Filtrer par genre
- 399 - Jamhuriyar Nijar ta gudanar da bikin ranar Hausa ta bana a ƙasar
Shirin Al’adumu na gado a wannan makon ya sake waiwayar baukukuwan ranar Hausa ne ta Duniya, ranar da babban taronta ke gudana a dukkanin ranakun 26 ga watan Agusta duk shekara, to amma kasancewar bikin ya samu karɓuwa a gwamman ƙasashe ya sa bayan babban taron ake gudanar da wasu ƙarin bukukuwan ranar hausar ta Duniya a ƙasashe daban daban, ciki har da Jamhuriyar Nijar, inda aka gudanar da bikin zagayowar ranar hausar ta Duniya a ranar 8 ga watan Satumban da muke.
Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Nura Ado Sulaiman.
Tue, 15 Sep 2026 - 398 - Muhawara kan banbance tsakanin ƙabilun Hausawa da kuma Fulani a Najeriya
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon ya mayar da hankali kan zamantakewa da auratayyar ƙabilun Hausawa da Fulani, ƙabilu 2 da suka juye zuwa Hausa Fulani bayan zaman tare na tsawon shekaru musamman a Najeriya.
A baya-bayan nan muhawara ta fara zafi kan buƙatar banbance ƙabilun biyu zuwa Hausa daban da kuma Fulani zalla, lamarin da ya ci karo da fahimtar wasu daga cikin masana a ɓangaren al'adu.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Tue, 08 Sep 2026 - 397 - Batutuwan da bikin 'Ranar Hausa ta Duniya' zai mayar da hankali kai a banaTue, 25 Aug 2026
- 396 - Halin da ake ciki game da al'adar 'Yan Kama da ke neman ɓacewa a ƙasar Hausa
Shirin "Al’adunmu na gado, ya mayar da hankali kan fadi-tashin da ake yi don adana tsohuwar al'adar mawaƙan 'Yan Kama a ƙasar Hausa.
Waƙoƙin 'Yan Kama salon fasaha ne na musamman da mawaƙan ke amfani da shi domin nishaɗantarwa, inda suke sauya shahararrun waƙoƙi su koma na maganar abinci ko cika tumbi.
A cikin shirin, masana sun bayyana yadda waɗannan mawaƙa ke da ƙwarewa wajen sarrafa harshen Hausa da sauya salon magana don juyata zuwa nishaɗi.
Sai dai bincike ya nuna cewa wannan daɗaɗɗiyar al'ada tana dab da ɓacewa gaba ɗaya a wannan zamanin na yanzu.
Babban dalilin da ya sa sana'ar ke mutuwa shi ne rashin gado, domin kuwa ko da su kansu 'ya'yan mawaƙan na 'Yan Kama ba sa sha'awar ɗaukar wannan sana'a don gadon iyayensu kamar yadda aka saba a baya.
Tue, 18 Aug 2026 - 395 - Wane tasiri Chamfi ke da shi wajen gyarawa ko kuma ruguza aure musamman a zamanin bayaTue, 04 Aug 2026
- 394 - Muhimmancin zurfafa bincike a dukkan fannoni gabanin aure
Shirin 'Al'adunmu Na Gado zai yi duba ne kan muhimmancin zurfafa bincike gabanin aure.
Al’adun al’ummar Hausawa da ma mafi yawan al’ummomin da ke zaune a yankin arewacin Nigeria, sun sahale wa iyaye, gudanar da bincike kan yaron da ya nuna kai yana son ‘yarsu da aure, kamar yadda shima bangaren angon, kan yi bincike kan yanayin lafiya, tarbiyya da nasabar yarinyar.
Irin wannan bincike, ya taimaka matuka wajen tantance masu neman aure tare da dakile wadanda ke da matsaloli a fannin dabi’u, rashin halayen kwarai da kuma matsala a fannin lafiya.
