Filtrar por género
- 563 - Shugaban Faransa ya bayyana halin da ake ciki a zirin Gaza a matsayin abin kunya ga duniya
A yau shirin ya yi waiwaye kan bankado yadda wasu fitattun yan siyasa a Najeriya suka wawure makudan kudade tare da mallakar kadarori a Amurka, sai Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da ta fara gwajin allurar Ervebo don daƙile cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo, da kuma fassarar kalaman shugaban Faransa Emmanuel Macron a babban taron MDD da ya bayyana halin da ake ciki a zirin Gaza na Palasdinu a matsayin babban abin kunya ga ƙasashen duniya.
Masu bincike da suka ɓanƙado yadda jami’an gwamnatin Najeriya na baya da na yanzu suka wawure makuɗan kuɗaɗen talakawa wajen sayen manyan gidaje na ƙasaita a Amurka, sun ce yaƙi da ta’addanci na daga cikin manyan hanyoyi da ake amfani da shi wajen satar dukiyar jama’a a Najeriya.
Haka zalika, kotun sasanta rikicin kasuwancin ta duniya dake birnin Paris na Faransa, ta yi watsi da buƙatar Kamfanin Sunrise da ya nemi Najeriya ta biya shi diyyar kuɗi dala miliyan 400.
Sat, 26 Sep 2026 - 562 - Ana ci gaba da tsokaci kan mutuwar mutane a hannun Civil Defence na jihar Neja
Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan makon ya tabo batun mutuwar matasa sama da 30 a jihar Neja da ke Najeriya a hannun hukumar tsaro ta Civil Defence. Haka nan Gwamantin Guinea ta aike da gargaɗi a hukumance ga kafofin yaɗa labaran Faransa game da yadda suke kiran sunan shugaban ƙasar, sai kuma Majalisar Ɗinkin Duniya da ta buƙaci masu bincike na ƙasa da ƙasa su karaɗe ilahirin Zirin Gaza, domin tattara hujjoji kan ɗaruruwan gawarwakin mutanen da ake zaƙuluwa daga ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine.
Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna............
Sat, 19 Sep 2026 - 561 - Dangote ya buɗewa al'uma ƙofar shiga a dama dasu a harkokin matatar mai
Shirin mu zagaya Duniya na wannan ya ba da hankali ne akan yadda Attajirin Afirka Aliko Dangote ya buɗe ƙofar sayar da hannayen jari ga jama'ar Najeriya, sai kuma matakin da mahukuntan Nijar suka ɗauka na umartar masu ababen hawa dasu je Yamai babban birnin ƙasar domin duba lafiyar ababen hawansu, sai batun ladan da Shigaban Amurka Donald Trump ya sanya ladan Dala dubu biyar-biyar ga Amurkawa idan har jam'iyarsa ta Republican ta samu nasara a zaɓen tsakiyar wa'adi.
Sat, 12 Sep 2026 - 560 - Yunkurin juyin mulki a Nijar ya ci gaba da ɗaukar hankali a faɗin duniya.
A wannan makon shirin Mu Zagaya Duniya ya yi waiwayen kan sukar kalaman shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da ya yi na cewa arewacin kasar ya fi amfana da manufofinsa, sai batun juyin yunkurin juyin mulkin Nijar da ya dauki hankali, sai rahoton MDD da ya gano katsalandan din kasashen waje ne ke rura wutar rikicin Sudan, sai luguden wutar da aka yi musaya tsakanin Amurka da Iran da ya janyo asarar rayuka.
A Najeriya, jam’iyyun adawa sun fara tsara yadda za su kayar da gwamnatin APC mai mulkin ƙasar ta wajen haɗakar da za ta fitar da ɗan takara ɗaya mai ƙarfi da zai iya gwabzawa da shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027, inda
ƙungiyar G-100, wadda ta tsara wannan haɗaka ta kawo shawarar cewa duk wanda ya samu takarar, zai yi wa’adi guda na shekaru 4 ne kacal.
