Filtrer par genre

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

RFI Hausa

Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Al’umma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalin’ariziki, al’adu da dai sauransu…

553 - Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun yi watsi da sabon harajin da CBN ya bullo da shi
0:00 / 0:00
1x
  • 553 - Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun yi watsi da sabon harajin da CBN ya bullo da shi

    Ƙungiyar Ƙwadago da sauran kungiyoyin farar hula a Najeriya sun yi fatali da matakin gwamnati na baiwa bankuna umarnin fara cirar harajin kashi 0.5 wato rabin ɗaya kenan cikin 100, kan duk hada-hadar aika kudaden da ‘yan kasar ke yi ta intanet.

    A cewar gwamnatin za a rika amfani da sabon harajin don samar da tsaro daga barazanar masu yi wa mutane kutsen satar kuɗaɗe da sauran muhimman bayanai ta shafukan intanet.

    Sai dai ƙungiyoyin sun ce sabon harajin zai sake jefa ‘yan Najeriya musamman matsakaita da masu ƙaramin ƙarfi ne cikin ƙarin ƙunci, bayan matsin da suke ciki.

    Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

    Thu, 09 May 2024
  • 552 - Kan gudun mowar Japan ga yankin Sahel wajen yaki da ta'addanci

    Bayan kammala ziyarar kwanaki biyu da ministar harkokin wajen ƙasar ta kai a Najeriya, gwamnatin Japan ta ce za ta bayar da gudun mowa domin yaƙi da ayyukan ta’addanci a yankin Sahel.

    A tarihi dai ba kasafai Japan ke shiga batutuwan da suka shafi yaƙi da ta’addanci ba a duniya, abin da ya sa wasu ke ganin cewa duk wani tallafi da zai fito daga ƙasar zai kasance mai alfanu wajen yaki da wannan matsala.

    Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

    Thu, 02 May 2024
  • 551 - Kan matakin rufe wasu kafafen yada labarai da gwamnatin sojin Burkina Faso ta yi

    Ƙasashen duniya da kuma ƙungiyoyi kaƙƙin aikin jarida da kuma ‘yancin bayyan ra’ayi, sun yi tir a game da matakin rufe wasu kafafen yaɗa labarai da gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso ta dauka.

    Baya ga kafafen yada labaran Faransa ciki har da RFI da kuma France24, matakin rufe kafafen yaɗa labaran ya shafi na Amurka, Birtaniya Faransa da dai sauransu domin kawai wallafa rahoton kungiyar HRW da ke zargin dakarun gwamnati da yi wa fararen hula kisan gilla.

    Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkeen shirin.

    Tue, 30 Apr 2024
  • 550 - Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa da dama

    Shirin ra'ayoyin masu saurare na wannan rana ta Juma'a ya bai wa jama'a damar tofa albarkacin bakinsu ne game da batutuwa da dama da ke ci musu tuwo a kwarya, kama daga siyasa, tattalin arziki, tsaro, zaman-takewa da dai sauransu.

    Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin.

    Fri, 26 Apr 2024
  • 549 - An fara samun karancin man fetur a sassan Najeriya

    Rahotanni daga sassan arewacin Najeriya na nuna cewar an fara samun karancin man fetur a gidajen sayar da man, abinda ya sa wasu masu man kara farashin da suke sayar da kowacce lita.

    Ko menene ya haddasa matsalar karancin man fetur din a sassan kasar?

    Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

    Thu, 25 Apr 2024
Afficher plus d'épisodes