Tue, 14 Jul 2026 - 393 - Makomar makarantun gwaji na harsunan gida a Jamhuriyar Nijar.Tue, 30 Jun 2026
- 392 - Yadda Hausawa ke cin kasuwar abincin gargajiya a Saudiyya
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoullaye Issa a wannan mako ya yi duba kan yadda Hausawa ke ɗabbaƙa al'adunsu ta hanyar hada-hadar abincin gargajiya a ƙasa mai tsarki ko kuma Saudi Arabiya.
Kamar yadda ya ke sanannen abu, Hausawa kan rungumi mabanbantan sabbin al'adu amma yana matuƙar wahala a garesu su yi watsi da abincin da suturarsu, wannan ya sanya samun kasuwannin abincin gargajiya da dama a ƙasa mai tsarki sakamakon yawaitar Hausawa ko dai ƴan safara ko kuma masu Ibada koma mazauna wannan ƙasar ta Saudiyya.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Tue, 23 Jun 2026 - 391 - Yadda kiɗan Gurmi ke neman ɓacewa a ƙasar Hausa
Shirinmu na yau ya leƙa sassan arewacin Najeriya da Jamhuriyar Nijar, tare da duba yadda wani fitaccen kiɗan gargajiya, wato kiɗan Gurmi, ke fuskantar barazanar bacewa a fadin ƙasar Hausa. Shin me ke janyo haka, kuma wane canji fasahar zamani ta kawo?
Gurmi, kayan kiɗa ne da aka sani tun kaka da kakanni, wanda ƙera ta hanyar amfani da ƙoƙon ƙwarya da aka rufe shi da fatar dabba, musamman fatar guza, sannan a ɗaura masa tsirkiya guda biyu ko uku.
A cikin shekarun da suka gabata, manyan mawaƙa irinsu Rabi'u mai Gurmi Gumel da Rabe mai Gurmi Jibia sun zagaya duniya suna baje kolin wannan fasaha.
Amma a yau, idan ka zagaya biranen ƙasar Hausa, da kyar kake jin sautin wannan kiɗa, maimakon haka, sautin kiɗan na’urorin zamani na matasa sune suka mamaye ko'ina.
Duk da wannan ƙalubale, wasu mawaƙan zamanin na ƙoƙarin haɗa sautin gurmi da kiɗan zamani don janyo hankalin matasa da kuma kaucewa ɓacewar wannan muhimmin kiɗa na al'ada.
Tue, 16 Jun 2026 - 390 - Yadda Hausawa mazauna Jamus suka gudanar da gagarumin taron sada zumunciTue, 09 Jun 2026
- 389 - Gombe: Fulani sun yi taro kan warware matsalolin da ke ɓata musu suna
Shirin Al'adunmu na Gado a wannan mako, yayi tattaki ne zuwa garin Gombe, inda Al'ummar Fulani suka gudanar da wani taro na farfaɗo da Al'adunsu na Gargajiya, da kuma tattaunawa a kan hanyoyin da za a bi wajen maido da Tarbiyya, gami da zamantakewa kyakkyawa a tsakanin Fulanin da kuma sauran Ƙabilu.
Thu, 28 May 2026 - 388 - Yadda al'ummar wani gari suka riƙe Al'adar da suke kira da "Sai kowa ya zo"Tue, 12 May 2026
- 387 - Tasirin karance-karance Littattafan Hausa wajen ɗabbaƙa al'adun Hausawa
Shirin Al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya mayar da hankali ne kan tasirin karance-karancen Littattafan Hausa a zamantakewar Al'ummar yankin.
Irin waɗannan Littafai kuwa sun ƙunshi Magana Jari da jiki Magayi baya da Uwar Gulma da Shehu Umar kana Ruwan Bagaja, waɗanda dukkaninsu suka taimaka wajen fito da Al'adar Hausawa a fili.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Tue, 05 May 2026 - 386 - Rawar da mayaƙa suka taka zamanin da a Masarautun ƙasar Hausa
Shirin Al’adun mu na Gado a wannan makon ya leka Jamhuriyar Nijar ne, inda ya duba batun da ya shafi mazajen dauri, musaman mayaƙan gargajiya a wannan zamani, jaruman da ke ƙarƙashin inuwar sarakunan gargajiya.
