuka na musamman da aka tsara ta don yi, kamar feshin maganin ƙwari a gonaki na zamani da kuma kai magungunan gaggawa zuwa yankunan karkara da motoci ba su iya zuwa saboda rashin hanya.
Duk da wannan gagarumar nasara, babban ƙalubalen da ke gaban matasan shi ne tsarin dokoki na ƙasa.
Masu fafutuka na ganin cewa, idan har gwamnati da masu ruwa da tsaki suka ba wa waɗannan matasa dama da goyon baya, wannan ƙoƙari daga birnin Kano zai zama tushen samar da dabarun tsaro da aikin gona na zamani ga ɗaukacin yammacin Afirka.
Tambayar da ta rage anan ita ce: Shin gwamnati za ta tallafa wa wannan fasaha ta gida don ta bunkasa, ko kuwa za a zura ido ta ɓace ne?
Tue, 18 Aug 2026 - 449 - Makomar ilimin yara a Kano na cikin halin rashin tabbas
Shirin na wannan makon cigaba ne kan wanda muka gabatar a makon jiya, wanda ya gano yadda yara a wasu yankunan jihar Kano basa zuwa makaranta saboda yawon tallace-tallace domin tara kudin kayan ɗaki. Yayin da su kuma mazan suke diban yashi da fasa Dutse, da sunan wai su taso suna da sana'ar dogaro da kai.
Yankunan da wannan lamari yafi kamari sun hada da Challawa, Kafin Maiyaki, Madobi, Gora, da Kanwa. Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata mun kawo rahoton yadda wasu makarantu suka koma dandalin shaye-shaye a garin Meshumi dake karamar hukumar Ungogo.
Tue, 14 Jul 2026 - 448 - Yadda makomar ilimin yaran karkara a Najeriya ke cikin rashin tabbas
A wannan makon, shirin ya nufi yankunan karkara, inda inda gine-ginen makarantu ke ci gaba da kasancewa a matsayin kango, kasancewar babu dalibai.
A wasu wuraren kuma, azuzuwan sun zama fanko, yayin da matasa da yara suka ƙaurace wa shiga, ‘yan mata na fita birni yin tallace-tallace, su kuma samari na dambatawa da aikin ƙwadagon fasa duwatsu da ɗiban yashi.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da sabon rahoton hukumar UNICEF ya nuna cewa, jihohin Kano, Katsina, da Jigawa ne ke kan gaba a faɗin Najeriya wajen yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, inda a faɗin kasar kuwa, akwai yara sama da miliyan goma sha takwas da dubu ɗari uku da makoma ta iliminsu ke cikin haɗari.
Sau da yawa, wannan zargi na komawa ga gwamnati, sai dai abin tambayar shine, shin ko laifin na iyaye ne da al'umma, ko kuwa suma hukumomi akwai nasu kason?
Mun ziyarci garin Meshumi da ke karamar hukumar Ungoggo a jihar Kano, inda shirin ya tarar makarantar firamare na nan a gine, amma dakin karatu ya zama kufai.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin, tare da Shamsiyya Haruna
Wed, 08 Jul 2026 - 447 - Taron ƙaddamar da littafin tarihi na wani fitaccen matashi a Kanon Najeriya
Shirin na wannan mako ya mayar da hankali ne kan taron ƙaddamar da sabon littafin tarihin nan mai suna 'Mu San Magabata', wanda fitaccen matashin marubuci Kabiru Ahmad Kwalli ya rubuta da aka gudanar a jihar Kanon Najeriya.
Taron ya haɗa masana, sarakuna, da ɗandazon al'umma domin duba yadda za a ceto tarihin ƙasar Hausa da ke shirin bacewa.
Wannan littafi, kamar yadda masana da dama suka bayyana, ya zo ne a daidai lokacin da matasan yanzu ke ƙara nisanta da asalin tarihinsu.
To ko me ya sa mawallafin, Kabiru Ahmad Kwalli, ya ɗauki tsawon lokaci yana wannan bincike? Ga abinda ya shaida mana lokacin da muke zantawa da shi.
Tue, 30 Jun 2026 - 446 - Yadda aka gudanar da taron manyan masana na duniya a birnin Lagos
A wannan makon, shirin ya mayar da hankali ne kan babban taron ƙungiyar Lagos Studies Association karo na goma da aka kammala a ƙarshen mako, wanda ya saba haɗa masana, malaman jami'o'i, da masu bincike daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashen waje domin tattauna halin da ilimi yake ciki a nahiyar Afirka cikin wannan ƙarni.
