Filtrar por género
- 409 - Dalilin da ya sanya aka fara haramta sana'ar jari bola a wasu sassan Najeriya
Sana’ar tattara wa da sayar da tsofaffin ƙarafa da sauran tarkace wadda aka fi sani da ‘Bola Jari’ na daga cikin sana’o’i da dubban mutane masamman matasa ke dogaro da su a Najeriya.
Amma a cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan, sana’ar ta fuskanci babban ƙalubale, musamman saboda zargin cewa wasu masu tattara ƙarafa na amfani da ita wajen sayar da kayayyakin da aka sace daga tituna, gadoji, layin dogo da sauran muhimman abubuwan more rayuwa.
Wannan ne ya sa wasu gwamnatocin jihohi suka ɗauki matakin dakatarwa ko haramta sana’ar baki ɗaya.
Yanzu haka Ƙungiyar masu sana’ar ta jari bola ta yi barazanar tsunduma yajin aikin gargaɗi, ta hanyar dakatar da lodi ko sayar wa kamfanoni baraguzai da suke tattarawa.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
Wed, 30 Sep 2026 - 408 - Matatar matatar Ɗangote ta ƙaddamar da sayar da hannayen jarinta a hukumance
Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon ya maida hankali ne kan ƙaddamar da shiga matatar Ɗangote kasuwannin hannayen jarin Najeriya, a wani biki da aka gudanar a babban shelkwatan kasuwannin hannayen jarin Najeriya da ke Marina a birnin Legas, inda shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko da kansa ya kaɗa ƙararrawar buɗe shigar matatar a hukumance.
Matatar ta sanya hannun jari biliyan 4 da miliyan 100 kasuwa, kan Naira 525 ga kowane guda, inda take fatan tara kusan Naira tiriliyan 2 da biliyan 150.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba..............
Wed, 16 Sep 2026 - 407 - Tasirin da saida hannun jarin matatar man Dangote ke da shi ga al'umma
Shirin kasuwa akai miki dole na wannan lokacin, ya maida hankali ne kan yadda matatar Dangote ta shirya buɗe ƙofifinta ga al’umma domin su mallaki wani kaso a matatar mafi girma a Afirka, bayan da a karon farko ta sanar da shiga kasuwar hannayen jari.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba...........
Wed, 09 Sep 2026 - 406 - Sharhi kan kalaman Alhaji Atiku na maido da tallafin mai a Najeriya
Shirin ‘kasuwa akai miki dole’ a wannan mako tattauna ne kan wasu batutuwa da suka taso masu nasaba da siyasa da tattalin arziƙi a Najeriya, Inda muhawara ta kaure kan batun tallafin man fetur, bayan da ɗan takarar shugabancin ƙasar na jam’iyyar adawa ta ADC Alhaji Atiku Abubakar ya yi alƙawarini maido da tallafin man idan aka zaɓe shi a 2027, to amma nan da nan gwamnatin Najeriyar ta mayar da martani.
Kalaman Atiku, sun tayar da kura tare da ƙara zafafa lamura a fannin siyasa da tattalin arzikin ƙasar, inda a ƙarshe, shugaba Bola Ahmed Tinubu, da kansa, ya fito ya soki lamarin.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmad Abba...............
Wed, 02 Sep 2026 - 405 - Ghana ta zama ƙasa ta 6 a cikin jerin ƙasashen da ke samar da zinari a duniya
Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon ya maida hankali ne kan yadda Ghana ta zama ta shida a cikin manyan ƙasashe da suka fi samar da zinare a duniya, bayan zarce Amurka a alƙaluman yawan zinare da ƙasar ta yammacin Afirka ta hako a shekarar 2025 da ta gaba. To, amma menene tasirin kasancewar ƙasar ta ɗaya daga cikin manyan masu samar da zinare a duniya ke nufi ga talakawan Ghana da kuma tattalin arzikin ƙasar?
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmad Abba............
