Filtrer par genre
- 321 - Yadda wani kamfanin kasar Denmark ya shirya zuba jarin dala biliyan 6 a NajeriyaWed, 08 May 2024
- 320 - Dambarwar EFCC da wasu jiga-jigan tsohuwar gwamnatin Najeriya kan badakalar kudi
Shirin kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya mayar da hankali kan matakin hukumar da ke yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annti EFCC na kaddamar na farautar tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello da kuma binciken wasu tsoffin mukarraban gwamnatin da ta shude kan cin hanci da rasha da kuma rufta da ci da dukiyar al’umma.
A Najeriya, cikin ‘yan makonnin baya-bayan nan kusan za’a iya cewa hankulan al’ummar ƙasar sun karkata ne kan matakan da hukumar EFCC ke dauka kan wasu tsaffin jjiga-jigan gwamnatin da ta gabata, inda hukumar ta tsare kuma take shirin gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen saman ƙasar ƙarkashin tsohon shugaban ƙasa Mohammdu Buhari, wato Hadi Sirika, bisa zargin almundahana na ƙudi da suka kai sama da naira biliyan takwas.
Yayin da a bangare guda, aka shiga wasan buya da cece-kuce tsakanin tsohon gwamnan jihar Kogi Alhaji Yahaya Bello da ke cewa abi umurnin kotu kan shirin kamashi yayinda shugaban hukumar ta EFCC ke cewa tabbas zai yi murabus muddun tsohon gwamnan bai gurfana don amsan laifin almundahanan sama da naira biliyan tamanin ba.
Wadannan da wasu batutuwa da suka shafi tattalin arzikin Najeriya na kunshe a cikin wannan shiri, ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Wed, 01 May 2024 - 319 - Koken 'yan Najeriya na rashin saukar farashin kayan masarufi duk da faduwar Dala
Shirin Kasuwa A Kai Miki Dole a wannan makon ya maida hankali ne kan batun korafin ‘yan Najeriya ke yi game da rashin ganin sauyi a farashin kayan amfanin yau da kullum, bayan karyewar farashin ƙudaden ƙetare masamman dalar Amurka da sanadin tashin ta ne ya haddasa mummunan tashin farashin kayayyaki a kasar, wanda har hukumar ƙididdiga ta ƙasar ta ce lamaarin ya yi muni.
Ko da ya ke a wasu manyan biranen Najeriya irinsu Legas da Abuja, an fara ganin sauƙi a wasu kayayyakin abinci irinsu shinkafa da man girki da dai sauransu.
Ku latsala alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba........
Wed, 24 Apr 2024 - 318 - Yadda matasa suka rungumi kananan sana’o’i lokacin azumin Ramadana a Damagaram
Shirin Kasuwa a Kai Miki Dole a wannan makon ya maida hankali ne kan kananan sana’o’i da matasa ke yi don samun na abinci a lokacin azumin watan Ramadana a Damagaram da ke jamhuriyar Nijar. wasu daga cikin sana'oin da matasan sukafi mai da hankali akai dai sun hada da bredi ko kayan marmari ko kayan lambu da dai sauransu.
Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Ahmed Abba.......
Wed, 03 Apr 2024 - 317 - Gidauniyar Dangote ta kashe naira biliyan 15 na tallafin abinci a Najeriya
Shirin Kasuwa A Kai Miki Dole a wannan makon ya maida hankali ne kan rabon tallafin abincin naira biliyan 15, da Gidauniyar Aliko Dangote ta kaddamar a Najeriya. Wannan dai na daga cikin matakan rage radadin talauci a tsakanin al'ummar Najeriya, da gidauniyyar hamshakin attajirin Afirka ta kaddamar a birnin Kano da ke arewacin kasar.
Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Ahmed Abba.......
Wed, 27 Mar 2024 - 316 - Yadda matsin rayuwa ya tilastawa 'yan Najeriya fasa rumbunan abinciWed, 06 Mar 2024
- 315 - Yadda al'ummar kasashen yammacin Afrika ke kokawa saboda tsadar rayuwa
A wannan makon shirin Kasuwa akai miki dole, zai yi duba ne game da bakar ukubar da al’ummar kasashen Nahiyar Africa ke fuskanta, a sanadiyar hauhawar farashin kayayyakin masarufi, musamman kasashen Nijeriya, Nijar da kuma Cameroon. Yanzu haka dai a iya cewa wannan yanayi na hauhawar farashin kayan masarufi tuni ya zame wa kasashen Nijeriya da Nijar da Ghana da kuma Cameroon Dan zani a kasuwa.
Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Abdulkadir Haladu Kiyawa.....
Wed, 28 Feb 2024 - 314 - Yadda Najeriya ke neman taimakon Bankin Duniya don farfado da tattalin arziki
Shirin Kasuwa a kai miki dole tare da Rukayya Abba Kabara a wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda Najeriya ke neman taimakon bankin duniya a wani yunkuri na farfado da tattalin arzikin kasar da ke fuskantar tarnaki.
Tattalin arzikin na Najeriya na ci gaba da durkushewa ne duk da kasancewarta mafi karfin tattalin arziki kuma mafi yawan jama'a a nahiyar Afrika, dalilan da ake alakantawa da yankewar yawan man da kasar ke fitarwa baya ga ci gaba da zangewar darajar kudin kasar.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...
Tue, 13 Feb 2024 - 313 - Faduwar darajar Naira ta tsayar da harkokin 'yan canji a makwaftan NajeriyaWed, 07 Feb 2024
- 312 - Dalilan soke lasisin wasu kamfanonin wutar lantarki
Shirin Kasuwa a Kai Maki Dole na wannan mako, ya mayar da hankali ne a game da batun wutar lantarki a Najeriya, bangaren da ke fama da matsalololi tsawon shekaru.
Shirin zai yi dubi ne a game da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na sokewa da kuma sabunta lasisi ga wasu kamfanonin da ke da alhaki rarraba wuta a cikin kasar.Wed, 31 Jan 2024 - 311 - Yadda faduwar darajar Naira ke yin illa ga kasuwanci a Najeriya
Shirin 'Kasuwa a kai miki dole' na wanna makon ya mayar da hankali akan faduwar darajar naira da ke ci gaba da yin illa ga harkokin kasuwanci a sassan Najeriya.
Wakilinmu a jihar Kano Abubakar Abdulkadir Dangambo ya duba yadda matsalar ke yin tasiri musamman babbar kasuwar hatsi ta Dawanau da ke Kano, wadda ke tattara 'yan kasuwa daga Najeriya da kuma kasashe irin su Chadi da Kamaru da Nijar da Mali da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Wed, 24 Jan 2024 - 310 - Yadda rufe iyakar Benin ya haifar da tsadar rayuwa a Nijar
Shirin "Kasuwa akai Miki dole" na wanan mako tare da Ahmed Abba ya leka ne jihar Dosso dake Jamhuriya Nijar, yankin da ke kan iyaka da birnin Cotonou na Jamhuriya Benin inda jama'a suka shiga matsanancin halin tsadar rayuwa tare da kariyar tattalin arziki, sakamakon takun-kuman da Kungiyayoyi irinsu ECOWAS ko CEDEAO suka laftawa kasar, saboda Juyin mulkin da Sojoji sukayi.
A Ranar 9 ga Watan Octoba da ya wuce Jamhuriya Benin ta rufe iyakar dake tsakaninta da makwabciyarta Jamhuriyar Nijar, bayan matakin da Kungiya ECOWAS ko CEDEAO ta dauka bayan da sojoji suka karbe mulki Ranar 26 ga watan Yuli wajen hambarar da shugaban Mohamed Bazoum.
Jamhuriyar Bénin ta dauki matakin soke duk wata hulda cinikaya da gwamnatin sojin Nijar.
Wanan matakin dai ya janyo hauhawa farashin Kayan bukatun jama'a na yau da kullun tare da haifar da koma bayan tattalin arziki a wasu sassan kasar, masamman yankin Dosso, jiha daya tilo a Nijar da ta yi iyaka da Bénin har tsawan kilimita 150 daga yammacin Kasar.
Wed, 22 Nov 2023 - 309 - 'Yan Najeriya na cikin matsin tattalin arziki tun bayan janye tallafin mai
Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan hauhawar farashin kayyaki da ake fama da shi a Najeriya, wanda ya jefa al'umma masu karamin karfi cikin halin kunci.