Wannan taro, wanda aka kafa shi shekaru goma da suka gabata a birnin New York, an dawo da shi gida Afirka domin tattauna ainihin matsaloli da ci gaban nahiyar ke fuskanta, kuma a bana, fiye da rukunonin tattaunawa 340 ne aka shirya, inda aka haɗa masana daga sassan duniya.
Shekarar 2026 ta yi daidai da cikar kungiyar LSA shekaru 10 da kafuwa, inda aka gudanar da taron ƙarƙashin taken makomar ilimin nahiyar Afirka a wannan ƙarni.
Wani sashe mai muhimmanci a taron shi ne tattaunawa kan littafi na musamman mai suna 'Our Digital Lives and Indigenous Pathways', wanda masana suka duba yadda za a haɗa fasahar zamani da dabarun gargajiya na Afirka don samun ci gaba mai dorewa.
Baya ga tattaunawar kimiyya, taron ya haɗa da baje kolin fasaha na musamman mai taken 'Histories on Scissors: The Black Essence on the Map of Being' wanda Dominic James Aboi daga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria ya gabatar. An kuma tattauna makaloli kan addini da rashin addini a Arewacin Najeriya.
An dai gudanar da wannan taro ne domin nazarin al'adun zamani da na gargajiya, inda masana suka gabatar da maƙaloli kan tarihin Afirka, al'adu, da kafafen yaɗa labarai haɗi da baje kolin dabarun bincike na zamani.
A taron na bana, masana sun gano muhimman abubuwa da suka shafi makomar nahiyar Afirka ta fuskar ilimi, zamantakewa, da fasaha, kuma babban jigon da aka mayar da hankali akai shi ne yadda za a fassara binciken ilimi ya zama abin da zai amfani rayuwar al'umma kai-tsaye.
Haka zalika an gano cewa ko da yake yawan binciken da masana da ke zaune a cikin Afirka ke fitarwa ya ƙaru sosai, amma ingancinsa da kuma bayyanarsa a manyan jaridun ilimi na duniya ya ragu sosai.
Tue, 23 Jun 2026 - 445 - Yadda talauci ke hana ɗalibai cikar burinsuTue, 09 Jun 2026
- 444 - Shirin kawar da matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta na samun nasara a Jigawa
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan makon ya sake waiwayar matsalar nan ce ta yawaitar yaran da ba za zuwa makaranta a arewacin Najeriya, batun da a fannin ilimi ke ci wa al’ummar yankin tuwo a ƙwarya.
Masu iya magana dai na cewa ‘mai rai ba ya rasa motsi’ domin kuwa duk da girman da wannan matsala ta yi a Najeriya musamman ma yankin arewacin ƙasar, akwai waɗanda suka tashi tsaye wajen ganin sun kawo ƙarshen wannan ƙalubale, kuma har ma an fara samun sakamako kyakkyawa.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman................
Tue, 02 Jun 2026 - 443 - Ɗimbin matasa na haƙura da karatun boko saboda rashin tabbas kan samun aiki
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda matasa a baya-bayan na ke haƙura da ilimin boko saboda shakku kan yiwuwar samun aikin yi.
Matsalar rashin aikin yi bayan shafe tsawon shekaru ana karatu tare da kashe maƙuden kuɗaɗe ya sanya matasa da dama musamman waɗanda ba ƴaƴan wasu ba ajje tunanin karatu tare da mayar da hankali a kasuwanci da koyon sana'a saboda abin da suka kira rashin tabbas na cin moriyar karatun da suka yi.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Tue, 19 May 2026 - 442 - An yafe wa ɗaliban da ke son shiga kwalejin ilimi rubuta JAMB a Najeriya
A yau muna ɗauke da wani labari mai daɗi ga ɗaliban da ke sha’awar zama malamai da kuma masu son shiga Kwalejin Ilimi a faɗin Najeriya.
Gwamnatin ta fitar da wasu sabbin tsare-tsare da nufin sauƙaƙa wa ɗalibai hanyar neman ilimi da kuma ƙarfafa musu gwiwa ta fuskar kuɗi.
Ministan Ilimi Tunji Alausa, ya sanar da cewa ɗaliban da ke son shiga Kwalejin Ilimi yanzu ba sai sun rubuta jarrabawar UTME ba.
Amma dole ne ɗalibi ya kasance yana da aƙalla darussa biyar a sakamakonsa na sakandare. Duk da cewa ɗalibi ba zai rubuta jarrabawa ba, dole ne ya yi rajista da hukumar JAMB don tantance takardunsa domin samun gurbin karatu ta tsarin CAPS.