Wed, 26 Aug 2026 - 404 - Me cigaban kasuwar hannayen jarin Najeriya ke nufi ga talakan ƙasar kashi na 2
Shirin 'Kasuwa a kai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya dora kan shirin makon da ya gabata, wanda ya mayar da hankali kan ci gaba da kasuwar hannayen jarin Najeriya ta samu, wajen zama ta ɗaya a duniya, kamar yadda mujallar Bloomberg ta sanar a ƙarshen watan Yulin wannan shekara ta 2026. To amma me cikin gaban kasuwar hannayen jarin ke nufi ga takan ƙasar?
Wed, 19 Aug 2026 - 403 - Cigaban kasuwar hannayen jari na nufin rayuwa ta fara inganta ga talakan Najeriya?
A ƙarshen watan Yulin wannan shekara ta 2026, mujalar Bloomberg da ke bibiyar harkokin tattalin arzikin ƙasashen duniya, ta bayyana kasuwar hannayen jarin Najeriya a matsayin ta ɗaya a duniya a fannin dala, wajen yi wa ta Koriya ta Kudu fintinƙau.
Masana tattalin arziki sun alakanta wannan gagarumin ci gaba da kasuwar ta samu da sauye-sauye masu tsauri da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi a fannin tattalin arziki.
Wed, 12 Aug 2026 - 402 - Ghana ta yiwa ƙasashen Afrika fintinkau a fannin ci gaban hada-hadar kuɗaɗe ta wayar hannuWed, 05 Aug 2026
- 401 - Illar cushen kusan naira tiriliyan 1 a kasafin kuɗin Najeriya ga tattalin arziƙi
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako, ya mayar da hankali ne kan yadda aka gano cushen kusan Naira triliyan ɗaya cikin kasafin kuɗin Najeriya na wannan shekarar ta 2026, domin sayen motocin alfarma da kuma ayyukan tallafa wa jama'a.
Wannan na ƙunshe ne cikin wani rahoton da wata cibiyar da ke sa’ido kan yadda gwamnati ke kashe kuɗaɗen kasafi a Najeriya wato Tracka.
Cibiyar ta ce adaɗin ya zarce jimillar kuɗin da aka ware wa manyan ma'aikatun gwamnatin tarayya guda bakwai. Batu da ya janyo ce-ce-ku-ce.
A cikin rahotonta, Cibiyar ta nuna cewa gwamnatin ta ware kusan Naira biliyan 960 ga ma'aikatun Sufurin Jiragen Sama, Gidaje, Harkokin Mata, Ciniki da Masana'antu, Shari'a, Kiwon Dabbobi da Albarkatun Man Fetur, amma kuma ta ware kusan Naira biliyan 963 domin sayen motoci da kuma ayyukan tallafa wa jama'a.
Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.
Wed, 29 Jul 2026 - 400 - Matakin matatar Ɗangote ya fusata ƙungiyar dillalan man fetur a Najeriya
Shirin a wannan mako tare da Ahmed Abba ya yi dubi ne kan matakin da ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu a Najeriya ta sanar na dakatar da sayen mai daga matatar Dangote, sakamakon matakin da matatar ta ɗauka na fara sayar musu da man da take tacewa da dala maimakon Naira.
Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......
Wed, 22 Jul 2026 - 399 - Rashin rassan bankuna ya tilastawa al'ummar karkara rungumar POS a NajeriyaWed, 08 Jul 2026
- 398 - Ana samun ƙaruwar cin bashin kuɗin kiran waya tsakanin jama'ar Najeriya
Shirin "Kasuwa Akai Miki Dole" na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda ƴan Najeriya suka rungumi ɗaukar bashin kiran waya, wanda wani rahoto ya ce, a bara kaɗai anci bashin kiran waya da ƙudinsu ya kai Naira Tiriliyan 4 da biliyan 61.
Wasu bayanai da cibiyar fintech firms Optasia mai tattara alƙaluman shige da ficen kuɗaɗen layukan sadarwa ta fitar a baya-bayan nan, ya nuna yadda ƴan Najeriya waɗanda ke amfani da wayar hannu, a kullum ke tururuwar ciwo bashin katin kira wanda ke ɗauke da kuɗin ruwa.