Haka zalika, ikirarin da shugaba Bola Tinubu ya yi cewa yankin arewacin ƙasar ce ta fi cin gajiyar manufofinsa na sauye-sauyen tattalin arziƙi ya janyo suka daga masu ruwa da tsaki, inda ƙungiyar al’ummar Arewacin ƙasar da wasu ƙungiyoyin yankin suka caccaki kalaman, su na mai cewa a maimakon cigaba, manufofin shugaban sun mayar da yankin arewa cibiyar talauci.
A gefe guda kuma, gwamnatin mulkin sojan Nijar zargi Ivory Coast, Benin, Faransa, Chadi da kuma ECOWAS da kitsa shirin kifar da gwamnati, biyo bayan wani bore da ya faru a ranakun 28 zuwa 29 ga watan Agusta, da kuma haifar da rarrabuwar kawuna, musamman a tsakanin rundunar soji.
Yayin da ake tsaka da damana har ma aka fara tunkarar alamomin kaka, har yanzu akwai wasu garuruwa 20 na yankin Damagaram da ba su samu saukar ruwan shuka ba a Ƙaramar Hukumar Gangara na gundumar Tanut.
Mafi yawanci damina Niger bata wuce wata 3 zuwa 4, domin dai tana ƙarewa a watan Satumba in ta yi tsawon watan Oktoba.
Domin jin cikakken shirin, latsa alamar sauti.
Sat, 05 Sep 2026 - 559 - Adadin mutanen da suka mutu a ambaliyar ruwan Nepal na ci gaba da ƙaruwa
Shirin ''Mu Zagaya Duniya" tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako, ya taɓo muhimman batutuwan da suka faru a makon da muke bankwana da shi, inda ya taɓo yadda ƴanbindiga suka yi awun gaba da mutum sama da 600 a wani kauye da ke kan iyakar Najeriya da Benin a can jihar Neja. Adadin mutanen da mumunar ambaliyar ruwa ta kashe a Nepal ya haura zuwa 470.
A ɓangaren wasanni kuwa, shirin ya yi waiwaye kan rahoto murabus ɗin shugabancin hukumar kwallon kafa ta Najeriya da kuma yadda aka gudanar da bikin ranar Hausa.
Ku latsa lamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna..........
Sat, 29 Aug 2026 - 558 - Mu zagaya Duniya: Fara yaƙin neman zaɓe da musayar yawu tsakanin Tinubu da Atiku
Shirin ''Mu Zagaya Duniya" tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako kamar yadda aka saba ya taɓo muhimman batutuwan da suka faru a makon da muke bankwana da shi a Najeriya da sauran ƙasashen Afrika da ma duniya baki ɗaya.
Cikin batutuwan da shirin ya taɓo akwai yakin neman zaben Najeriya, inda aka jiyo tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar na shan alwashin dawo da tallafin man fetur, da kuma raddin shugaba Tinubu kan wannan furuci, sai cikar shekaru goma sha biyar da kifar da gwamnatin shugaban Libya Muammar Ghaddafi, inda a yankin Gabas ta tsakiya muka tabo labarin Iran da ta sanya ladan makudan kudade ga duk wanda ya kamo mata sojojin Amurka dama sauran muhimman labarai daga sassa daban-daban na duniya.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Sat, 22 Aug 2026 - 557 - Waiwaye game da muhimman labarai da suka faru a wannan makon
A Colombia, wata girgizar ƙasa mai karfin maki 7.4 da ta afkawa ƙasar da ke kudancin Amurka tare da hallaka akalla mutane sama da 100, yayin da wasu da dama suka jikkata,a cikin shirin da ke waiwaye game da muhimman abubuwan da suka faru a makon da mu kayi ban kwana,wato Mu zagaya Duniya za ku ji irin wainar da aka tuya a wasu ƙasashe..............
Sat, 15 Aug 2026 - 556 - Saudiya, Pakistan da Turkiya sun sanar da kulla yarjejeniyar tsaro
Ƙasashen Saudiya,Pakistan da kuma Turkiya sun sanar da kulla yarjejeniyar tsaro a tsakanin su yau juma’a a birnin Djeddah a wani yanayi da ake kara samun tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.
