Filtrar por género

Dandalin Fasahar Fina-finai

Dandalin Fasahar Fina-finai

RFI Hausa

Fili ne na musamman kan Fina-finai ta hanyar tattauna da masu ruwa da tsaki a wannan fanni a duniya, Tare da wayar wa ma su sauraro kai da kara masu basira dangane da hikimar da Allah ya  bai wa wasu ta fanin shirya fim ko tsara wasan kwaikwayo. Wanda ke zo maku a duk ranar Asabar da safe, tare da maimaici a ranar Lahadi da yamma.

274 - Manyan labaran da suka wakana a wannan mako a duniyar fina-finai
0:00 / 0:00
1x
  • 274 - Manyan labaran da suka wakana a wannan mako a duniyar fina-finai

    A cikin shirin na wannan rana zamu zagaya da ku masana’antun shirya fina-finai don tsamo muku manyan labaran da suka wakana a wannan mako.

    Akwai mu da yadda aka fitar da jerin fina-finan da suka fi jan hankalin ƴan kallo a watanni 6 na wannan shekara daga ƙasar India.

    Muna tafe da yadda muhawara ta barke a shafukan sada zumunta, kan yadda jarumai daga jihar Plateau suka mamaye Kanywood, yayin da ake da karancin jarumai daga jihar Katsina.

    Sat, 11 Jul 2026
  • 273 - Tattaunawa ta musamman da mashiryin Fina-finai Abdul Amart

    A cikin shirin na wannan mako za ku ji mu ɗauke da tattaunawa ta musamman da mashiryin Fina-finai Abdul Amart.Muna tafe da batu kan fina-finan da aka fi tafka muhawara akan su cikin mako da muke bankwana da shi.

    Akwai mu da tattaunawa da Dauda Kahutu Rarara, wanda ya ballo sabuwar Dambarwa da mawaƙi Davido, da kuma yadda yake ganin wakokinsa na siyasa ka iya tasiri a zabe mai zuwa.

    Sat, 20 Jun 2026
  • 272 - Karancin ingantaccen labarin fina-finai, lamarin da ke karya darajar su a Najeriya

    A cikin shirin na wannan mako a bangaren mu na Kannywood zamu duba yadda karancin ingantaccen labarin fina-finai, lamarin da ke karya darajar fina-finan. Za ku ji mu tafe da dambarwar da ta kunno kai tsakanin fitaccen mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara, da hukumar tace fina-finai ta jijar Kano.

    Sat, 16 Nov 2024
  • 271 - Korafe-korafen makallata fina-finan Hausa

    A cikin shirin na wannan mako, zamu sake yin waiwaye kan korafe-korafen makallata fina-finan Hausa, kan yadda mashirya fina-finai suka fi mayar da hankali kan soyayya, tare da fatali da sauran fannonin rayuwa.

    Za mu tsallaka Jamhuriyar Nijar, inda zamu duba yadda zamani yayi tafiyar ruwa da wake-waken ‘yan mata da ke tashe a baya.

    Muna tafe da tattaunawa da Hadiza Gire, guda daga cikin matan da suka yi tashe a jamhuriyar Nijar lokacin da suke fagen rera wakokin ‘yan mata.

    Sat, 13 Jul 2024
  • 270 - Ko ana 'kan ta waye' a masana'antar Kannywood?

    Shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' ya yi nazari ne a kan al'amarin nan da ake kira 'kan-ta-waye'. Shirin ya yi  bayani a kan menene 'kan-ta-waye', sannan ya tattauna da baki, wadanda suka fadada bayanin don fahimtar mai sauraro.

    Sun, 06 Feb 2022
Mostrar más episodios

Otros podcasts de Noticias y Politica