Rahoton cibiyar ya ce a shekarar 2025 kawai ƴan Najeriya sun ci bashin katin kiran waya da ya kai Dala biliyan 3 da miliyan 18 kwatankwacin Naira tiriliyan 4 da biliyan 61, abinda ke haskawa ƙarara cewa adadin ya ƙaru da kaso 12.3 cikin 100 idan an kwatanta da shekarar 2024, wadda ya kasance Naira tiriliyan 4 da biliyan 38.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Wed, 01 Jul 2026 - 397 - Yadda tattalin arzikin Ghana ke haɓɓaka sannu a hankaliWed, 17 Jun 2026
- 396 - Koken ƴan Najeriya kan yadda bankuna ke zare musu kuɗi daga asusun ajiyarsu
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya yi dubi ne kan yadda ƴan Najeriya, ke nuna fushinsu dangane da zargin cire musu kuɗi ba bisa ka’ida ba daga asusun bankunansu.
Miliyoyin 'yan Najeriya da yanzu haka ke fuskantar hauhawan farashin kayayyaki da kuɗin sufuri, da kuma rashin tabbas ga makomarsu a fannin tattalin arziki, caje-caje da dama da bankuna ke yi a asusun ajiyarsu na sake jifasu cikin damuwa.
A cikin 'yan watannin nan, koke-koke sun mamaye kafofin sada zumunta, sakamakon rashin karin bayani kan yawaitan kudaden da bankunan ke cirewa..
Duk da cewa bankuna sun dage cewa hakan tsari ne da kuma sahalewar haka daga babban bankin kasar CBN, kwastomi na diga ayar tambaya kan cirewa fiye sau ɗaya kan, ko kuma daga wanda ya tura da kuma wanda ya ƙarba, yayin da wasu ke kokawa kan rashin maida musu kudinsu nan take idan aka samu masalar sabis kudi bai je ga wanda aka tura ba da dai sauransu...
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Wed, 20 May 2026 - 395 - Yadda ƴan kasuwa a Najeriya suka jingine harakokinsu saboda tsadar sufuriWed, 13 May 2026
- 394 - Yadda tsadar sufuri ya tilastawa 'yan kasuwa jingine sana'o'insu a Najeriya
A yau shirin ya mayar da hankali ne kan yadda a Najeriya, 'Yan kasuwa da dama suka fara jingine harkokinsu saboda yadda tsadar sufuri ke cinye ribar da suke samu, wasu lokuta har da jarinsu .
Sannu a hankali, irin hada-hadar da aka saba gani tsakanin mafi yawan kasuwannin Nigeria na neman zama abun tarihi, sakamakon yadda ‘yan kasuwa masu tarin yawa suka jingine harkokinsu na kasuwanci saboda tsadar sufuri.
‘Yan kasuwa, na kukan samun wagegen gibi tsakanin uwar kudin jarinsu da abinda suke kashewa na safarar kayansu zuwa kasuwanni, saboda tsadar kudin sufuri da kuma rashin ciniki saboda halin rashin kudi da ‘yan kasar ke ciki.
Kasancewar kowane sasshen Nigeria na da nau’in kayayyakin da yake da su a wadace, ‘yan kasuwa daga arewacin kasar, kan saro kayayyaki irin su Manja da Man Gyada da Garin Kwaki da makamantan su, daga kudancin kasar, yayinda ‘yan kasuwa daga kudanci, kan sayi hatsi, dabbobi da makamantan su daga arewacin kasar.
Bayanan hukumar kididdiga ta Nigeria, sun yi nuni da cewa damar ikon sayen kayayyaki a kasuwanni wato purchasing power a turance, da ‘yan Nigeria ke da ita, ta ragu da kashi 21, a sakamakon tashin gwauron zabi da farashin kayayyakin suka yi, da koma-bayan kudin shigar masu karamin karfi a kasar.
