Filtrar por género

Ilimi Hasken Rayuwa

Ilimi Hasken Rayuwa

RFI Hausa

Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken kimiya da fasaha da ke neman saukakawa Dan’adam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Bil’Adama. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe, a ku maimata ranar Alhamis.

462 - Yadda ƙungiyoyi masu zaman kansu ke baiwa ilimi tallafi a arewacin Najeriya
0:00 / 0:00
1x
  • 462 - Yadda ƙungiyoyi masu zaman kansu ke baiwa ilimi tallafi a arewacin Najeriya

    Shirin wannan mako ya duba yadda ake cigaba da ƙoƙartawa ne wajen samar da tallafin karatu ta hannun ƙungiyoyi da kuma Gidauniyar da ake kafawa a wurare daban daban a yankin Arewacin Najeriya.

    Ga misali a waccan makon da ya gabata, gidauniyar Muktariyya da ke jihar Kano ta yaye ɗalibai kusan dubu 2000, waɗanda aka ilimantar a fannonin na’ura mai ƙwaƙalwa da kuma aikin Jarida bayan da suka kammala ɗaukar horon neman ƙwarewa kyauta tsawon shekara guda.

    Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nura Ado Sulaiman.

    Tue, 17 Nov 2026
  • 461 - Yadda ake cigaba da samun tallafin karatu daga ƙungiyoyi a arewacin Najeriya

    Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan mako ya duba yadda ake cigaba da ƙoƙartawa ne wajen samar da tallafin karatu ta hannun ƙungiyoyi da kuma Gidauniyar da ake kafawa a wurare daban daban a yankin Arewacin Najeriya. Ga misali a waccan makon da ya gabata, gidauniyar Muktariyya da ke jihar Kano ta yaye ɗalibai kusan dubu 2000, waɗanda aka ilimantar a fannonin na’ura mai ƙwaƙalwa da kuma aikin Jarida bayan da suka kammala ɗaukar horon neman ƙwarewa kyauta tsawon shekara guda.

    Tue, 17 Nov 2026
  • 460 - Yadda maye gurbin makaranta da yawon talla ke kassara rayuwar mata a Najeriya

    Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali, ya yi duba ne kan makomar da yarinya mace ke da ita idan aka hanata taɓa alƙalami, aka kuma bata kwanon tallace-tallace a yankunan karkara, yayin da a dai dai wannan lokaci da ake fuskantar matsin tattalin arziki, fargabar tsaro da wasu tsoffin al'adun gargajiya na ci gaba da raba 'yan mata samun damar shiga ajujuwan karatu, musamman a Arewacin Najeriya da yankin tafkin Chadi.

    Shin wace rawa muryoyin dake cikin al'umma za su taka wajen ceto goben yarinya mace? Cikin mintuna goma na wannan shiri na musamman, za mu ji muryoyin da ke fuskantar wannan kalubale da kuma masu neman mafita.

    Mu fara da duba ainihin abin da ke faruwa a cikin makarantun karkara, inda karancin dalibai mata ke dada fitowa fili musamman idan sun fita daga firamare sun shiga sakandare.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    Tue, 10 Nov 2026
  • 459 - Yaɗuwar fasahar AI a harkar koyo da koyarwa

    A wannan makon, shirin namu ya yi duba ne ga guguwar fasahar zamani ta Artificial Intelligence ko kuma AI, da kuma yadda take sauya fasalin yadda ake koyo da koyarwa a makarantunmu. Ko wace makoma ce ke jiran azuzuwanmu na gaba a daidai lokacin da dalibai suka rungumi amfani da manhajoji irin su ChatGPT da Google Gemini?

    Gudunmowa ko kuma illar da fasahar AI ke da ita ga dalibai na ci gaba da daukar hankalin masana. A yayin da wasu ke kallon ta a matsayin wata babbar dama ta samun ilimi cikin sauki, wasu kuwa na fargabar cewa za ta sanya dalibai lalaci ko kuma ta maye gurbin malamai gaba daya.

    Tue, 03 Nov 2026
  • 458 - Matakin sallamar shugabannin makarantu sama da ɗari 4 a Nijar ya haifar da cece-kuce

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya maida hankali ne kan matakin sallamar shugabannin makarantu sama da ɗari 4 da gwamnatin Nijar tayi, bayan da ɗaliban makarantun da suke jagoranta na firamari da kuma sakandare suka gaza samun makin da ake buƙata, lamarin da ya sanya ɗiga ayar tambaya kan ko wannan mataki zai haifar da ɗa mai ido ga ɓangaren ilimin ƙasar.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Shamsiyya Haruna............

    Tue, 27 Oct 2026
Mostrar más episodios