Bayan rage wa ɗalibai wahalar jarrabawa, gwamnatin ta kuma samar da tallafin karatu domin jawo hankalin kwararru zuwa fannin koyarwa. inda ta amince da biyan ɗaliban da ke karatu a kwalejojin ilimi na gwamnati alawus din naira naira 50,000 a kowane zango, waɗanda ke karatun digiri a fannin ilimi a jami’o’in gwamnati za su samu naira naira 75,000
Masana a fannin ilimi dai na ganin cewa, wannan wata babbar dama ce ga iyaye da ɗalibai da ya kamata su yi amfani da ita don sauƙaƙa wa kansu nauyin kuɗi da kuma samun gurbin karatu cikin sauƙi.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shrin
Tue, 12 May 2026 - 441 - Tasirin fasahar zamani wajen bunƙasuwar aikin jarida
Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali ne kan bikin ranar ƴancin ƴan Jaridu ta duniya da ke gudana a kowacce ranar 3 ga watan Mayu, bikin da ke zuwa a wannan karon cikin wani yanayi da aikin na Jarida ke ganin koma baya.
Akwai dai ƙorafe-ƙorafe daga sassa daban-daban kan yadda aikin na Jarida ke fuskantar barazana kodayake masu ruwa da tsaki a wannan fanni sun ce yanayin yaɗa labaran ya samu ci gaba da matuƙa ta sakamakon yaɗuwar fasahar zamani.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Tue, 05 May 2026 - 440 - Yadda makarantun tsangaya suka fara gauraya karatun addini da na Boko don tafiya da zamani
Shirin Ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda makarantun tsangaya da na Islamiyya suka fara gauraya karatun addini da na zamani a ƙoƙarin da suke yi na tafiya da zamani da kuma amun tallafi daga gwamnatoci da manyan ƙungiyoyi na duniya.
Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.
Tue, 28 Apr 2026 - 439 - Yadda mata a arewacin Najeriya ke yaƙi da jahilci don tallafawa ilimin ƴaƴansu - kashi na 2
Shirin Ilimi Haske Rayuwa na wannan makon ci gaba ne kan yadda wasu daga cikin iyaye mata ke fafutukar neman ilimi a Kano, duba da yadda a wasu makarantu ake tambayar matakin karatunsu kafin ɗaukar yaran su a matsayin ɗalibai. Mafi yawan iyaye lamarin baya musu daɗi, wasu na zargin ƙin ɗaukar yaran, sai dai hanzarin shine sanin irin kulawar da ya kamata makarantun su baiwa yaran ne yasa suke tambayar.
Ku latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna..............
Wed, 22 Apr 2026 - 438 - Yadda mata a arewacin Najeriya ke yaƙi da jahilci don tallafawa ilimin ƴaƴansu - kashi na 2
Shirin Ilimi Haske Rayuwa na wannan makon ci gaba ne kan yadda wasu daga cikin iyaye mata ke fafutukar neman ilimi a Kano, duba da yadda a wasu makarantu ake tambayar matakin karatunsu kafin ɗaukar yaran su a matsayin ɗalibai. Mafi yawan iyaye lamarin baya musu daɗi, wasu na zargin ƙin ɗaukar yaran, sai dai hanzarin shine sanin irin kulawar da ya kamata makarantun su baiwa yaran ne yasa suke tambayar.
Ku latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna..............
Tue, 21 Apr 2026 - 437 - Yadda mata a arewacin Najeriya ke yaƙi da jahilci don tallafawa ilimin ƴaƴansu
A arewacin Najeriya, shigar mata makarantun yaki da jahilci ya fara ne a matsayin wani yunkuri na inganta rayuwar iyali da kuma tarbiyyar yara, inda mata da dama sun fahimci cewa rashin ilimi na hana su taimaka wa yaransu wajen karatunsu na zamani da kuma kulawa da lafiyarsu.
Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.
Tue, 14 Apr 2026 - 436 - Wani matashi ya yi nasarar ƙera jirgi marar matuƙi a jihar Kano
Shirin Ilimi Haske Rayuwa na wannan makon, ya yi dubi ne kan yadda wani matashi a jihar Kanon Najeriya ya ja hankalin jama’a, bayan ƙirƙirar jirgi maras matuƙi, daidai lokacin da matasan wannan ƙasa ke faɗi tashin yadda za su samo masu ɗaukar nauyin ayyukan fasahar da suke son cimmawa.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruwa...........
