Filtra per genere

Ilimi Hasken Rayuwa

Ilimi Hasken Rayuwa

RFI Hausa

Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken kimiya da fasaha da ke neman saukakawa Dan’adam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Bil’Adama. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe, a ku maimata ranar Alhamis.

454 - Jigawa ta gabatar da tsarin rage barace-baracen Almajirai a jihar
0:00 / 0:00
1x
  • 454 - Jigawa ta gabatar da tsarin rage barace-baracen Almajirai a jihar

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan daɗaɗɗen batun nan na yaran da basa zuwa makaranta a Najeriya matsalar da har kawo yanzu ta ƙi ci taki cinyewa.

    Wani Rahoton UNICEF ya bayyana jihohin Kano da Jigawa da kuma Katsina a matsayin jihohin da ke da rinjayen yaren da basa zuwa Makaranta, inda a jumlace ƙasar ta yammacin Afrika ke da yara fiye da miliyan 18 da basa zuwa Makaranta, galibinsu a arewacin ƙasar.

    Tuni Jihar Jigawa ta ɗaura ɗamarar yaƙi da wannan matsala, inda ta gabatar da wani sabon tsarin mayar da ɗimbin yara makarantu.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    Tue, 29 Sep 2026
  • 453 - Gwamnatin Kano na shirin tilasta koyar da ilimin Kwamfuta a makarantun Firamare da Sakandare

    Shirin Ilimi Hasken rayuwa na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda majalisar dokoki jihar Kano ta bukaci a mayar da ilimin Kyamfuta dole a matakin makarantun Firamare da Sakandare.

    Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

    Tue, 22 Sep 2026
  • 452 - Gwamanatin Najeriya na shirin Horas da malamai sama da miliyan guda

    A yau shirin ya mayar da hankali ne kan matakin gwamnatin Najeriya kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka da ke shirin horas da malaman makaranta sama da miliyan guda.

    Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

    Tue, 15 Sep 2026
  • 451 - Gudunmowa ko kuma illar da shafukan sada zumunta ke yiwa al'adun Bahaushe

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa ya duba irin yadda guguwar kafafen yada labarai da shafukan Internet ke barazana ga al'adun Hausawa da salon rayuwarsu.

    Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

    Tue, 01 Sep 2026
  • 450 - Yadda matasa suka ƙera jirgi maras matuƙi mai cin Kilomita 30 a Kano

    Shirin a wannan makon ya leka Kanon Najeriya, inda aka gano wani sabon tarihin bunkasar kimiyya da fasaha da matasan yankin ke jagoranta.

    Wannan gagarumar bajinta dai wani matashi Abubakar Waiya, wanda ya daɗe yana fafutukar kera na'urorin shawagi ne ya ƙera jirgi maras matuƙi domin taimakawa ɓangaren tsaro da kuma boma.

    Jirgin da ya kera a yanzu yana da ikon tashi da kansa har na tsawon kilomita 30 ba tare da ya ɓace ba.

    Wannan na'ura tana da aiyuka na musamman da aka tsara ta don yi, kamar feshin maganin ƙwari a gonaki na zamani da kuma kai magungunan gaggawa zuwa yankunan karkara da motoci ba su iya zuwa saboda rashin hanya.

    Duk da wannan gagarumar nasara, babban ƙalubalen da ke gaban matasan shi ne tsarin dokoki na ƙasa.

    Masu fafutuka na ganin cewa, idan har gwamnati da masu ruwa da tsaki suka ba wa waɗannan matasa dama da goyon baya, wannan ƙoƙari daga birnin Kano zai zama tushen samar da dabarun tsaro da aikin gona na zamani ga ɗaukacin yammacin Afirka.

    Tambayar da ta rage anan ita ce: Shin gwamnati za ta tallafa wa wannan fasaha ta gida don ta bunkasa, ko kuwa za a zura ido ta ɓace ne?

    Tue, 18 Aug 2026
Mostra altri episodi