Yarjejeniyar da aka raɗa wa suna yarjeniyar Makka, ko baya ga harakar tsaro ta kuma tanadi faɗaɗa alakar da ke tsakanin ƙasashen a fanoni daban-daban.
Sat, 08 Aug 2026 - 555 - Mu Zagaya Duniya: Zafin alaƙa tsakanin Najeriya da Afrika ta kudu
Shirin "Mu Zagaya Duniya" tare da Oumarou Sani kamar kowanne mako ya taɓo muhimman labaran da suka faru a sassa daban daban na Najeriya ciki har da zafin alaƙa tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu, kana dambarwar ma'aikatar Bogi a Najeriya sai kuma batun cika shekaru 3 da faro mulkin Soji a Najeriya sannan batun ficewar Chadi daga kotun ICC.
Zamu soma shirin daga Najeriya inda batun kirkirar ma’aikatar Bogin nan ta PFIPC karkashin jagorancin Adeniyi Adeyimi Mattew wadda ke habbaka hulda da zuba jari ta sake tayar da kura a kasar .
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Sat, 01 Aug 2026 - 554 - Mu zagaya Duniya: Kotu ta yiwa ƴan ta'adda ɗaurin rai da rai a NajeriyaSat, 25 Jul 2026
- 553 - Ceto ɗalibai da malamansu a Oyo na cikin labarai da suka ja hankali a makon jiya
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon tare da Oumar Sani ya yi bitar wasu daga cikin manyan labarai da suka fi ɗaukar hankali a makon da muka yi bankwana da shi ciki har da nasarar kuɓutar da dalibai tare da malamansu 40 a jihar Oyo da ke Najeriya bayan sun shafe kwanaki 50 a hannun wadanda su kayi garkuwa dasu.
Sat, 18 Jul 2026 - 552 - Faɗa ya sake ɓarkewa tsakanin Amurka da Iran bayan rugujewar yarjejeniya
Shirin a wannan makon zai leka Gabas ta Tsakiya inda rikici ya sake barkewa tsakanin Amurka da Iran abin da ya kawo karshen yarjejeniyar fahimtar juna ta watanni uku da suka cimma a tsakaninsu. Bayan nan, shirin zai taɓo wasu mahimman lammuran da suka wakana a sassan yammacin nahiyar Afirka, musamman Najeriya, Nijar da Kamaru.
Sat, 11 Jul 2026 - 551 - Bitar muhimman labarun da suka faru a mako daga Rfi hausaSat, 04 Jul 2026
- 550 - Ana ci gaba da laluben dubban mutanen da suka ɓata a girgizar kasa a Venezuela
Shirin na wannan mako zai soma ne daga Venezuela inda a yammacin ranar laraba girgiza ƙasa mai karfin maki 7 a ma’aunin celcius ta afkawa arewa maso yammacin ƙasar abin da ya jefa al'umma cikin mawuyacin hali da alhini sakamakon rasa rayuka da dukiyoyi.
Alkaluman hukumomi sun ce sama da mutum 900 ne suka rasayukansu kawo yanzu yayin da sama da 4,000 suka jikkata bayaga sama da 50,000 da suka yi ɓatan dabo.
Tuni dai Ƙasashe suka fara aike da saƙonni jaje baya ga jami’an agaji don taimakawa a aikin laluben mutanen da girgizar ƙasa ta birne da kuma waɗanda ke cikin mawuyacin hali.
A nahiyar Turai kuwa matsanancin zafi ya tilasta dakatar da harakokin yau da kullum a ƙasashe da dama.
A wasu birane zafin ya kusa kai maki 40 a ma’aunin Celsuis abin da ya tilsatawa mahukunta fitar da gargaɗi da dakatar da muhimman harakokin yau da kullum.
A Faransa, an rufe ɗaruruwan makarantu a ranar Litinin yayin da aka rage lokacin tashin wasu dubbai.