Tue, 07 Apr 2026 - 435 - Yadda wasannin na'ura kwamfita ke samun karɓuwa a tsakanin matasaTue, 31 Mar 2026
- 434 - Tasirin faɗowar wasu sinadarai daga sama a fagen kimiyya da fasaha
Shirin "Ilimi Hasken Rayuwa" na wannan mako tare da Shamsiyya Haruna ya yada zango ne a Jamhuriyar Nijar inda abaya-bayan nan aka rika samun fadowar wasu abubuwa daga sararin samaniya, lamarin da ke ci gaba da faruwa a sassan a kasar.
A baya bayan ne dai wasu abubuwa suka fado daga sararin samaniya a kauyuka 5 daban daban a yankin Kornaka, da Dakwaro da suka hada da Dan Madi, Baushi, da sauransu, haka abin ya taba kasancewa a 2021 inda aka samu wani babban dutse da ya fado daga sama a garin Aikawa na yankin Gazawa sannan, an samu wasu duwatsun a yankin Tanut, Agades da sauran yankunan Nijar.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...
Tue, 03 Mar 2026 - 433 - Ra'ayoyi sun banbanta kan amfani da fasahar AI wajen yin tiyata
Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako a wannan makon, ya mayar da hankali kan binciken da ya gano cewa shigar fasahar AI cikin fannin tiyata na haifar da wasu matsaloli masu kama da barazana ga rayuwar ɗan adam, kan haka ne ma muka zanta da masana a fannin kimiyya da kuma ɓangaren lafiya, inda muka jiyo ra’ayoyin mutane game da yadda wasu ke yarda AI ya duba lafiyarsu har ta kai ga tiyata a wasu lokutan.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna............
Tue, 24 Feb 2026 - 432 - Yadda satar jarabawa ke taka rawa wajen kassara ingancin ilimi a Najeriya
Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda satar jarabawa ke ƙoƙarin zama ruwan dare a makarantun sassan Najeriya, matsalar da ke ci gaba da illa ga ingancin ilimi a dukkan makarantu na ƙasar.
Akwai zarge-zargen da ke nuna cewa wasu daga cikin jami'an hukumomin da ke kula da shirya jarabawa a matakai daban-daban na taimakawa wannan mummunar ɗabi'a ta satar jarabawa ta hanyar fallasa amsoshin tambayoyin da ake shirin fitarwa ga ɗalibai.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Tue, 17 Feb 2026 - 431 - Yadda masu larurar ji ke fama da ƙalubalen karatu a NajeriyaTue, 10 Feb 2026
Podcasts semelhantes a Ilimi Hasken Rayuwa
El Partidazo de COPE COPE
Herrera en COPE COPE
La Linterna COPE
Dante Gebel Live Dante Gebel
Es la Mañana de Federico esRadio
La noche de Cuesta esRadio
La Trinchera de Llamas esRadio
Hondelatte Raconte Europe 1
Affaires sensibles France Inter
LEGEND Guillaume Pley
El colegio invisible OndaCero
La Rosa de los Vientos OndaCero
Les grands dossiers de l'Histoire par Franck Ferrand Radio Classique
Espacio en blanco Radio Nacional
Enquêtes criminelles RTL
Entrez dans l'Histoire RTL
Le grand récit RTL
Les Grosses Têtes RTL
L'Heure Du Crime RTL
Parlons-nous RTL
El Larguero SER Podcast
SER Historia SER Podcast
Todo Concostrina SER Podcast
Un Libro Una Hora SER Podcast
Outros Podcasts de Educação
Choses à Savoir - Culture générale Choses à Savoir
Learning English Conversations BBC Radio
Philosophie pour tous Le Précepteur
Learning Easy English BBC
BBC 随身英语 英文解忧杂货铺
Podcast Italiano | Learn Italian (Intermediate & Advanced) Podcast Italiano
Métamorphose, éveille ta conscience ! Anne Ghesquière
Quelle Histoire Présente Quelle Histoire
Learn Spanish | SpanishPod101.com SpanishPod101.com
الشيخ كشك Sheikh Kishk
6 Minute English BBC Radio
T'as qui en Histoire ? Stéphane Genêt
Parler anglais Choses à Savoir
DianaUribe.fm Diana Uribe
Choses à Savoir ÉCONOMIE Choses à Savoir
Wissen mit Johnny Johnny
NéphrOdio CUEN
Easy German: Learn German with native speakers | Deutsch lernen mit Muttersprachlern Cari, Manuel und das Team von Easy German
Easy French: Learn French through authentic conversations | Conversations authentiques pour apprendre le français Hélène & Judith
Garde ta Joie Verrocchio Leandro
