Filtrer par genre

Dandalin Siyasa

Dandalin Siyasa

RFI Hausa

Shirin Dandalin Siyasa, yana tattaunawa tare da tafka muhawar kan al’amurran siyasa da ke faruwa a kasashen duniya, da batutuwan da suka shafi al’umma kai tsaye, wanda Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta. Wannan Shirin na zuwa ne a karshen mako Ranar Assabar da maimaci a ranar Lahadi a Shirye Shiryen Safe da Yamma.

164 - Jawabin Tinubu na cika shekaru 66 da samun ƴancin kan Najeriya ya bar baya da ƙura
0:00 / 0:00
1x
  • 164 - Jawabin Tinubu na cika shekaru 66 da samun ƴancin kan Najeriya ya bar baya da ƙura

    Shirin ‘Dandalin Siyasa’ na wannan mako, ya maida hankali ne kan cikar Najeriya shekaru 66 da samun ƴancin kai, kuma yayin da ake bikin wannan rana, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa ’yan ƙasar jawabi inda ya jaddada nasarorin da ya ce gwamnatinsa ta ce ta samu a fannin tattalin arziki, tare da bayyana fatansa na ganin ƙasar ta samu ƙarin wadata. Sai dai shugaban bai yi magana kan matsalar tsaro da ke ci gaba da ta zame wa wasu sassan ƙasar ƙarfen ƙafa ba.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson.............

    Sat, 03 Oct 2026
  • 163 - A Najeriya shirin yaƙin neman zaben 2027 ya shiga wani sabon mataki

    Shirin na wannan makon tare da Michael Kuduson, ya yi nazari ne akan yadda a Najeriya yakin neman zaben 2027 ya shiga wani sabon mataki, bayan fara yakin neman zaben kujerun gwamna da ’yan majalisun jihohi a hukumance, inda Hukumar zabe ta Najeriya INEC ta kuma tunatar da ’yan takara da jam’iyyun siyasa cewa dole ne su gudanar da yakin neman zabe bisa tanade-tanaden doka.

    Sat, 12 Sep 2026
  • 162 - INEC na duba yiwuwar gudanar da zaɓen gwaji na shugaban ƙasa gabanin zaɓen 2027

    Shirin na wannan makon, ya karkata ne kan yadda jam'iyyun siyasa ke ƙoƙarin cimma matsaya game da yadda za su tunkari zaɓen 2027, daidai lokacin da Hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta INEC, na duba yiwuwar gudanar da zaɓen gwaji amma, na shugaban ƙasa, domin tantance shirye-shiryen tsarin zaɓen na baɗi.

    Wannan na zuwa ne, yayin da cikin makon jiya, aka jiyo Shugaba Bola Tinubu na bayyana cewa ɓangaren Arewacin ƙasar ne ya fi cin gajiyar wasu daga cikin sauye-sauyen da gwamnatinsa ta ƙaddamar, abin da ya fuskanci suka da caccaka daga masu ruwa da tsaki da ƙungiyoyin fararen hula.

    A gefe guda kuma, batun yadda ake tallafa wa jama'a a lokutan matsin tattalin arziki na cigaba da zama wani batu na siyasa, inda Ministan Tsaro ya yi kira ga gwamnonin jihohi da su daina raba babura a matsayin tallafin gaggawa ga jama'a, yana mai neman a mayar da hankali kan hanyoyin da za su samar da mafita mai ɗorewa.

    Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson.

    Sat, 05 Sep 2026
  • 161 - Ƴan adawa sun kaɗa hantar jam'iyar APC mai mulki a Najeriya

    Yayin da aka kaɗa gangar siyasa gabanin zaɓen shekarar 2027 da ke kara kusantowa, ƴan siyasa na ci gaba da gabatar da manufofi da alƙawuran da suke cewa za su inganta rayuwar ƴan Najeriya. A wannan makon, batun tallafin man fetur, sake bude iyakokin ƙasa da matsalar tsaro sun sake zama wasu daga cikin muhimman batutuwan da ƴan adawa ke amfani da su wajen ƙalubalantar gwamnati.

    Ku lasha alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson...........

    Sat, 29 Aug 2026
  • 160 - Tasirin zaɓen gwamnan Osun ga babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027

    Shirin Dandalin Siyasa na wannan mako ya mayar da hankali ne kan tasirin zaɓen gwamnan jihar Osun yayin da ake tunkarar babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027.

    Shirin ya kuma yi duba game da halin da ake ciki a zaɓen na Osun, kama daga rikicin siyasa da kuma zarge-zargen da abokan hamayya ke yi wa juna.

    Latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin...

    Sat, 15 Aug 2026
Afficher plus d'épisodes

Autres podcasts de Actualités et Politique