A wani labarin kuma, ranar Alhamis da ta gabata al’ummar musulmi mabiya ɗarikar Shi’a a duniya suka gudanar da juyayin tunawa da kisan jikan Annabi Muhammad SAW, da aka yi a garin Karbala na ƙasar Iraqi ta yanzu, kwanakin da ke yiwa laƙabi da Tasu’a da Ashura.
A ƙasar Iran wadda itace cibiyar mabiya Shi’a a duniya an gudanar da bikin na wannan rana a cikin yaƙi da kuma rashin jagoran addinin ƙasar Ayatoullah Ali Khamna’ei, wanda ke jagorantar ranakun a kowacce shekara.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Oumarou Sani.
Sat, 27 Jun 2026 - 549 - Shirin yayi bita kan harin da aka kai filin jirgin saman Yamai da ma wasu labaraiSat, 20 Jun 2026
- 548 - Shirin ya fara da yadda aka buɗe bikin gasar cin kofin duniya a ƙasar Mexico
Ranar Alhamis 11 ga wannan watan aka yi bikin buɗe gasar cin kofin duniya karo na 23, gasar da itace karo na farko da ƙasashe 3, Amurka da Canada da kuma Mexico su ka karbi baƙunci, sai dai kuma an gudanar da zanga-zanga a wasu sassa na birnin ƙasar.
Ƙasashe 48 ne ke fafata domin samun zakaran bana kuma yan wasa 1,248 da alkalan wasa 52 za su jagoranci wasanni 104 da za'a kwashe kwanaki 39 ana yi.
A cikin shirin akwai labarin, shugaban Amurka Donald Trump, da ya ce ya soke shirinsa na kai munanan hare-haren da ya shirya yi a Iran, sakamakon wata tattaunawar da yace ya yi da wasu ƙusosshin gwamnatin ƙasar, Ikrarin da ya zuwa yanzu hukumomin ƙasar basu ce komai akai ba.
Haka zalika, Majalisar Dokokin Najeriya ta amince da dokar kafa ƴansandan jihohi da gagarumar rinjaye, matakin da zai bai wa gwamnatocin jihohi damar kafa rundunar da za ta taimaka wajen magance matsalolin tsaron da suka addabi ƙasar.
A Jamhuriyar Nijar gwamnati ce ta rattaɓa hannu a kan dokar haramta auran jinsi ko kuma mu’amalar jinsi guda wanda ta tanadi hukuncin ɗaurin da ka iya kai wa shekaru 20 a kan duk wanda aka samu da laifin yin haka.
A wani abu da ba’a saba gani ba, Kungiyar mayaƙan JNIM mai alaƙa da Al Qaeda reshen Mali ta yi tayin bayar da tukwicin miliyoyin Yuro ga duk wanda ya ba ta bayanai kan inda shugaban kasar Assimi Goita da manyan jami'an sojinsa suke, a yayin da ta bayyana gwamnatin a matsayin haramtacciyar.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin, tare da Oumarou Sani.
Sat, 13 Jun 2026 - 547 - Yadda malaman makaranta suka gudanar da zanga-zanga kan rashin tsaro a NajeriyaSat, 06 Jun 2026
- 546 - Mahajjata kusan miliyan biyu sun gudanar da aikin Hajjin bana
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon tare da Oumarou Sani, kamaar yadda aka saba ya yi bitar wasu daga cikin muhimman lamurran da suka wakana a makon da muka yi wa bankwana.
Daga cikin muhimman batutuwan kuma akwai, yadda Musulmi kusan miliyan biyu suka samu nasarar gudanar da aikin Hajjin bana.
Shirin ya kuma leƙa Yankin Gabas ta Tsakiya domin jin halin da ake ciki, musamman kan ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Iran.
Sat, 30 May 2026 - 545 - RFI Hausa ta cika shekaru 19 da fara watsa labarai cikin harsshen Hausa
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' ya fara ne da labarin cikar wannan tasha ta RFI Hausa shekaru 19 da kafuwa.
Ranar alhamis 21 ga wannan watan gidan Rediyonku na RFI sashen Hausa ya cika shekara daya- daya har 19 da soma yada shirye-shiryensa .