Duk inda akwai masarautun gargajiya an san su da tarin mayaƙa da ke yin tsarin daka a cikin kowane irin hali don kare su. Wannan tsarin ne da ya samo sali tun zamani da ake yaƙe-yaƙe tsakanin masarautu.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa...........
Tue, 21 Apr 2026 - 385 - Yadda kiɗan shantu ke ƙoƙarin ɓacewa duk da shaharar da ya yi a shekarun baya
Shirin Al'adun mu na gado na wnnann mako ya waiwayi kiɗan Shantu ne da ya shahara tsakanin Mata a shekarun baya, wanda bayan tasirin da ya yi a waccan lokaci a fagen nishaɗantarwa, kiɗan na Shantu ke neman ɓacewa a yanzu. A shekarun baya dai wannan kiɗa na Shantu ya shahara ne tsakanin mata a yankunan arewacin Najeriya musamman a makarantu ko ɗalibai da kuma wasu sassan Jamhuriyar Nijar.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman...........
Tue, 07 Apr 2026 - 384 - Yadda bikin addinin gargajiya na Vodun ke gudana a Jamhuriyar Benin (2)Tue, 27 Jan 2026
- 383 - Yadda bikin addinin gargajiya na Vodun ke gudana a Jamhuriyar Benin
Shirin Al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya yi tattaki ne zuwa Jamhuriyar Benin, inda ya halarci bukukuwan addinin gargajiya na Vodun, bikin da ke da muhimmanci matuƙa a ƙasar.
Tun a bara ne aka ƙara wa'adin ranakun gudanar da wannan biki wanda ke samun mahalarta daga sassa daban-daban na duniya, inda alƙaluma suka nuna cewar a shekarar bara baƙi fiye da dubu 100 ne suka halarci bikin.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Tue, 20 Jan 2026 - 382 - Hausawan Turai na fuskantar barazanar ɓacewar harshe da al'adunsu
Shirin "Al'adunmu na gado" a wannan makon tare da Nura Ado Suleiman ya leƙa ne Masarautar Hausawa da ke nahiyar Turai, inda a makon Masarautar ta karɓi baƙuncin Mai Martaba Sarkin Daura Dakta Umar Faruk Umar da ya yi tattaki daga Tarayyar Najeriya, domin halartar bikin karrama Sarkin Hausawan na Turai da kuma naɗin wasu sabbin muƙaman na sarauta da suka shafi sassan nahiyar.
Daya daga cikin kalubalen da Hausawa mazauna Turai ke fuskanta, shi ne bacewar harshen Hausa da al’adu a tsakaninsu, sai dai a yayin ziyarar da ya kai wa Sarkin Hausawan Turai da ke birnin Paris Alhaji Surajo Jan Kaɗo, Mai Martaba Sarkin Daura Dakta Umar Faruk Umar, ya yi alkawarin farfaɗo da martabar harshen na Hausa.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Tue, 13 Jan 2026 - 381 - Yadda aka gudanar da bikin nuna al'adu na masarautar Jiwa a AbujaTue, 06 Jan 2026
- 380 - Yadda aka gudanar da bikin naɗin sarautar sarkin Komadugu a Maraɗi
Shirin na yau ya yada zango jihar Diffa dake Jamhuriyar Nijar,yankin da aka gudanar da bikin nadin sabon sarkin Komadugu, wanda ya samu halartar baƙi daga ciki da wajen ƙasar.
Diffa dai kamar dai yadda masana tarihi suka tabbatar, ana na nufin Diwa a harshen Kanuri kenan.
Kalmar ta samo asali ne daga kalmar "Di wa Nallé wa," wadda ke nuna tsabtar jiki da dai sauran abubuwan da suka shafi maza da mata na yankin.
Di na nufin farin gashi, kuma Nallé na nufin lalle wanda ke da ma'ana biyu.
Wannan jumla, Di wa Nallé wa, na nufin mata waɗanda, ko da a cikin tsufa, suna rina gashinsu da lalle.
Tarihi ya nuna cewa a ƙarni na 19, yankin Diffa a lokaci na karkashin masarautar Kanem-Bornu,inda a shekarar 1933 Turawan mulkin mallaka a lokacin sun kafa yankin Komadougou, wanda aka bayyana yankin da farko yake zaune a Bosso sannan daga baya ya koma Gueskérou.