Wed, 13 May 2026 - 393 - Damarmaki da kuma ƙalubalen da manoman Albasa a arewacin Kamaru ke fuskantaWed, 29 Apr 2026
- 392 - Matakan da bankin CBN ke ɗauka na sake fasalin tsarin harkokin kuɗi a Najeriya
Shirin Kasuwa akai miki doke na wannan mako ya yi duba ne kan matakan da babban bankin Najeriya CBN ke ɗauka na sake fasalin tsarin harkokin kuɗaɗe, domin rage hauhawan farashin kayayyaki a kasuwanni da kuma daga darajar kuɗin ƙasar wato Naira, ta hanyar rage kuɗaɗe da ke yawo a hannun jama’a.
Babban Bankin Nigeria, ya fito da bakin alƙalamin adadin kuɗaɗen da ke bankuna da waɗanda ake hada-hada da su a cikin ƙasa tare da waɗanda jama’a ke jujjuyawa a hannunsu.
Adadin wannan kudi dai a cewar bankin na CBN, ya kai Naira Triliyan 123 da biliyan 15, a watan Fabareiru, inda aka samu raguwar adadin madarar kuɗi da ke hannun jama’a akan na watan Janairu, wanda ya kai Nera Triliyan 123 da biliyan 36.
Haka ma adadin kudaden kasar a asusun ajiyarta na ketare ya ragu zuwa Nera Triliyan 28 da biliyan 41 daga Nera biliyan 29 da biliyan 61.
Ku latsa alamar sauti don sauti don sauraron cikkan shirin tare da Ahmad Abba.............
Wed, 22 Apr 2026 - 391 - Yadda matsalolin tsaro ke kassara kasuwanci a arewacin Najeriya
Shirin na wannan makon ya mayar da hankali ne kan irin fargabar da 'yan kasuwar arewacin Najeriya da ke fatauncin kayayyaki zuwa wasu sassan jihohi ke ciki, sakamakon ayyukan bata gari da ke tare hanya wanda a wasu lokuta kan kai ga rasa rayuka.
Abune da aka saba gani, ‘yan kasuwar dake hada Hada tsakankin jihohi daga wannan kasuwa zuwa waccan ko tsakanin kasuwannin kauyuka.
To sai dai Kuma irin wannan tsarin na fuskantar cikas ko koma baya, alal misali ga yan kasuwa a jihar filato dake arewacin Najeriya, sakamakon munanan halaye na wasu bata gari marasa tausayin rayuwar Dan Adam, dake tare Yan tireda ko Kuma matafiya inda suke Kai musu farmaki, tare da yi musu kisan gilla.
A kwanakin baya wasu Bata gari sun tare wasu Yan kasuwa da ke fatauci daga garin Jos zuwa yankin kudancin Jihar, inda suka kashe biyar daga cikinsu, Wannan al’amari ya Sanya Yan Kasuwar da sauran matafiya shiga hali na fargaba a kowane yanki dake jihar.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Wed, 08 Apr 2026 - 390 - Yadda matasa ke fatan cin gajiyar yarjejeniyar tattalin arziki tsakanin Nijar da AlgeriaWed, 01 Apr 2026
- 389 - Koma bayan da kasuwancin duniya ya fuskanta sakamakon rikicin Gabas Ta Tsakiya
Shirin "Kasuwa Akai Miki Dole" tare da Ahmed Abba a wannan mako ya ɗora ne kan inda ya tsaya a makon jiya, game da gagarumin koma baya a fannin kasuwanci da tattalin arziki da duniya ke fuskanta masamman a bangaren makamashi, sakamakon yaƙin da kawancen Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran, da kuma martinin jamhuriyar musuluncin kan Isra’ila da muradun Amurka a kasashen labarawa suka janyo.