A shekara 2007 ne kwarrariyar ƴar Jarida Lanni Smith ta kirkiri sashen Hausa na RFI da aka yi wa matsuguni a birnin Lagos da ke kudu maso yammacin Najeriya.
Kuma bikin na bana yazo a wani yanayi da kafar ke kara samun daukaka a idon duniya.
Sat, 23 May 2026 - 544 - Yadda harin dakarun Najeriya ya kashe ɗimbin mutane a kasuwar Zurmi
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' yana bita ne na mahimman labaran al'amura da suka wakana a makon da ya gabata. a wannan makon shirin ya soma ne daga Najeriya inda a farkon makon da ya wuce wani harin da dakarun Najeriya suka kai ta sama a kasuwar Tumfa ta karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamafara ya hallaka akalla mutum dari 100 tare da jikkata wasu da dama.
Wannan harin da ke zaman mafi muni da dakarun kasar su kai kan fararen hula shi ne na uku a cikin kasa da wata guda .
Sat, 16 May 2026 - 543 - Wasu daga cikin muhimman labaru a cikin makon daya gabataSat, 09 May 2026
- 542 - Yadda haɗakar ƙungiyoyi suka ƙaddamar da farmaki a sassan Mali
Shirin ya soma daga ƙasar Mali inda a ranar 25 ga watan Afrilun da mu kayi ban kwana haɗakar mayakan Abzinawa na FLA da na ƙungiya masu ikirarin jihadi ta JNIM suka ƙaddamar da mugayen hare-hare a garuruwa huɗu na ƙasar da suka haɗa da Sevare, Kidal, Gao da kuma Kati.
A garin Kati da ke zaman babban sansanin sojin ƙasar ƴan bindigar sun yi amfani da motoci shake da bama-bamai da manyan bindigogi inda suka kai hari kan gidan ministan tsaron kasar Sadio Camara tare da hallaka shi.
A kasar Chadi kuwa aƙalla mutum 42 ne suka mutu bayan ɓarkewar wani rikicin ƙabilanci da ya faro sanadiyyar taƙaddama tsakanin wasu mata biyu yayin da suke ɗiban ruwa a wata rijiyar bayan gari.
A Najeriya kuwa, ranar Alhamis ne kotun ƙolin ƙasar ta yanke hukunci kan rikicin cikin gida na jam'iyyun ADC da PDP.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin, tare da Oumarou Sani.
Sat, 02 May 2026 - 541 - Shirin mu zagaya duniya ya tattaro manyan labaran da suka faru a wannan makoSat, 25 Apr 2026
- 540 - Makomar masu shiga tsakani,kan neman ƙulla yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran
Mecece makomar ƙoƙari da masu shiga tsakanin, musamman Pakistan ke yi a kan neman ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran duba da tsaurin wasu ko da dama daga cikin sharuɗɗan da ɓangarorin biyu suka gabatarwa juna?
Nura Ado Suleiman ke yi muku barka da sake haɗuwa cikin shirin Duniyarmu a Yau
Sat, 18 Apr 2026
Podcasts similares a Mu Zagaya Duniya
El Partidazo de COPE COPE
Herrera en COPE COPE
La Linterna COPE
Dante Gebel Live Dante Gebel
Es la Mañana de Federico esRadio
La noche de Cuesta esRadio
La Trinchera de Llamas esRadio
Hondelatte Raconte Europe 1
Affaires sensibles France Inter
LEGEND Guillaume Pley
El colegio invisible OndaCero
La Rosa de los Vientos OndaCero
Les grands dossiers de l'Histoire par Franck Ferrand Radio Classique
Espacio en blanco Radio Nacional
Enquêtes criminelles RTL
Entrez dans l'Histoire RTL
Le grand récit RTL
Les Grosses Têtes RTL
L'Heure Du Crime RTL
Parlons-nous RTL
El Larguero SER Podcast
SER Historia SER Podcast
Todo Concostrina SER Podcast
Un Libro Una Hora SER Podcast
