Filtrar por gênero

Mu Zagaya Duniya

Mu Zagaya Duniya

RFI Hausa

Shirin Mu Zagaya Duniya na duba Wasu Muhimman Labarai da suka ja hankalin Duniya a cikin mako. Ana gabatar da shirin ne a ranar Asabar da safe a kuma maimaita ranar Lahadi da daddare.

563 - Shugaban Faransa ya bayyana halin da ake ciki a zirin Gaza a matsayin abin kunya ga duniya
0:00 / 0:00
1x
  • 563 - Shugaban Faransa ya bayyana halin da ake ciki a zirin Gaza a matsayin abin kunya ga duniya

    A yau shirin ya yi waiwaye kan bankado yadda wasu fitattun yan siyasa a Najeriya suka wawure makudan kudade tare da mallakar kadarori a Amurka, sai Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da ta fara gwajin allurar Ervebo don daƙile cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo, da kuma fassarar kalaman shugaban Faransa Emmanuel Macron a babban taron MDD da ya bayyana halin da ake ciki a zirin Gaza na Palasdinu a matsayin babban abin kunya ga ƙasashen duniya.

    Masu bincike da suka ɓanƙado yadda jami’an gwamnatin Najeriya na baya da na yanzu suka wawure makuɗan kuɗaɗen talakawa wajen sayen manyan gidaje na ƙasaita a Amurka, sun ce yaƙi da ta’addanci na daga cikin manyan hanyoyi da ake amfani da shi wajen satar dukiyar jama’a a Najeriya.

    Haka zalika, kotun sasanta rikicin kasuwancin ta duniya dake birnin Paris na Faransa, ta yi watsi da buƙatar Kamfanin Sunrise da ya nemi Najeriya ta biya shi diyyar kuɗi dala miliyan 400.

    Sat, 26 Sep 2026
  • 562 - Ana ci gaba da tsokaci kan mutuwar mutane a hannun Civil Defence na jihar Neja

    Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan makon ya tabo batun mutuwar matasa sama da 30 a jihar Neja da ke Najeriya a hannun hukumar tsaro ta Civil Defence. Haka nan Gwamantin Guinea ta aike da gargaɗi a hukumance ga kafofin yaɗa labaran Faransa game da yadda suke kiran sunan shugaban ƙasar, sai kuma Majalisar Ɗinkin Duniya da ta buƙaci masu bincike na ƙasa da ƙasa su karaɗe ilahirin Zirin Gaza, domin tattara hujjoji kan ɗaruruwan gawarwakin mutanen da ake zaƙuluwa daga ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine.

    Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna............

    Sat, 19 Sep 2026
  • 561 - Dangote ya buɗewa al'uma ƙofar shiga a dama dasu a harkokin matatar mai

    Shirin mu zagaya Duniya na wannan ya ba da hankali ne akan yadda Attajirin Afirka Aliko Dangote ya buɗe ƙofar sayar da hannayen jari ga jama'ar Najeriya, sai kuma matakin da mahukuntan Nijar suka ɗauka na umartar masu ababen hawa dasu je Yamai babban birnin ƙasar domin duba lafiyar ababen hawansu, sai batun ladan da Shigaban Amurka Donald Trump ya sanya ladan Dala dubu biyar-biyar ga Amurkawa idan har jam'iyarsa ta Republican ta samu nasara a zaɓen tsakiyar wa'adi.  

    Sat, 12 Sep 2026
  • 560 - Yunkurin juyin mulki a Nijar ya ci gaba da ɗaukar hankali a faɗin duniya.

    A wannan makon shirin Mu Zagaya Duniya ya yi waiwayen kan sukar kalaman shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da ya yi na cewa arewacin kasar ya fi amfana da manufofinsa, sai batun juyin yunkurin juyin mulkin Nijar da ya dauki hankali, sai rahoton MDD da ya gano katsalandan din kasashen waje ne ke rura wutar rikicin Sudan, sai luguden wutar da aka yi musaya tsakanin Amurka da Iran da ya janyo asarar rayuka.

    A Najeriya, jam’iyyun adawa sun fara tsara yadda za su kayar da gwamnatin APC mai mulkin ƙasar ta wajen haɗakar da za ta fitar da ɗan takara ɗaya mai ƙarfi da zai iya gwabzawa da shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027, inda

    ƙungiyar  G-100, wadda ta tsara wannan haɗaka ta kawo shawarar cewa duk wanda ya samu takarar, zai yi wa’adi guda na shekaru 4  ne kacal.

    Haka zalika, ikirarin da shugaba Bola Tinubu ya yi cewa yankin arewacin ƙasar ce ta fi cin gajiyar manufofinsa na  sauye-sauyen tattalin arziƙi ya janyo suka daga  masu ruwa da tsaki, inda ƙungiyar al’ummar Arewacin ƙasar da wasu ƙungiyoyin yankin suka caccaki kalaman, su na mai cewa a maimakon cigaba, manufofin shugaban sun mayar da yankin arewa cibiyar talauci.

    A gefe guda kuma, gwamnatin mulkin sojan Nijar zargi Ivory Coast, Benin, Faransa, Chadi da kuma ECOWAS da  kitsa shirin kifar da gwamnati, biyo bayan wani bore da ya faru a ranakun 28 zuwa 29 ga watan Agusta, da kuma haifar da rarrabuwar kawuna, musamman a tsakanin rundunar soji.

    Yayin da ake tsaka da damana har ma aka fara tunkarar alamomin kaka, har yanzu akwai wasu garuruwa 20 na yankin Damagaram da ba su samu saukar ruwan shuka ba a Ƙaramar Hukumar Gangara na gundumar Tanut.

    Mafi yawanci damina Niger bata wuce wata 3 zuwa 4, domin dai tana ƙarewa a watan Satumba in ta yi tsawon watan Oktoba.

    Domin jin cikakken shirin, latsa alamar sauti.

    Sat, 05 Sep 2026
  • 559 - Adadin mutanen da suka mutu a ambaliyar ruwan Nepal na ci gaba da ƙaruwa

    Shirin ''Mu Zagaya Duniya" tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako, ya taɓo muhimman batutuwan da suka faru a makon da muke bankwana da shi, inda ya taɓo yadda ƴanbindiga suka yi awun gaba da mutum sama da 600 a wani kauye da ke kan iyakar Najeriya da Benin a can jihar Neja. Adadin mutanen da mumunar ambaliyar ruwa ta kashe a Nepal ya haura zuwa 470.

    A ɓangaren wasanni kuwa, shirin ya yi waiwaye kan rahoto murabus ɗin shugabancin hukumar kwallon kafa ta Najeriya da kuma yadda aka gudanar da bikin ranar Hausa.

    Ku latsa lamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna..........

    Sat, 29 Aug 2026
Mostrar mais episódios

Outros Podcasts de Notícias e Política