A Najeriyar tun bayan janye tallafin man fetir da kuma matsalolin rashin kudaden waje masamman dalar Amurka sun tsunduma kasar cikin mummunar hauhawar farashin kayayyaki a kasuwanni, lamarin da ya jefa al’ummar kasar musamman masu karamin karfi cikin mawuyacin hali.
Alkaluman hukumar kididdigar Najeriya na watan Satumba sun nuna cewa hauhawan farashin kayayyaki ya kai kashi 26.72, wanda masana ke gargadin zai iya kaiwa da kaso 30 cikin 100 nan da watan Disamba muddun ba’a kai ga gano bakin zarenba.
Domin duba girman matsalar hauhawan farashin, RFI Hausa ya leka kasuwar Mile 12 International dake birnin Legas, daya daga cikin manyan kasuwannin kayan abinci da gwari a kasar.
Wed, 15 Nov 2023 - 308 - Yadda masu kiwon kaji a Najeriya ke rufe gonakinsu saboda tsadar kayan abinciWed, 01 Nov 2023
- 307 - Yadda aka sake bude kasuwar Monday Market a jihar BornoWed, 25 Oct 2023
- 306 - CISLAC ta horas da 'yan majalisun Najeriya kan muhimmacin haraji ga kasa
Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan jan hankali da kungiyoyi irinsu CISLAC ke yi a Najeriya, wajen ganin gwamnati ta maida hankali kan gibi da ake samu a fannin tara haraji domin samun kudaden shiga.
Masana sun yi ittifakin cewar Najeriya na da dimbin arzikin da bai kamata ace sai ta ciyo bashin kudade kafin biyan bukatun ta ba, amma sakaci da kuma cin hanci da rashawa da ya yi wa kasar katutu ke mayar da ita baya.
Wannan yasa kungiyar CISLAC mai zaman kanta da ke sa ido kan ayyukan majalisar dokoki da kuma yaki da rashawa, da hadin guiwan cibiyar horar da ‘yan majalisun dokoki da demokuradiyya, suka shirya taro don horarwa da nunawa ‘yan majalisu rawar da za su taka wajen yin dokoki da saka ido a hanyoyin samar da haraji ga kasa.
Wed, 18 Oct 2023 - 305 - Yadda Proparco ta ba da gudummuwa ga tattalin arzikin Najeriya cikin shekaru 15
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole na wannan makon ya mayar da hankali ne kan bukin cika shekaru 15 cibiyar bada lamuni da raya kasashe ta kasar Faransa Proparco ta yi ta na gudanar da ayyukanta a Najeriya, inda ta zuba jarin da ya kai dala biliyan daya a kasar cikin shekarun. Shirin zai mayar da hankali ne kan yadda ayyukan cibiyar ke bayar da gudunmawa ga fannonin daban-daban na ci gaban tattalin arzikin Najeriya.
Tun bayan kafa cibiyar a shekarar 2008 a Najeriya, Proparco ta mai da hankali wajen hadin gwiwa da cibiyoyin hada-hadar kudi na cikin gida da na wasu kasashen Afirka wajen zuba hannun jari ga kamfanoni masu tasowa da sabbin kafuwa a fannin makamashi mara gurba da muhalli da harkokin noma da kere-kere da kiwon lafiya da dai sauransu…
Tue, 17 Oct 2023 - 304 - Jiragen ƙasa sun fara jigilar kayayyaki daga Legas zuwa IbadanWed, 20 Sep 2023
- 303 - Yadda kwanaki 100 na gwamnatin Tinubu ya riski ƴan NajeriyaWed, 13 Sep 2023
- 302 - Matsunta a Kamaru sun bukaci dage haramcin kamun kifi a LagdoWed, 06 Sep 2023
- 301 - Tasirin tattalin arzikin shigar sabbin kasashe kungiyar BRICS
Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole na wannan mako ya maida hankali ne kan taron Kungiyar BRICS ta kasashe masu tasowa wadanda suka kunshi Brazil da Rasha da India da China da kuma Afirka ta Kudu, wanda aka kafa ta domin kalubalantar kaifin tattalin arzikin kasashen yammacin duniya, wadda ta amince da shigar da sabbin kasashe shida cikinta amatsayin mambobi, wato Saudiyya da Iran da Habasha da Masar da Argentina sai kuma Hadaddiyar Daular Larabawa.
