Filtrar por género

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

RFI Hausa

Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Al’umma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalin’ariziki, al’adu da dai sauransu…

773 - Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa mabanbanta
0:00 / 0:00
1x
  • 773 - Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa mabanbanta

    Yau juma'a kamar yadda aka saba, sashen Hausa na RFI na bai wa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwan dake ci musu tuwo a ƙwarya, kama daga siyasa, tattalin arziƙi, tsaro, zamantakewa da dai sauransu.

    Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

    Fri, 18 Sep 2026
  • 772 - Ra'ayoyin masu sauraro kan ƴan aikin jarida dake fuskantar tarnaƙi a Afrika

    Ƴancin aikin jarida na ci gaba da fuskantar tarnaƙi a wasu ƙasashen Afirka, saboda yayin da wasu ke fuskantar tursasawa a Najeriya, a Jamhuriyar Nijar kuwa ana tsare da Moussa Tchangari kusan shekaru biyu ba tare da shara’a ba, yayin da a hannu ɗaya, wani ɗanjaridar wato Moussa Kaka ya ɓata yau kwanaki 16 kenan.

    A can kuwa Mali ko shekaran jiya litinin ma an yanke wa wani ɗanjaridar hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari, kamar dai yadda ake cafkewa tare da tilasta ƴanjaridar da ra’ayoyinsu suka bambanta da na gwamnati, shiga aikin soji a Burkina Faso.

    Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai yau.

    Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

    Wed, 16 Sep 2026
  • 771 - Ra'ayoyin masu sauraro kan hauhawar farashin man fetur a Najeriya

    Hauhawar farashin man fetur na ci gaba da haifar da tarin matsaloli ga al’ummar Najeriya, inda a jihohi irinsu Sokoto, Kebbi da Zamfara, farashin lita ya doshi Naira dubu ɗaya da 500 a halin yanzu kuma kusan hakan farashin yake a mafi yawan jihohin arewacimn ƙasar.

    Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai yau, musamman game da yadda ake samun hauhawar farashin akai-akai da kuma yadda wataƙila hakan ke shafar kasuwanci da kuma sufuri a yankunanku.

    Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

    Tue, 15 Sep 2026
  • 770 - Ranar yaƙi da jahilci ta duniya a bana ya duba yadda za a inganta ilimin manya

    Ranar takwas ga watan Satumban kowacce shekara, rana ce da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware, tun a shekarar  1960 a matsayin ranar yaƙi da jahilci, inda ake mayar da hankali wajen faɗakar da jama'ar a sassan duniya mahimmancin ilimi da samar da tsari ko dabarun koyar da mutanen da basu samu dama ba.

    A mafi yawan ƙasashe dai an sha aiwatar da tsarin yaƙi da jahilci da ke bai wa dattijai ko masu manyan shekaru damar iya koyon rubutu da karatu a rayuwarsu.

    Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

    Tue, 08 Sep 2026
  • 769 - Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa mabanbanta

    Kamar yadda aka saba ko wace rana irin ta yau Juma’a, muna baku damar tofa albarkacin bakin ku kan wasu abubuwa da ke ci muku tuwo a ƙwarya kama daga siyasa da tattalin arziƙi da zamantakewa da dai sauransu.

    To yau ba ta sauya zani ba, sai ku latsa alamar sauti don sauraren shirin...

    Fri, 28 Aug 2026
Mostrar más episodios

Otros podcasts de Noticias y Politica