Filtra per genere

Kasuwanci

Kasuwanci

RFI Hausa

Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masana’antu dangane da halin da suke ciki.

409 - Dalilin da ya sanya aka fara haramta sana'ar jari bola a wasu sassan Najeriya
0:00 / 0:00
1x
  • 409 - Dalilin da ya sanya aka fara haramta sana'ar jari bola a wasu sassan Najeriya

    Sana’ar tattara wa da sayar da tsofaffin ƙarafa da sauran tarkace wadda aka fi sani da ‘Bola Jari’ na daga cikin sana’o’i da dubban mutane masamman matasa ke dogaro da su a Najeriya.

    Amma a cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan, sana’ar ta fuskanci babban ƙalubale, musamman saboda zargin cewa wasu masu tattara ƙarafa na amfani da ita wajen sayar da kayayyakin da aka sace daga tituna, gadoji, layin dogo da sauran muhimman abubuwan more rayuwa.

    Wannan ne ya sa wasu gwamnatocin jihohi suka ɗauki matakin dakatarwa ko haramta sana’ar baki ɗaya.

    Yanzu haka Ƙungiyar masu sana’ar ta jari bola ta yi barazanar tsunduma yajin aikin gargaɗi, ta hanyar dakatar da lodi ko sayar wa kamfanoni baraguzai da suke tattarawa.

    Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

    Wed, 30 Sep 2026
  • 408 - Matatar matatar Ɗangote ta ƙaddamar da sayar da hannayen jarinta a hukumance

    Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon ya maida hankali ne kan ƙaddamar da shiga matatar Ɗangote kasuwannin hannayen jarin Najeriya, a wani biki da aka gudanar a babban shelkwatan kasuwannin hannayen jarin Najeriya da ke Marina a birnin Legas, inda shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko da kansa ya kaɗa ƙararrawar buɗe shigar matatar a hukumance.

    Matatar ta sanya hannun jari biliyan 4 da miliyan 100 kasuwa, kan Naira 525 ga kowane guda, inda take fatan tara kusan Naira tiriliyan 2 da biliyan 150.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba..............

    Wed, 16 Sep 2026
  • 407 - Tasirin da saida hannun jarin matatar man Dangote ke da shi ga al'umma

    Shirin kasuwa akai miki dole na wannan lokacin, ya maida hankali ne kan yadda matatar Dangote ta shirya buɗe ƙofifinta ga al’umma domin su mallaki wani kaso a matatar mafi girma a Afirka, bayan da a karon farko ta sanar da shiga kasuwar hannayen jari.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba...........

    Wed, 09 Sep 2026
  • 406 - Sharhi kan kalaman Alhaji Atiku na maido da tallafin mai a Najeriya

    Shirin ‘kasuwa akai miki dole’ a wannan mako tattauna ne kan wasu batutuwa da suka taso masu nasaba da siyasa da tattalin arziƙi a Najeriya, Inda muhawara ta kaure kan batun tallafin man fetur, bayan da  ɗan takarar shugabancin ƙasar na jam’iyyar adawa ta ADC Alhaji Atiku Abubakar ya yi alƙawarini maido da tallafin man idan aka zaɓe shi a 2027, to amma nan da nan gwamnatin Najeriyar ta mayar da martani.

    Kalaman Atiku, sun tayar da kura tare da ƙara zafafa lamura a fannin siyasa da tattalin arzikin ƙasar, inda a ƙarshe, shugaba Bola Ahmed Tinubu, da kansa, ya fito ya soki lamarin.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmad Abba...............

    Wed, 02 Sep 2026
  • 405 - Ghana ta zama ƙasa ta 6 a cikin jerin ƙasashen da ke samar da zinari a duniya

    Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon ya maida hankali ne kan yadda Ghana ta zama ta shida a cikin manyan ƙasashe da suka fi samar da zinare a duniya, bayan zarce Amurka a alƙaluman yawan zinare da ƙasar ta yammacin Afirka ta hako a shekarar 2025 da ta gaba. To, amma menene tasirin kasancewar ƙasar ta ɗaya daga cikin manyan masu samar da zinare a duniya ke nufi ga talakawan Ghana da kuma tattalin arzikin ƙasar?

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmad Abba............

    Wed, 26 Aug 2026
Mostra altri episodi