A makon jiya, shirin ya tattauna wannan batu ne da malaman da muka gayyato, wato Dr. Aminu Idris Harbau masamanin tattalin arziki a tarayyar Najeriya, da Dr. Ibrahim Adamu na sashin nazarin yankin gabas ta Tsakiya a jami’ar Havard da ke Dubai na haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, sai Mohammad Qaddam Sidiq Isa, mai sharhi kan al’amuran Yau da Kullum shima a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, sai kuma Isma’il Albabawee ɗan jarida kuma ɗalibi a jami’ar Karbala a ƙasar Iraki.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Wed, 18 Mar 2026 - 388 - Yadda yaƙin Iran ya haifar da koma baya ga tattalin arzikin Duniya
A yau shirin Kasuwa A kai Miki Dole na wanan mako tare da Ahmad Abba ya mayar da hankali ne a kan yadda Yaƙin da kawancen Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran, da hare-haren mayar da martini na jamhuriyar musuluncin kan yahudun Isra’ila da muradun Amurka a kasashen labarawa suka janyo gagarumar koma baya a fannin kasuwanci da tattalin arzikin duniya masamman a bangaren makamashi.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin......
Wed, 11 Mar 2026 - 387 - Yadda aka gudanar da taron tattalin arzikin a Akwa IbomWed, 04 Mar 2026
- 386 - Najeriya da China sun yi bukin cika shekaru 55 da hulɗar diflomasiyya
Shirin 'Kasuwa a kai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan tasirin tattalin arziki dangane da alaƙar China da Najeriya da a makon jiya aka yi bikin cika shekaru 55 da faro hulɗar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.
Najeriya da China sun sake jaddada karfafa dangantakar diflomasiyya da ke tsakaninsu yayin da kasashen biyu ke bikin cika shekaru 55 da fara huldar diflomasiyya a bikin baje kolin sabuwar shekarar kalandar kasar China da aka gudanar.
Wed, 18 Feb 2026
Podcasts similares a Kasuwanci
Al-Quran Al-kareem Al-Quran Al-kareem
dakwah.me - Ustadz Adi Hidayat dakwahme
KH ANWAR ZAHID OFFICIAL Dakwah NU
Bagong Ndagel Dhiyon Daimonos
Ngaji Bareng Gus Baha Gus Baha
Kumpulan Ceramah Agama Islam IWAN
K.H. ZAINUDDIN MZ K.H. ZAINUDDIN MZ
Ludruk Cak Kartolo dkk Ludrukan
Bodor Sunda Mang Udin
Seni Sunda Wayang Golek Mohamad Rohmat
Murottal Qur'an Terjemahan Audio Indonesia Muslim
Pengajian KH Anwar Zahid Pengajian KH Anwar Zahid
Kumpulan Dakwah Sunnah PodcastSunnah
Wayang Kulit Indonesia Raden Ontoseno
Radio Rodja 756 AM Radio Rodja 756AM
Murotal Metode Ummi Rumah Digital Education (sutego)
Wayang golek SI CEPOT
Spesial Horor Spesial Horor
Sinau Bareng Cak Nun Telat Cerdas
Ustad Das'ad Latif Ustad Das'ad Latif
Al Quran dan Terjemahan wahyu hanan
Ludruk Jawa Timur Yohan Arie Chandra
Kajian Islami Bersama Ustad Abdul Somad Yuda Prawira
Quran Indonesian القرآن الكريم
Otros podcasts de Negocio
BFM Bourse BFM Business
C'est votre argent BFM Business
UNBX, le podcast de la réussite UNBX
Culture IA BFM Business
Les experts BFM Business
Entendez-vous l'éco ? France Culture
Choses à Savoir ÉCONOMIE Choses à Savoir
QR Podcast QR PODCAST
Freedom to be Happy Sukriti Vadhera Kohli
Sound Laws of Success Podcast James Karl Butler
Le marché de François-Régis Gaudry France Inter
Dubai Owen
Tanguy Pastureau maltraite l'info France Inter
La librairie de l'éco BFM Business
Grands Leaders, les leçons de l'Histoire Radio Classique
BFM Crypto BFM Business
Info éco FRANCE 24
مُلخص كتاب Podcast Record
Tout pour investir BFM Business
UNBX, le podcast de la réussite UNBX