Sat, 02 Sep 2023 - 300 - Janye tallafin mai: Ta yaya tallafin gwamnatin Najeriya zai kai ga marasa galihu?
Shirin kasuwa a kai miki dole na wannan mako ya yada zango ne tarayyar Najeriya, inda Gwamnatin kasar ta ware kusan Naira biliyan 200, wanda ta rabawa jihohi 36 na kasar da birnnin tarayya Abuja da kuma motocin shinkafa, domin ragewa talakawa radadin da janye tallafin man fetur ya jefasu ciki.
Ta yaya wannan tallafi zai kai ga marasa galihu, wadanda akayi dominsu? Abin da Shirin zai maida hankali akai kenan
Wed, 23 Aug 2023 - 299 - Farashin kayan abinci ya yi tashin goron zabi a duniya
Shirin Kasuwa A Kai Miki Dole na wannan makon ya yi nazari ne kan yadda ake ci gaba da samun hau-hawan farashin kayayyakin abinci a kasashen duniya musamman nahiyar Afrika.
Masana sun bayyana cewa, yakin da ake fama da shi Ukraine na daya daga cikin manyan dalilan da suka haddasa tsadar farashin abinci a kasashen duniya, yayin da matsalar ke ci gaba da kamari a nahiyar Afrika saboda karin dalilai da suka hada da hare-haren ta'addanci da suka hana manoma zuwa gona ballantana shuka da girbi.
Ku latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken shirin tare da Ahmed Abba.
Wed, 16 Aug 2023
Podcasts similaires à Kasuwanci
- Health Naturally with Denis Stewart 2NURFM
- Aa Gym Official Aa Gym Official
- ABC News Daily ABC
- Al-Quran Al-kareem Al-Quran Al-kareem
- Kumpulan Shalawat Andri Nugraha
- CNN Indonesia CNN Indonesia
- KH ANWAR ZAHID OFFICIAL Dakwah NU
- Dakwah Tauhid Dakwah Tauhid
- Dzulqarnain Muhammad Sunusi Dzulqarnainms
- Firanda Andirja Official Firanda Andirja
- Ngaji Bareng Gus Baha Gus Baha
- Ps. Juan Mogi Juan Mogi Official
- K.H. ZAINUDDIN MZ K.H. ZAINUDDIN MZ
- Kumpulan Dakwah Islam Lentera Pagi
- Ludruk Cak Kartolo dkk Ludrukan
- Dongeng Sunda, Dongeng Enteng Mang Jaya Mang Jaya
- Merry Riana Merry Riana
- Murottal Qur'an Terjemahan Audio Indonesia Muslim
- Ngaji Gus Baha' Ngaji Gus Baha'
- Wayang Kulit Indonesia Raden Ontoseno
- Radio Rodja 756 AM Radio Rodja 756AM
- GUS BAHA sofa bisnis
- Ustad Das'ad Latif Ustad Das'ad Latif
- Misteri Seru Widya Yudha Utama
Autres podcasts de Affaires
- Tanguy Pastureau maltraite l'info France Inter
- Les experts BFM Business
- BFM Bourse BFM Business
- C'est votre argent BFM Business
- Forward Leadership George Moustakelis
- Tout pour investir BFM Business
- Midnight Zen Wilton Ng
- On n'arrête pas l'éco France Inter
- FAQ IMMOBILIER Maryan GreatParis
- Le Mag Immo France Télévisions
- Once Upon a Business Mirasee FM
- Medium Energy Evan Helda
- Coconut Avenue (Singapore Properties by TFC) The Financial Coconut
- La Martingale Matthieu Stefani | Orso Media
- IA qu'à m'expliquer Le Temps Podcasts
- Ni Buenas Ni Malas Ni Buenas Ni Malas Podcast
- Leadership Stars Linda Patten
- Leadership English Tannia Suárez
- Grands Leaders, les leçons de l'Histoire Radio Classique
- Motivational and Inspirational Motivation And Inspiration