An gudanar da zaɓen sabon sarkin na komadugu a jahar Diffa a gaban hukumomin bariki da na gargajiya da kuma sauran al’umma, wanda ya kai ga zaɓen Hassan Mamadou Abba Kyari a matsayin sabon sarkin na Komadugu.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Abdoullaye Issa.
Tue, 02 Dec 2025 - 379 - Yadda sana'ar sassaƙar Turmi ke fuskantar koma baya sabida ci gaban zamani
Shirin "Al'adun mu na Gado" na wannan makon ya yi duba ne akan sana'ar nan ta sassaƙar Turmin, wadda ke a matsayin sana'ar al'adun gargajiya, ko da yake a yanzu samar da na'urori da ke amfanin da Turmin keyi ya mayar da sana'ar baya matuka gaya.
A baya duk macen da za'a kai gidan miji, akan hadata da Turmin babba da ƙarami kana da kuma na ƙarfe wanda za ta rika daka kayan ƙanshi wasu ma hatta Kwalli fari da ake sanyawa jarirai da shi suke dakawa, baya da kuma na da kan sakwara da kuma babba na surfe da daka.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa............
Tue, 25 Nov 2025 - 378 - Yadda ƴan siyasa ke katsalandan a harkokin masarautu a NajeriyaTue, 18 Nov 2025
- 377 - Bikin Kalankuwar farfaɗo da al'adun Hausawa a jihar Kano ta Najeriya
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali ne kan Kalankuwar farfaɗo da al'adunmu Hausawa a jihar Kano ta arewacin Najeriya, a wani yanayi da al'umma ke fuskantar matsalar gushewar tarin al'adu a mataki daban-daban.
Yayin wannan bikin Kalankuwa dai an duba fannoni daban-daban na al'adu kama daga Kiɗan gargajiya da Waƙa baya ɓangarorin wasanni da dama, bikin da ya samu halartar sarakuna da dama.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...
Tue, 04 Nov 2025 - 376 - Yadda al'adar ''Ƴar zaman Ɗaki'' ta zama tarihi tsakanin hausawa
Shirin Al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda sananniyar al'adar nan ta zaman ɗaki ke ƙoƙarin shuɗewa tsakanin al'ummar Hausawa.
Shekaru aru-aru, da zarar an yi auren budurwa a ƙasar Hausa akan haɗata da ƙaramar yarinya da za ta yi mata zaman ɗaki, wanda a wasu lokutan anje kenan domin galibi aure ke raba wannan ƙaramar yarinya da gidan, kodayake wasu kan shafe wani wa'adi ne gabanin komawa gaban iyayensu na ainahi.
Sai dai a ƴan shekarun nan wannan al'ada da kan yi tasiri wajen ƙarfafa zumunci ta zama tarihi, walau ko saboda yanayi na rayuwa, ko kuma saboda yadda aka tsagaita da auren ƴammata masu ƙarancin shekaru da dai sauran dalilai.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...
Tue, 28 Oct 2025
Podcasts similaires à Al'adun Gargajiya
El Partidazo de COPE COPE
Herrera en COPE COPE
La Linterna COPE
Es la Mañana de Federico esRadio
La noche de Cuesta esRadio
Hondelatte Raconte Europe 1
Au Coeur du Crime Europe1
Affaires sensibles France Inter
LEGEND Guillaume Pley
El colegio invisible OndaCero
La Rosa de los Vientos OndaCero
Les grands dossiers de l'Histoire par Franck Ferrand Radio Classique
Espacio en blanco Radio Nacional
Enquêtes criminelles RTL
Entrez dans l'Histoire RTL
Le grand récit RTL
Les Grosses Têtes RTL
L'Heure Du Crime RTL
Parlons-nous RTL
El Larguero SER Podcast
SER Historia SER Podcast
Todo Concostrina SER Podcast
Un Libro Una Hora SER Podcast
HISTORIAS DE LA HISTORIA VIVA RADIO
